Sashe 97
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mujaheed daya dawo daga gurin aiki mama ta sanar dashi zuwan umma har take bashi labari da yabon ƙirkinta, tace ya shirya yaje ya ɗauko matarsa. Cikin tsananin farin ciki ya wuce ɗaki ya watsa ruwa kana ya sanya manyan kaya ya fito yana baza ƙamshin turate, Safara'u sai washe baki take tana ambaton ango, Mujaheed ya dalla mata harara yana cewa.
Shashasha wai ke ko irin kishin nan ba ruwanki.
Ni dai Jaheedi karka riƙa gwasaleta gaban matarka ta rainata bana son haka.
Cewar mama, Mujaheed baice komai ba ya fice dan a kullun Safara'u bata laifi a gurinta, haka ya tari napep ya nufi badarawa a asalin Mujaheed, yau ne rana ta farko daya je gidan bada motarsa ba, koda ya isa sallama ya yi a ƙofar gida Junaid ya amsa ya fito dan shike tsakar gida suna hira da iyayensu, koda yaga Mujaheed ne ya miƙa masa hannu suka gaisa kana ya yi masa jagora zuwa cikin gida, a nan tsakar gida aka shimfiɗa masa dadduma ya zauna ya gaishesu cikin mutuntawa da bayar da haƙurin jinsu shuru, a takaice bai ɓoye zafin da mama ta ɗauka ba dama zuwan umma gidan ɗazun wanda dalilin zuwanta yasa mama ta sauko, baba ya shiga girgiza kai.
Halima! Halima kai Allah ya shiwa matar nan da albarka ta iya mu'amala, tasan ta rama alkhairi akan sharri, duk irin abubuwan da suka faru ta mance komai ta yi mana wannan halacci, Najwa! Najwa! maza zo nan.
Baba ya ƙare maganar yana kwalawa Najwa kira cikin zafin rai, data fito ta tsuguna a gefe Baba ya nunata da yatsa.
Kin ga duk irin abinda kika aikawata Sameeha bai hana Halima ta shiga gaba wajen gyara aurenki ba Najwa, wlh kibi duniya a sannu babu komai a cikinsa sai ruɗani, ki zauna a ɗakinki kiyi bautan Allah, ki mance komai ki gyara zuciyarki da halinki dan wlh idan kika aikata mummunar abu bani kika wulaƙanta ba Halima kika yiwa wacce ta yi miki halacci kuma bai dace ki ƙara saka mata da sharri ba, kin ga dai gamu nan mu iyayenki ba muda komai bamu bayar ajiya ba haka muke cikin rufin asirin Allah, ki saka a ranki arziki na Allah ne kuma yana goshin ko wani bawa ki taƙaita dogon buri domin ki wanye da duniya lafiya. Kai kuma don son ma'aikin Allah s.a.w ka cire ƙarya da yaudara a cikin lamarinka duk abinda zaka yi mata ka yi iya ƙarfin ka, ka gyara alaƙarka da ita in har kana so zamanku ya ɗaure, gata nan amana ce muka baka in kaci to wlh Allah bazai barka ba, Zulai in kina da abin cewa ki faɗa sai su wuce.
Baba ya ƙare maganar ga Inna, itama faɗan ta kuma yiwa Najwa da nasiha ta haɗa da Mujaheed ɗin, daga bisani suka sallame su Najwa ta faɗa jikin inna tana ta kuka, hakanan taji zuciyarta ta tsinke wanda sai a wannan lokacin ne ta ji bata kyautawa Sameeha ba da kuma tunanin duk tarin abubuwan data yi bai hana umma ta shiga gaba ba wajen daidaita aurenta, ta kuma san har abada su Sameeha sun fita ba zata taɓa haɗa kanta dasu ba, tunda zama gidan Mujaheed ya zame mata ƙaya a maƙoshi bata san ranar fitanta ba, sai ta ƙara fashewa da sabon kuka.
Baba da Inna ku yafe mini, In Sha Allah bazan taɓa baku kunya ba.
Mun yafe miki Najwa dama mu fatanmu ki gane kinyi kuskure.
Cewar Inna tana bubbuga bayanta, baba ko kwalla yaji ya cika masa ido dan yana matuƙar ƙaunar Najwa saboda ita kenan musu ɗiya mace, dole yake danne son saboda ya nuna mata kuskurenta. Haka Mujaheed yayi musu godiya da sallama ya fita shima duk jikinsa yayi sanyi da dana sanin ƙaryar daya yi mata, Najwa kuwa sai da inna ta ɗagata ta kamata suka miƙe kana ta kaita ɗaki ta kuma shiryawa sai ta rakota har ƙofar gida, Junaid ya yi musu rakiya har zuwa bakin hanya, ya tare musu napep suka shiga yayi musu fatan alkhairi suka wuce.
Suna isa gida Mujaheed yayi musu jagora sai da suka fara shiga ɗakin mama Najwa ta gaisheta ta amsa fuska sake kamar ba wani abu daya faru, hakan ya faranta ran Mujaheed daga bisani suka wuce ɗakinsu ya buɗe suka shiga sai ya ce mata zai je ya dawo ya fito ya wuce, Najwa kuwa kwanciya tayi a gado bata cire komai a jikinta ba sai duniyar tunani data shiga da lissafin yadda zata fara rayuwa a gidan da ko a mafarki bata taɓa kawowa kanta ba. Kusan minti arba'in Mujaheed ya ɗauka kafin ya shigo gidan, sai da ya fara kaiwa su Mama nasu kazar yace ta ɗibarwa Safara'u sai yayi mata sai da safe ya dawo ɗaki ya samu Najwa a kwance, ya fita ya rife ɗakin ya ɗauko plate da kofi ya dawo ya zauna gefen gado ya ciro gasasshiyar kaza ya aje a plate ya buɗe kwalin holandiya ya tsiyaya a kofi ya ce.
