Sashe 29
Abun Da Ciwo Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Aminu ya fito cikin shirin tafiya yasha manyan kaya, shima har rama yayi dan idanunsa zun zurma, fuskarsa a ɗaure ya isa ƙofar ɗakin Jamila ya buga, Jamila da tun asubahi ta farka ta kasa fitowa dan duk taji abinda ya faru a tsakaninsa da 'yan uwansa, tayi mamaki sosai daya ɓoye ganin 'yan matan nan a gidansa, kanta ya ɗaure sosai ga yadda abubuwa suka faru sannan suka cukuikuiye mata kai, da kyar ta samu barci ya ɗauketa a dare, kiran sallar asubahi ya tashe ta dan ta saka alarm da ringing ɗin kiran sallah, ta kasa fitowa ne dan bata san da wani ido zata kalli mutanan gidan ba, buga ƙofar ta yayi matuƙar ɗaga mata hankali dan a zabure ta sauko daga kan gadon tazo ta buɗe, tana ganin Aminu ne taja da baya zata koma ciki ya daka mata wata uwar tsawa.
Ina zaki koma munafuka, wato har kin iya haÉ—a munafurci ki kira Hauwa ki faÉ—a mata gidana ba lafiya ko, shiyasa ashe Sameeha tun farko taki yarda ki mata aiki ashe da gaskiyarta munafurci zaki haÉ—a mata, to maza ki haÉ—o kayanki yanzun nan na baki minti biyar ki bar mini gidana, in ba haka ba sai na saka 'yan sanda sun kamaki sun É—aure ki har sai igiya tayi rara.
Na shiga uku dan Allah Alhaji kayi hakuri yanzu zan tafi.
Ta faɗa cikin rawar murya, ta koma ciki ta ɗauki jakar gana mazgo ɗinta da tarkacenta dake waldrob ta zuba a jaka ta ɗauki wayarta ta zura hijab ta fito, haka Aminu ya tasa ƙeyar ta har gate yace idan ta bari ya ƙara ganin fuskarta ko a hanya ne sai ya karya ta, kuma munafurcin da tayi tayi a kuɗin aikinta na watan dan bazai bada ba, Haka ta wuce tana kukan baƙin ciki dan sosai ta gama lissafin kuɗin da zata haɗa a watan in an biyata, ta shiga jan ƙafa da gana mazgo a kanta tama rasa ina zata mufa, amma ya zama dole ta nima Najwa dan ita kaɗai ce zata taimaketa, kuma a yanzu ba zata iya zuwa gun Hauwa ba dan gani take kila ba zata amsheta ba kuma tana tsoron ta haɗu da Amimu a can.
[2/20, 7:27 PM] Rahma Kabir: *Littafin nan na kudi ne, don Allah da son annabi ku karfafa min guiwa, duk wanda ya ga wannan littafin ya siya result karanta domin hakkina ne. Pay N400 to 0106956864 Ramatu Muhammad Kabir Access bank (Diamond). Ko a biya a POS, ko a tura MTN card N400 a 09034940106, masu so ta pc su tura N700. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106. Dan Allah banda vtu.*
20.
Aminu ya koma cikin gida ya zaun falonsa ya rubutawa Sameeha takardan saki ukunta kana ya ɗauki abinda zai ɗauka ya fito falo ya aje mata takardan akan center table yasan zata gani ta ɗauka, sai ya fita zuwa ƙofar gate dan tuni mai motarsa yazo, ya buɗe mazaunin baya ya shiga ya zauna da bisimillah, nan take yaji hawaye ya cika masa ido tunawa da tare da Sameeha zasu tafi, sai ya shiga ambaton innalillahi... A zuciyarsa ya yi saurin share hawayen daya zubo masa tare da jin raɗaɗin rabuwa da matarsa wacce yake da yaƙinin ba zai taɓa samun kamar ta ba, a ganinsa sakin shine kawai mafita duk da ya yarda da rantsuwar da tayi masa akan bata aikata lesbian ba amma idan ya tuna yadda yaga 'yan matan a kanta sai zuciyarsa ta shiga gargada da shakku akan haka, shiyasa yaga rabuwarsu shine kawai mafi alheri. Ya gama yankewa ba zai ƙara aure ba tunda ba lafiya ce da shiba zai cigaba da rayuwa a haka har zuwa ranar da zai bar duniya, sosai zai inganta rayuwar yaranta domin su samu tagomashin duniya da lahira dan shi ne kaɗai gatan da zai nuna musu a yanzu, shiyasa ya yanke shawarar zai riƙe 'ya'yansa a hannunsa dan zai iya kulawa da su. Amma wani ɓangare na zuciyarsa kuma yana so ya kure tunanin Hauwa bisa takurawa rayuwarsa da tayi wanda yake ganin abinda take yi masa sam ba so bane face muzgunawa, shiyasa ya ce zai auri wacce tace ta samo masa, dan ya sakata cikin uku masifa kamar yadda ta addabi rayuwarsa data iyalinsa, lokaci yayi da zai nuna mata kurenta sannan ya samu damar haɗawa kwakwalwarta zafi dan sai ya gunnusa mata ya sakata a matsala, idan bai yi haka ba to bazai taɓa jin ya huce daka haushinta da yake ji ba. Wannan tunanin yasa shi tuna shekara shida baya daya wuce, saboda Hauwa itace ta zamo masa silar matsalar da yake ciki, duk da ƙaddararsa ce yazo a haka amma Hauwa ce sila.
