Sashe 40
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haba inna ke da zaki tayani murna shine zaki fara korafi, tun yaushe kike so kiga na fito da miji na yi aure, amma kike niman ki sakar mini da guiwa.
Ni bawai bana murna bane kawai dai naga yaron nan bai taɓa zuwa wajen babanku ya nima izini ba ko ya turo a niman masa, sai kawai maganar aure, dama shi zancen ne kike yiwa ihu? na ɗauka ma ko mummunar labari aka baki.
Zencen kenan inna.
To Allah ya kyauta ni ki fito ki É—aura sanwa biyar ta wuce, in babanku ya dawo zan sanar da shi muji ranar da zasu zo.
To Najwa tace jiki na rawa ta aje wayarta ta fito ta cigaba da haÉ—a wutar , alla alla take ta gama ta koma É—aki ta bawa Nafeesa labarin abinda ke faruwa, da duk ta sare ganin an shafe watanni ba wata magana har cewa Nafeesa take yi kamar dai auren ba zai yuwu ba, da alama ita ba tada sa'a ga Sameeha ta fita amma kuma shigarta gidan yana niman ya zama wahala, Binafa tace ko zasu gwada shiga malamai ne a karkato da hankalin Aminu, Najwa tace shagalarta bai kai nan ba dan haka zata cigaba da gwada sa'arta idan kuma lamarin ya ci tura sai su kauce hanya duk da ba hakan take so ba.
Sai bayan sallar Isha'i Najwa ta samu kanta wanda a lokacin ta kira Nafeesa ta faɗa mata, ba ƙaramin murna tayi ba tace washe gari zata zo tare da Binafa dan su tayata murna, tace ba damuwa sai sun zo, nan dai ta hau online ta fara sakin status da wasu maganganu mai harshen damo, wanda yake nuna tana cikin farin ciki, wanɗanda suka gani suka kasa shuru sai da suka tanka tace ba komai tare da gindawo ƙarya, Ikram ma tana cikin waɗanda suka yi mata magana akan.
Allah yasa ba wani kika cuta ba kike murna, dan nasan halinki uwar yaudara.
Bana son tashin kanhali karki farraka mini farin cikin da nake ciki, kuma Zaidu ne nace bana so akai kasuwa idan ma dan shi kike wannan surutun.
Kanki ake ji, kuma wlh a juri zuwa rafi watarana dole tulu sai ya fashe.
Cewar Ikram Najwa ta rubuta mata tsaki tare da imoji na gwalo, Ikram bata ƙara bi takanta ba ta cigaba da chart da mutanenta. Inna a daren ta faɗawa baba yace su zo jibi Juma'a bayan sallar magariba ko isha'i. Inna tazo ta faɗa mata nan take ta kira Hauwa ta sanar da ita, ranar Najwa da Hauwa sunyi kwanan farin cikin da suka jima basu yi shi ba.
******
Ranar Juma'a.
Kamar yadda suka tsara hakan ta kasance Yaya Alhassan Kamalu da Kawu Lawal da wani abokin Abba Alhaji Datti sune suka je nimawa Aminu auren Najwa, ba wani ja baba yace ya basu dan yarinya tace tana so kuma ba zai yi mata auren dole ba, ganin Baba yasan Alhaji datti ya kuma ce ɗan Amininsa ne daya rasu yasa shi saurin amincewa, sam Baba bai gane daga dangin mijin Sameeha bane tunda shekaru kusan goma sha ɗaya da yawa, sannan ma lokacin bikin Sameeha ɗaurin aure kawai yaje bai wayesu ba. Suka yanke sadaki dubu dari na gaisuwa dubu Hamsin sai kayan saka rana dubu Hamsin, nan suka basu musu dubu ɗari biyu cash 'yan dubu ɗai-ɗai, baba yayi matuƙar jin dadin tare da ɗan uwansa Malam Isyaku da kuma Junaid yayan Najwa, suka tsaida rana nan da wata shida mai zuwa lokacin azumi bai wuce wata guda ba, dan a lokacin ne Aminu ya buƙaci a saka rana a cewarsa lokacin ne ya kammala shiryawa, suka ce ba damuwa Allah ya kaimu, nan dai suka rabu cikin tsananin farin ciki suka tafi ko wanne yana sambarka, da baba ya sallami ɗan uwansa ya shiga gida ya kwalawa Inna kira a tsakar gida ta fito daga ɗaki tana amsawa, baba ya miƙa mata kuɗi dumus yana cewa.
