← Book details Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 103

Sashe 95

Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakata Junaidu ba sai ka wahalar da kanka ba, Najwa zo nan.

Ya ƙare maganar yana haɗe rai ya juya ta tafi ɗakinsa, Najwa ta bi bayansa suka shiga ciki Inna ma ta shiga ɗakin, Junaid ya tsaya a bakin ƙofar ɗakin, Najwa ta tsuguna a gaban baba daya zauna gefen gado. Baba Ya ya nuna mata kansa yana cewa.

Ni wanene a gurin ki.

Kai babanmu ne.

To ina so in har kina so na cigaba da amsa sunnan mahaifinki ki tashi ki koma gidanki, idan kuma kin zaɓi duniya ce to zan barki da ita, sannan ba zaki ƙara amsa sunan 'yata ba dan zan tsameki daga cikinsu har abada bani ba ke, idan kin kaso aurenki to sai ki nima wani uban, dan kar ki kuskura naga ƙafarki a gidan nan na sallawa duniya ke, ko mutuwa nayi bance ki zo ba. Zaɓi ya rage naki.

Yana gama faɗar haka yaja pillow ya kishingiɗa ransa a matuƙar ɓace dan har wani ɗaci ɗaci yake ji a makoshinsa, lamarinta a yanzu ya daina bashi mamaki face tsoro dan gani yake tamkar ba asalin Najwan su bace yarinya mai kunya da kawaici ga biyayya, shi dai kam data kaso aurenta a karo na biyu gwara ya sallamawa duniya ita dan baya jin zata kuma cin abincin gidansa balle ta samu wajen kwana. Bakwa ko jikinta yayi mugun la'asar da zantukan baba ta girgiza matuƙa akan furicinsa, wanda bata yi tsammani ba sam a zaton ta da ƙaramin lisaafinsa zasu goya mata bayane akan sakin tunda Mujaheed ya yaudaresu ne, Inna tace.

Haka nima kazalika idan kika kaso wannan auren wlh bani ba ke Najwa, duk tarin soyayyar da kika ganin muna yi miki bazai sa idonmu ya rufe ba mu cigaba da zuba miki ido kina iskancin da kika ga dama ba, ya kamata ace kina da iyaka bazai yuwu ba, dan haka ki miƙe ki koma in da kika fito dan wlh yadda kika dawo ke kaɗai haka zaki mayar da kanki idan kin so ki yi zaman aure idan kin so ki kashe auren ki shiga duniya amma ba gidan nan ba, ai ba ke ce kaɗai pya ba sauran sun ishemu zaman duniya.

Nan jikin Najwa ya ɗauki rawa zuciyarta kamar zata faɗo kasa, bata zaci haka ba tayi tunanin zasu goyi bayanta, yanzu da kunya ta koma gidanta ita kaɗai ba tare da an rakata ba sannan ma in ta koma tace me ita data nima saki, daka mata tsawan da Junaid yayi yasa ta miƙe zumbur tana matsar kwalla cikin kuka ta soma cewa.

Yaya dan Allah ku saurari uzurina wlh ba a son raina ba na dawo, Mujaheed ya yaudareni yayi mini ƙaryar da bai dace nayi zaman aure da shi ba, yanzu ina kuke so na tsoma zuciyata, rana zafi inuwa kuna.

Najwa duk abinda ya faru fa ke ce kika jawa kanki kuma Allah ya duba zuciyarki ne shiyasa ya zaɓa miki Mujaheed a matsayin miji, idan kin gyara zuciyarki tabbas Allah zai jiƙanki. Ki ɗauki wannan auren matsayin ƙaddara dan haka wuce muje.