Shekara shida daya wuce...
Lokacin Sameeha ta haifi Amrah da kusan mako guda dan sunyi taron sunansu a iya mutanen arzikin da suke hulɗa dasu a nan Lagos, ba wanda yazo daga kaduna saboda nisa da kuma yanayin tsadar rayuwa da mutane suka fara fuskanta a mulkin daya shuɗe, shiyasa kowa sai dai ya kirasu yayi musu barka, babu wanda ya aika musu da wani abin alheri sai umma itama kayan gyaran jiki ne da kuma kayan kuka daddawar miya da yaji, banda ita babu wanda yayi musu abu dan Aminu yace su barshi, Hauwa dama tace ita ba abinda zata bayar dan ƙarawa mai ƙarfi ƙarfi ne. Bayan kwana biyu da suna jikin mahaifiyarsu ya tashi sosai dan har an kwantar da ita a asibiti Aminu yaso zuwa amma suka ce ya barshi ta samu lafiya har an sallame su, to sai dai waya yake yi dasu akai akai yana jim jikinta dan har ita kanta umman tasu suna waya tana kwantar masa da hankali, hakan yasa Aminu ya saki ransa ya daina damuwa game da rashin lafiyar nata ya cigaba da harkan gabansa.
Bayan kwana biyar da sallamo Umma a ranar ta rasu bayan sallar la'asar wanda ciwon dai ya kuma tashi kirji da haki da yake damunta, kafin sukai ga asibiti tace ga garinku nan, kuma hakan yayi daidai da sati biyu da haihuwar Sameeha. Aminu yana cikin mota zai je gida saboda ya baro office ɗinsu, ganin gosilo zai ɓata masa lokaci yasa shi sauya hanya yabi ta baya inda mutane basu cika bi ba saboda rashin kyawun hanyar, yana tsaka da tuƙi Hauwa ta kirashi kamar bazai tdauka ba sai kuma ya fasa dan ɗazun yaga miscall ɗin yaya Kamalu, bai samu kiransa ba ya bari inya je gida ya kirashi, kuma dama ya kirashi ne ya faɗa masa jikin umma ya tashi sai bai ɗauka ba, hakan yasa ya riƙe kan mota da hannu ɗaya ya ɗauki wayar da hannun dama, kururuwar kukan Hauwa yaji tana magana da ƙarfi.
Aminu umma ta rasu yanzu nan, shikenan mun zama marayu ba Abba ga umma ta tafi ta barmu. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, kayi kokari kazo yau ku gana dan sunce kafin magrib za a kaita.
Aminu wani abu yaji ya sara masa a kai ga wani bugu da zuciyarsa tayi wanda nan take ta tsaya cak ta daina aiki, wayar ma faÉ—uwa tayi Hauwa tanata helo helo ganin bai amsa ba ta kashe wayar, shi kuma Aminu motar tasa tafiya ta cigaba da yi wanda bai san halin da yake ciki ba, nan motar ta sauka a hanya taje ta daki falwaya daya kusa karyewa, yana dakansa fol É—in ya faÉ—o kan motarsa hayaki ya fara fita daga injin motar, mutane sai ihu suke suna salati da kiran jesus, domin wani irin mugun hatsari ne ya auku wanda kowa ya sadakar wanda yake cikin motar ya mutu. An fitar da Aminu da kyar a cikin motar dan saida akayi kokarin daga falwayar kafin aka fito da shi jina jina baya ko motsi, haka aka kai shi asibiti cikin mutuwa ko rai.