← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 87

Sashe 9

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yake yiwa magana a haka ya sake talabo fuskarta kasa kasa ya ce" Menene? Bakya so a kaiki asibiti ko?" A hankali Auta ta gyada kanta, sannan ta dago idannuwanta ta dube shi muryarta a raunane ta ce" Ni ba mahaukaciya bace ABAHNA kar a kaini ka ji?" "Ahaf, idan ba haukan ba me zai saka aikata wani aikin yar nan? Yayanki ne fa kike ce masa ABA, ai ke ba magajiyarsa bace, kuma wannan zama haka ai idan ba ana cikin hali na rashin hayaci ba ba za'a aikatashi ba sam" bafansu ya fada yana dan kada kafa Kasa kasa ta dan mike ta dauki jus din dake ajiye ta kai gabansa ta ajiye masa, cikin dabara ta saka kafarta ta take tasa da karfi, harda murzawa sannan ta koma baya ta zauna tana murmushin yake ta ce" Aa fa bafansu, ba za'a kai min yarinya asibiti ba, a nan din ai zata fi saukewa idan tana ganninmu a gefenta, a hankali sai ka ga kamar ba'a yi ba, tunda likita yace ciwonta na dan lokaci ne, damuwa ce ta haifar mata da shi, idan har ta samu kwonciyar hankali ko yayane zata samu sauki" UMUGHLUK dake rike da ita idannuwansa a lumshe, zuciyarsa na tafarfasa ya dan ja hannunsa a hankali wanda ta nitsa masa farce ya sake dago fuskarta ya ce" Auta, kina ji? Tashi ki je ki kimtsa kayanki kin ji? Sai mu tafi ko? Ki shiryasu sosai fa, ki saka harda bruch da maganinki duka kin ji?" Wata irin ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi ta mike tana sauri harda hade tafiyarta ta yi waje , wanda ke nuni da kamar wani irin farin ciki ta ji na furucin nan A hankali ya juyo inda Bafansa yake ya dan wara kafafuwansa ya dora hannayensa biyu a saman gwuiwoyinsa ya kai hannunsa wajen gashin kansa dake daure ya fan shafa kadan sannan ya saka idannuwansa cikin na Bafansa , A kausashe ya ce" Bismillah " Bafansa na zarar ido ya dago shima yana sake kallonsa, dan sai ya ji kamar amon muryarsa yanzu ba daya ba da ta dazu A dan rikice kadan ya ce" Dangane da abinda ya faru ne dama jiya na kasa zama nace zan zo" Shiru ya yi ko zai ji ya yi magana? Sai ya ji bai ce komai ba Bafansa ya ci gaba da fadin" Ka san lamarin mata ne da rashin jin magana, ka yafe masu ba zasu kuma ba in sha Allah " Ikon Allah kawai yake kallo, kwata kwata bafansa bashida wayo bale tunani Kai ya fan girgiza yana cire dubansa kadan ya ce" Ok ba damuwa" Da mamaki ya kalle shi, kasa rike mamakinsa ya yi ya ce" Kana nufin komai ya wuce kennan?" ASADEEK ya muke tsaye , gaba daya tsayinsa ya mike a gabansu Dan murmushi ya yi ya dubi Ummansu dake zaune kanta sade kwata kwata bata damu da maganar da suke yi ba, ya tabata ta shigo ne dan a kimtsa masa kayan tafiyarsa, yana son fada mata umura fa ya nufa yana kuma cewa ba zai fada mata ba zai mata surprise ne idan ta je su hade a cen Dubansa ya maida kan BAFANSA a hankali ya ce" Babu wata damuwa ai, Mata ne, bakinsu bashida linzami sai sun samu dorinar da ta daki bangonsu..............., Allah ya takaita ama ina tsoron fushin da dogarai suka dauka, harfa cewa BABAYE ya yi in ba dan bafana kake ba, me ya hauda kai saman karaga bayan dan kaka hajia kake ba dan kaka elhaji ba?" Gabansa sai da ya kwonci kwonci ya fadi har ya mike tsaye cirr daga zaunen da yake hannayensa na rawa Da sauri ya ambaci sunnansa gannin ya juya ya nufi uwar dakansa, sai dai bai tsaya ba Da sauri ya daga kafarsa da nufin binsa, sai dai ya dakata da karfi yana kallonta gabansa naa faduwa Da idannuwanta ta masa nuni da waje sannan ta sake shi da sauri ta fara ficewa ta nufi bangarensa Tana tsaye a dakin tana kai kawo ya bude ya shigo hankalinsa a mugun tashe ya nufota yana fadin " Me wancen marar mutuncin yake nufi? Me yake nufi da furucinsa a kaina?" Da sauri ta karaso ta dora hannunta saman lebensa tana fadin" Shuiiiiit, safiya ce, WA'INDA ke jira yace a yi sun fara bazuwa ka rufawa harshenka asiri kar tun daga nan ya kirayi Sarkin damagaram su tujeka daga kujerar mu shiga uku baki dayanmu!" Yanzun kam tsakaninsa da Allah jikinsa rawa yake Zaune ya kai dan ba zai iya jure tsayuwar ba, muryarsa na rawa ya ce" Me yake nufi da ni? Yaya zan yi kennan?" Idannuwanta ta wanna tamkar wata yarinyar mace ta zauna itama a daf da shi sosai tana kallonsa ta ce" Abunda yake nufi da kai ramuwar gaya ce, abinda zaka yi kuma a yanzu idan ka saurareni ina iya saka ka a hanya!" Fuskantarta ya yi sosai dan haka ta yi murmushi ta ce" INA BAHIJA?" Zufar dake gaban goshinsa ya share yana sake