Ya ƙare maganar yana nuna mata hanyar fita, jikinta a sanyaye ta wuce yabi bayanta hawaye kawai take yi ta rasa meke mata daɗi, sai ta ja mayafinta ya rufe mata fuska ta wuce har titi ya samu napep ta shiga shima ya shiga gefenta suka wuce abakwa lokacin wajen goma saura, har ƙofar gidan suka isa, Junaid ya ciro wayarsa ya kira Mujaheed akan ya fito ƙofar gidansu, Najwa tayi mamakin yadda Junaid ya san gidan tunda ba tambayarta unguwar yayi ba, hakan ya na nufin yasan komai kenan, a haka Mujaheed ya fito shida Mamansu suka tsaya Junaid ya sauko daga Napep ya tasa ƙeyar Najwa suka isa ƙofar gida, mama da faɗanta tace.

Allah yasa ba dawo da ita kayi ba, dan dama jira nake garin Allah ya waye mu aiko da takardan sakin da ta buƙata, dan bazan yarda ta kashe min shi ba a banza.

Dan Allah mama kuyi haƙuri In Sha Allah ba zata sake aiwatar da komai ba, anyi mata faɗa sosai.

Yaro batun kisa fa ake magana, yarinyar nan wuƙa ta ɗauko akan lallai zata kashe shi in bai saketa ba, Allah ne ya tsare shi ya amsa wuƙar fa, dan haka wlh ka mayar da ita gida sai anyi sabon zama bazai yuwu ta yi irin wannan abu ba in ɗauke shi da sauƙi.

Mamaa tunda sun dawo na tabbatar ba zata yi komai ba wlh gidansu akwai kula da tarbiyya, kuma na faÉ—a miki laifina ne da har yasa tayi haka ni na ja komai.

Cewar Mujaheed da duk ya ƙosa a bashi matarsa dan sosai yaji farin cikin dawo masa da ita, amma fir mama tace.

Ai dama kai shashasha ne so ya rufe maka ido har baka gane kanka, yarinyar data nima kasheka kake rawar ƙafa akanta. Kai yaro ka mayar da ita gida sai munyi shawara tukuna dan wannan maganar sai mun zauna mu iyaye mun tattaunata.

Shikenan mama Allah ya kyauta na gaba ya kuma ƙara muku haƙuri, ke kuma muje gida kin kyauta abinda kika yi.

Ya faɗa yana juyawa Najwa kuka kawai take wanda hakan ya haifar mata da ciwon kai mai tsanani, akan wannan ƙasƙantaccen gidan mama tayi musu haka, wanda ita In son ranta ne ba zata zauna a ciki ba, ba ƙaramin muzanta tayi yau ba komai ya lalace mata a lokaci guda, haka ta juya suka shiga napep ya mayar dasu gida, Mujaheed kuwa kamar zai ɗaura hannu aka ya fasa ihu dan sosai ya ji ba daɗin abinda mama tayi, haka suka juya suka shiga gida kowanne ransa a jagule.

Junaid suna isa gida yace ta wuce É—akin inna shi kuma ya yi sallama É—akin baba da suka yi masa izini ya shiga ciki ya zauna, nan ya basu labarin duk yadda suka yi da mahaifiyar Mujaheed, inna tace.

Banga laifinta ba wlh dan tana da gaskiya, maganar kisa ba wasa bace, wlh Najwa sai ta san ta aikata waÉ—annan abubuwan, na rasa yadda aka yi ta sauya halinta gabaÉ—aya.

Laifinki ne da baki saka mata ido, ga irin ta nan ai ita kaɗai ta hanamu saƙat.

Haba malam kaima kasan ina iya ƙoƙarina, yadda ka shagoɓa Najwa ai ni bana yi mata da wasa, kawai dai halin ɗan yau ne ka haifa baka haifi halinka ba, fatanmu Allah ya sa wannan ya zama shine abu na ƙarshe yasa hanyar shiryuwarta ce.