Ɗiyarki dai tayi goshi dubu ɗari biyu aka amsa na aurenta, an tsaida rana nan da wata shida a ƙarshen watan, ranar ne kaɗai ba a faɗa ba ko Juma'a ko Asabar.
Malam daga zuwa ba wani bincike sai maganar aure gadan gadan har da saka rana.
Ke dalla abu ne ma na gida, nasan É—aya daga cikin manema auren kuma nan kusa suke unguwar dosa, kiyi fatan Allah yasa hakan alkhairi ne, yanzu kije ki adana kuÉ—in nan mu samu sayan mata kayan katako na MG furnitures, naji faÉ—i da aka saka bikin da nisa.
To Allah ya nuna mana yasa ayi damu ya kuma sanya alkhairi kaga muma saimu shirya a hankali ba gaggawa.
Cewar Inna baba yace hakane kam kana ya shiga É—akinsa, inna ta tafi É—akinta ta adana kudin ta fito ta shiga dakin Najwa da duk taji abinda suka tattauna, tayi murna cewar an kawo kuÉ—in aurenta na Aminu mijin Anty Sameeha da nan da kwanaki zata maye gurbinta, sai dai murnan ta bai kai zuciya ba ganin an saka bikin da nisa taso ace baifi wata biyu aka saka ba. Inna tace.
To hankalinki sai ya kwanta an kawo kuÉ—in aurenki kuma an saka rana wata shida.
Wlh inna na so wata biyu kawai aka saka ayi a huta.
Daƙuwa inna tayi mata.
Kin ci gidanku Najwa gabaÉ—aya kin zama fitsararriya na rasa meya sauya min ke duk ki canza hali.
Inna zamani ne fa mu ba irin mutanen da bane komai yanzu an waye.
Da rashin kunya ba. Allah dai ya kawo lokaci ki bar mini gida na huta da fitsaranki.
Amin Najwa tace a hankali Inna tace.
Au amsawa kika yi.
Uu um inna bance komai ba.
Najwa ta faÉ—a tana gumtse bakinta. Inna girgiza kai tayi ta wuce É—akinta, Najwa kam ta hau WhatsApp tana rubuta status.
_Ranar muke jira yau gashi ta zo, wato rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya._
Nan mutane suka yi mata ca da tambaya, sai duk tsuit banza dasu ta cigaba da hira da Nafeesa da take bata labari, ba zata so aurenta ya bayyana ba sai ya zo gab saboda akwai samarinta da take so ta cigaba da wankesu son ranta, dan tayi alƙawari a jikinsu zata samu kuɗin sayan wasu kayan kitchen.
...
Washe gari Asabar Inna ta tafi can gidansu ta sanar da 'yan uwanta, sannan tace in an kawo sweet da goro na saka rana zata aiko a rabawa dangi, daga nan ta wuce gidan su Sameeha dan ta faÉ—awa su Umma, koda taje ta samu Sameeha bata nan Umma tace mata taje kasuwa Ikram kuma lokacin ne ta dawo akan zata bi Sameeha Kasuwa su dawo tare, sai suka yi waya Sameeha tace a lokacin take shirin dawowa harma da zanen kayan da ta ce zata siyawa yaranta Ikram ta hanata.
****
Sameeha.