jan ajiyar zuciya yana jin meye na tambayar Bahija bayan ba wannan ya kawo shi ba, ba shine matsalar ba! A takaice ya ce" Tana Hotel zata je Umarah wai bana!, Ki min maganar da kika ce mana" Murmushi ta yi ta sake gyara zamanta ta ce" Dama shawarata a gareka itace, ka sake samunsa wannan karron tare da Gimbiya, ku zauna a saman cafet ku zanta, ka dube shi ka bashi hakuri mai sunnan hakuri, sannan ka nuna masa ka zo da maganar bashi yarinyarka mace kwalin kwal ya aura!" Ido ya zarro yana kallonta Da mamaki ya ce" Lalle yau na fara tunanin ke ya dace ki hadiyi maganin saka barcin nan na wancen mahaukaciyar kanwar tasa ba ita ba!, Kina nufin ni na dauki yarinyata na bashi? Kyan zata zauna kallo har duniya ta nade ne ko me? " Kai ta girgiza tana safe dafe kanta, lalle wannan mutumen babu mahaukaci irinsa, ba kuma zai taba zama mai hankali ba Sai dai tunda so take yi su fuskanci junna sai ta sake tausasa muryarta ta ce" Ka gane inda na dosa mana Aban BAHIJA, kasancewar babu abinda zai iya yi matan na kwadaita mana haka, sannan zamu jefi tsuntsu biyu da jifa guda ne!" Kallon me kuke nufi yake yi mata, dan haka ta sake gyara zamanta ta ce" Ka san menene burinmu, wanda muke fata yaron nan kar ya jima a saman kujerar mulki, idan yau BAHIJA ta zamto iyalinsa hakan na nufin itace mafi kusanci da shi fiye da kowani dan Adam a duniya, ta haka a kwanaki kalilan tana iya kawo karshen rayuwarsa, kai ka gaje abinda ya gada cikin ruwan sanyi ba tare da mun wahala baki dayanmu ba, sannan ta fita ta auri wanda take so ko?" Ido ya zuba mata sosai yana kallonta Bai san lokacin da wani murmushi ya kubuce masa ba, Da sauri ya mike yana fadin" Bara na koma na ganshi yanzuma" Hannunta ta saka ta janyo shi har sai da ya zauna daf da cinyarta, a hankali ta dora hannunta saman cinyarsa ta dan matsa ta ce" Ka manta tafiar yamacin nan zai yi? Ai ba zaka samu kebewa da shi ba kuma , inaga zai nufi kasashen turai ya huta ne, ka zauna kawai zan je na hanna wancen mahaukaciyar binsa, domin idan har ta bi shi komai na iya faruwa, ka bari idan ya dawo sai ku zo da Gimbiya ku same shi, nima zan kasance a wajen kafin lokacin dan na tayamu yaki" Cike da bege ya rakata da kallo har ta gama bada sawunta ta tsaya ta gamsu da hanyar ba mai ganninta ta fita da sauri ta nufi bangaren AUTA Karar bude kofar ya sakata dagowa da sauri daga cusa hijabanta da take yi a cikik akwatinta ta juyo Gabanta ya sake yankewa ya fadi da sauri ta zauna ta hade gwuiwoyinta ta dora kanta a sama tana yin gaba da baya kamar tana zizigar jariri a bayanta , tsoro da faduwar gaba sun cikata Dakin ta rufe da ky ta karasa inda take zaunen nan ta duka cike da takaici ta ce" Ina kike tunanin zuwa? Ama bakida hankali yarinyar nan kwata kwata!, To bari ki ji, idan har kika yarda kika bi yayanki tafiyar da zai yi na rantse maki da wanda raina yake hannunsa kina dawowa zan makala maki mugun sharin da yayanki da kansa zai haka rami ya saka ki kanki a fili sannan ya jefe ki da duwatsu har sai kin rasa ranki......, Ke kin san ciwon wannan zai halaka shi shima dan makahon son da yake maki!, Ta rage naki , ki duba ki ga abinda zai gyara ki!" A hankali ta dafe zuciyarta ta silale a kasa ta dora kanta a saman akwatinta ta rintse idannuwanta A bayane ta furta" ALLAHU AJURNI FI MASIBATI, WA KHALIFUNI KHAIRAN MINE HA....." sai kuma ta karashe tana mai sakin kuka tana jin kanta tamkar zai tarwatse gida biyu A hankali ta sake dafe gaban kirjinta, ita ba waya ba, ita ba komai ba, an amshe , yanzun a barta ta je ta yi ibadar ko zata sake neman gafarar ubangijinta da fatan ta gama da duniya lafiyama ba zata samu ba? Lalle ta fara kulatar mijinta, shin ina yake ya bari ake neman kasheta? Ba zai lekota ya ga amanar da aka bashi ba? Ba zai nemi ganninta ba ko zai karanci damuwarta? Ko dan ta rasa cikin dake jikinta ne ya tsaneta?....... A wannan rana sallah kawai take tashi ta gabatar ta koma ta nade, har lokacin tafia ta yi, tana ji tana gani ta gilawa yayanta karyar juwa take ji ba zata iya tafiyar ba, zata je haji idan Allah ya nufa, tana ji tana gani ya mata salama ya fice tamkar zata mutu dan tashin hankali, sai dai ta sake mayar da kanta ta sha madarar ruwa ta kuma fuskantar alkibla, ta san Allah yana gani, ta kuma san idan bata ga warwarewar matsalarta a duniya ba tabas a kiyama Allah zai saka mata, dan haka sai ta ringa kai masa kukanta tana fada masa yayanta dai, yayanta dai, domin babu babar fargabar da ta
Chapter 9 · 0% Book details