Suka amsa da amin, kana Junaid ya fito ya wuce ɗakinsa ransa ba daɗi, ya rasa wani irin rayuwa Najwa ta zaɓarwa kanta sam bata lissafi, duk abin da yazo mata a rai shi take aikatawa ko da hakan zai cutar da ita, ba zai ce yarinta ke damunta ba kawai tsabar son rai ne yayi mata yawa, haka ya kwanta da tumani barkatai, farin cikinsa ɗaya da Mujaheed ɗin yana sonta dan yaga haka ƙarara a idanunsa.

Washe gari.

Duk yadda suke tsammanin lamarin ya wuce tunaninsu, domin tun safen suke zuba idon ganin dangin Mujaheed har zuwa dare ba amo ba labari, da yake baƙi duk sun watse a ranar gida ya rage sai su kaɗai, Najwa kam daga kwanciya ba abinda take yi ga damuwa yayi mata yawa dan ƙiri ƙiri duk pyan gidan sun ɗauki gaba da ita ba mai yi mata magana, kota gaishesu babu mai amsawa haka ta yini a ɗaki, abinci ma sai dai inna ta shigo mata da shi ba um ba um um. Wasa wasa aka shafe kwana biyu ba labarin 'yan uwan Mujaheed kuma shima bai zo ba domin mama tace in yaje bata yafe masa ba, dan dole sai ta nunawa Najwa kuskurenta yadda in ta dawo gidan zata natsu tayi abinda ya dace, Najwa wani rama tayi na ban tausayi saboda yawan zazzaɓin da take fama dashi, ka kaɗaici dan har lokacin ba mai shiga shirginta, wayarta ma Junaid ya amshe ba abinda zata yi da zai ɗebe mata kewa, ko kallon tv ma ba daɗi yake mata ba kuma har lokacin bawai tana son auren Mujaheed bane, kawai dai biyayya ta ɗauki ɗamarar yi domin ta rabu da su Inna lafiya, amma tasan zaman gidan Mujaheed tamkar zaman kurkuku ne wanda babu farin ciki a ciki, bata tunanin zata so shi balle ta iya yi masa biyayya, tunanin mafitar yadda auren ba zai jima ba kawai take yi dan hankalinta ya koma Kano, gwara ta koma ta auri Atiku duk da yana da muni amma yanada kuɗin da zata ji daɗin rayuwa, ta yarda da su Sameeha sun fita kuma ƙaddararsu ba zata zama ɗaya ba amma tana buƙatar ace itama ta auri wani taji daɗin aure kamar yadda suma suke ji, haka take yini tunani da kuka babu abinda inna take sata tayi mata, ba mai hira da ita ba wayar da zata yi magana da mutane chart balle ta samu wacce zata fallasa sirrin dake ranta, tasan Anty Saleema ce kaɗai zata saurareta harta bata taimako da shawara, fushin da take da ita yasa ma bata zo bikin ba, tasan kuma In ta kirata ta bata haƙuri har ta sako zancen Atiku ƙila ta saurareta tunda itama tanada burin daya sa take so ta aureshi. Ganin fa in bata miƙe ta nimawa kanta mafita ba haka zata ƙare a kwance, hakan yasa ta miƙe ta fito daga ɗaki ta shiga ɗakin baba ta ɗauko wayar Inna data aje a nan, sai ta dawo ɗaki ta kwanta, dama innar ta shiga wanka ne, sai ta fara tunanin wanda zata kira a lokacin, Umma ce ta faɗo mata a rai dan tasan ita ce kaɗai zata iya taimakonta, dan tana da tabbacin bata san tana gida ba.

****

Sameeha.

Tun sadda suka bar gidan Najwa suka sauke matan da suka É—auka a bakin titin gidansu Najwan sai suka wuce, Sameeha ta kalli umma tana cewa.

Umma kinga inda Allah ya kai Najwa, kuma ba laifi gidanta yayi kyau kawai dai bata samu yadda take so ba, dan ina ganin Allah yasa ta zauna dan kamar ba haka taso ganin gidanta ba.

In Sha Allah zata zauna ai so ba samu bane, mu bita da fatan alkhairi.
Chapter 95 · 0% Book details