Najwa tashi kici abinci.
Ba musu ta tashi ta zauna ganin kayan kwaɗayi yasa ta dan sake fuska, haka ta amsa kofin tasha ta sauko ƙasa kusa dashi suka fara cin kaza daga haka ya dinga janta da hira har ta saki fuska. A wannan daren dole Najwa ta bada kai bori ya hau dan kuwa Mujaheed ba baya ba wajen iya zuba lafazi, sai dai wannan karan ya yi ƙoƙarin gyara harshensa gudun yin ƙarya, ya samu Najwa a cikakkiyar budurwa hakan ya ƙara dulmiyar da zuciyarsa wajen soyayyarta dan son ta ya ninku. Najwa dai tasan ƙaddara ta riga fata so bai taɓa zama samu, Mujaheed shine babban ƙaddarar Jarabawanta a duniya.
*Hoooohoho ya kamata ace littafin nan ya ƙare a nan fa, ko da yake akwai saura pages ɗaya ko biyu In Sha Allah*
[5/26, 8:28 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shai wanidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
58
Da gari ya waye.
Najwa ta shiga kitchen domin É—aura musu ruwan wanka sai dai me babu gas domin haka aka kawo mata tukunyar, sai ta dawo uwar É—aka ta zauna a gefen gado tana cewa Mujaheed dake kwance.
Ya za muyi babu gas, kuma nepa sun É—auke wuta.
Subhanallahi yanzu ya zamu yi wanka, ko da yake bari na amso mana ruwa gurin mama dan tun asuba take tashi haÉ—a abin kari. In yaso anjima sai a siwo miki gawayi ki fara amfani da shi kan na siyo gas É—in.
Mujaheed gawayi fa kace? taya ina amarya nayi amfani da gawayi haba dai É—an abincinmu kwata kwata kwaya nawa ne da sai na hura wuta, gas É—in dai zaka siyo mini.
Gaskiya Najwa bani da kuɗi dan abinda ya rage mini kenan na siyo kaji biyu da sauran abubuwan, dubu guda da ɗari biyu ya rage mini yanzu, in zan je aiki zan bawa mama ɗari biyar na cefane sauran nayi kuɗin mota. Haƙuri za kiyi ki amfani da gawayi dan yanzu so nake muyi zama da gaskiya ba zan yi miki abinda nasan bani da ƙarfinsa ba, in ma ba kida murhu akwai na mama dana Safara'u ki ara ɗaya ki amfani da shi sannan girki mama zata riƙa yi damu har na kwana biyu.
Wlh bazan bar gawayi a gidanmu ba na zo nan inyi amfani da shi ba, ai gas ba ƙarya kayi ba dan ka siyan mini shi.
Najwa sai fa kiyi amma banda kuÉ—in gas a yanzu.
Yana gama fatdar haka ya sauko daga kan gado ya zura riga ya fice, Najwa wani baƙin ciki taji ya tsaya mata a maƙoshi wai gawayi, abinda take tunanin har gaban abada tafi ƙarfinsa a yanzu amma kuma yana niman laƙa mata amfani dashi na dole, bata jin zata yi amfani da shi domin tun a gidansu tayi hannun riga da shi, wayarta ta ɗauko taga ƙarfe bakwai saura still da sauran gari ya waye, amma ya zata yi dole ta kira gida dan a kawo mata ɗauki tunda suna son zamanta a gidan dole suyi mata abinda take so. Yaya Junaid ta kira cikin barci ya ɗauka yana tambayar lafiya ta kira shi da sassafe.
Yaya gas ne babu ba a saka mini ba a tukunyar shine na yiwa Mujaheed magana wai sai dai inyi amfani da gawayi baida kuÉ—in sayan gas.
To Najwa miye aibun gawayin naga anan gida ma da shi muke amfani.
Haba haba yaya amarya ce ni fa taya daga zuwana sai gawayi, ya kamata kona shekara nayi amfani da gas.
To shikenan bari anjima zan aiko yaron aikina ya amsa gas É—in, zan bashi number É—inki in yazo zai kira ki masa kwatance ya amsa ya ciko miki ya dawo da shi, dama inna tayi amfani dashi wancen auren naki da aka dawo dashi dan a cike yake, nace kar a aje ayi amfani dashi.
To nagode yaya.
Shikenan ko akwai bata damuwa.?
Babu.
To Najwa kita haƙuri ko ba komai ne rai yake samu ba.
To tace masa sai suka yi sallama a lokacin har Mujaheed ya shigo da ruwan zafin a bokiti ya zauna ta gama wayar, tana ajewa kuwa ya kalleta rai a ɓace.
Bazan lamunci kina tona asirin gidana ba, ai bance bazan siya ba kawai ki fara amfani da gawayi kafin na samu, shine har zaki kira gida domin aga gazawata dake.
Kai kaso hakan ya faru amma banga dalilin daga zuwana gidanka na fara da gawayi ba sai kace amaryar tushe, wai ma ina akwatina daka ce sai nazo zaka nuna mini ko shima duk yana cikin ƙaryar daka yi mini.
Yaushe kika zo gidan da kika ga kin jima ba a baki akwatin ba.