Da suka shigo kan titin Sabon kawo sun zo kan wani layi Khairy ta tsaida motarta a titi ta rage volume É—in wakar da suke saurare, ta na cewa Sameeha.
Wannan layin shine layin gidana idan kika shiga zaki ga wata makarantar boko private an rubuta Khairy nursery and primary academy. Ko makarantar kika shiga kice a kaiki gidan Ummulkairi maman Faisal za a nuna miki gidana.
Allah sarki aiko wata rana zaki ganni bari na samu abin hawa na ƙarasa, nagode Allah ya saka da alkhairi.
Sameeha tace tana tunanin makarantar ma nata ne a yadda ta faɗi kwatancen gidanta, to ko meye nawa a zuwa gidanta oho, tace a ranta sai ta juya tana ƙoƙarin buɗe motar Khairy tayi saurin saka shii a luck, da sauri ta waigo ƙirjinta na dukan uku uku, Khairy ta sakar mata murmushi.
Har gida zan kai ki domin na ƙarasa samun ladanki.
Wlh da kin barshi ai na kusa gida ko a kafa zan ƙarasa ma.
Hmmm Khairy tace cike da ƙarfin hali ta kunna mota suka ci-gaba da tafiya, Sameeha ta kasa cewa komai sai mamakin ƙarfin halinta kawai take yi, ta cigaba da kallon gefen hanya ba wanda ya cewa kowa komai har suka fara shiga rafin guza, sai Sameeha ta tsinkayi maganar Khairy.
Ina ne unguwarku.
Layi na biyu ne idan kin je sai ki sauke ni bakin hanya na kasara.
Murmushi Khairy tayi ta cigaba da tuƙi har suka kai kan layin Sameeha tana jiran ta tsaya sai taga ta shiga layin Khairy ko a jikinta, har tana jiman wuce gidansu sai ta dakatar da ita.
Ai mun kawo wannan gidan ne mai baƙin gate.
Masha Allah, na kawoki lafiya ba tare da na cutar da ke ba sai hankalinki ya kwanta dan naga a tsorace kike dani, ni kuma wlh zuciyata fes.
Murmushin yaƙe Sameeha tayi.
Haba karki É—auka haka kawai dai kin san yadda rayuwar take yanzu mutum ba abin yarda bane, amma yau ke kin cire mini shakka, Nagode sosai bari na shiga gida
Ba komai ga wayata ki saka mini number ɗinki mu riƙa gaisawa ko ta WhatsApp ne in kina yi. Sannan baki sanar dani sunan ba.
Sameeha ba wani ja ba ta amsa wayar tana murmushi ta saka mata number ɗinta sai ta miƙa mata, ta buɗe motar da yake ta yi unluck ɗin motar, tana fita Anwar yana fitowa daga gida yana ganin Sameeha ya taraso da sauri yana.
Anty Sameeha inna Rakiya tazo tare da Anty Kuluwa kuma innar Najwa tazo duk suna ciki.
To kai ina zaka suda mai bakin magana.
Pure water zan sayo na gida ya ƙare.
Ya bata amsa yana wucewa, Sameeha ta rufewa Khairy motar tana cewa.
Kiyi hakuri na tsaida ki, sunana Sameeha Ahmad maman Abi da Amrah.
Murmushi Khairy ta yi tana gyaɗa mata kai kana suka yi sallama ta ja motar baya tayi ribas duk akan idon Sameeha kana ta juya motar ta wuce tana danna mata hon Sameeha tana ɗaga mata hannu kana ta shiga gida. Tana isa falon umma ta tadda baƙi wato Ƙanwar umma inna Rakiya da 'yarta Kuluwa da suka zo daga Zaria, sai inna Zulai mahaifiyar Najwa,nan ta zauna suka gaisa kana suka shiga hira inna Rakiya na cewa.
Ai tun safe muka zo muna gidan baba nace nan zan kwana shiyasa na tawo da wuri muyi hira kuma zuwan ma kusan naki ne takanas.