Sashe 76
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aikin kwatar rayukanmu muke yi tukuru, ba ji ba gani, innata na tare da ni a nan, ta zubar da gidanta, ta baro mijinta dan burinmu , mu yi mu gama muma mu samu sa'ida, ko kuma akoy lauje cikin nadi ne? Ina nufin ko kuma idan muka gama aikin ba za'a barmu bane muke ciki haikan?" Umma ta kama gefen hijabinta ta ringa ja Inna na ja, a birkice ta ce" Ki cika min hijabi mana na samu damar yin magana!" Inna Hindu da kyar ta sakar mata Hijabin Ama ta yi wata tsayuwa ta kaka gida a gabanta Umma ta yi tsaki ta ce" Kawai daga jin magana sai ki nemi zuba min komai saman kaina bayan nima abinda aka kirayeni aka sanar min kennan har na fito ko alkyaba babu a jikina?, Kun zo kunna ta sakin magangannu a gaban yarinyar nan duda ni ba tsoronta nake ji ba kuma inada damar da zan sakata yin shiru koda a gabanta na aikata aikin nan, ama ku fa?, Zaku zo ku yi tsaye kunna wasu irin abubuwa bayan muma abinda ya daga mana hankali kennan ana cen ana nemansu?" "Ana neman wa? Waye yake neman wa? Da wace siga? Da wani dalili? Ta yaya?, Dan girman Allah ki sanar mana abinda kuke nufi , wani nema zaku yi ne bayan mun san me yake nade a harshenku bayan kyakyawan furuci da shinfidadiyar fuska mai fara'a?" NADIRAH ta sake fada, a wani irin sanyaye, wara irin juwa na dibanta, tana ta son rike abu ama babu abinda zata iya rikewa karshe sai da ta samu kanta a kasa warwas domin Juwar nan sai da tamakata a kasssss A rikice su biyu suka yi kanta, watau Auta da Inna Hindu Taimaka mata suka yi suka jinginar da ita da kujera Auta hankalinta na sake tashi Umma ce ta ci gaba da magana, babu abinda ya dameta da faduwar ta NADIRAH , itama damuwarta ta isheta ana neman dora masu laifin sace mutanen da basu sace ba, a sanninta dau basu sace din ba, in dai ba sarauniyar Tanus ta saka aka sace din ba to fa bata da takamaimiyar amsa , da son convincng dinsu ta ce" Cewa ta yi an fito daga masalaci suka yi fada shi da wani mutun a gaban kowa mutumen ya ce sai ya kashe shi da danginsa baki daya, kuma ga sheda nan an kwashe su, an ce mutumen kamar wani kasurgumin dan ta'ada, wai yannayin halitarsa mai saka a ji tsoronsa ne , shikenan sai ku ce mu ne? Mu bamu dauke su ba" Zuciyarta dake beating da karfi ta dafe tana lumshe idannuwanta zazafan hawayenta suka shiga gangarowa a saman kumatunta Innalilahi wa inna ilaihi raj'une Dishi dishi take kallon yadda rigima ta kaure tsakanin innarta da UMMA babu mai ba yar uwarsa hakuri, ita kuma auta magangannun dake fitowa daga bakinsu ke neman tsayar da numfashinta, bata san haukan nata ne ya motsa ba ko menene har take tunanin matar da take ji a ranta a yanzu fiye da kowace mace a matsayin yar uwa rabin jiki, da matar da take kira Mamah bayan mahaifiyarta ba ainahin wace take zato bace na neman sakata jin kamar zata shiga a hali na hauka ya saka babu wanda ya ji motsin NADIRAH, basu ankara da ficewarta ba, sai karar rufe kofar da suka ji wace ita dinma dan ta murda Ky din wajenta da ta cire ta mayar da shi ta baya ta rufe suka gane cewar wani zai shigo, ko wani ya fita Cikin Umma daga sama sai da ya dawo kasa, lokaci daya ya shiga bada wani kuka kuuuuuuuuuuuu alamu na gudawa na tatara kanta sannan wata makirar zufa irin ta saman goshin nan tace Bismillah, lokaci daya ta karra jin bata yaba fuskantar fargaba da tashin hankali irin na yau, lokaci daya kuma wajen ya dauki shiru ya zanto kamar babu wata halita a wajen , kowa ya yi tsittt hanyar yake kallo da jiran wanda zai shigo, dan babu wanda ya gane cewar fita aka yi, ba shigowa ake son yi ba Wanzuwar shirun da ya yi yawa ya saka INNA HINDU karasawa ta leka Idannuwanta ta kankance tana hango abinda take gani, watau babu KY din wajen, Hakan ya sakata zarro ido ta juyo tana kallon UMMA da a lokacin take ji a cikin jikinta kamar lokacinta ne ya yi, irin yadda zuciyarta ke dokawa da karfin masifa kamar zata bar gangar jikinta Sai da ta watsa Hannayenta, sannan da bakinta ta ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 5 Sai da ta watsa Hannayenta sannan da bakinta ta ce" Inna Indi?" Gaba daya sai Umma Ta nemi neman wacece Indi a cikin kwakwaluwarta, dan harga Allah a irin lokacin ba lallene in ta tuna sunnanta na kantama bale wai wani Indi Wajen da take Innar ta kai dubanta, sai kuma ta kai zaune ta saka hannayenta biyu kaf ta rangada tagumi kasa kasa tana fadin" Yau kam ana falatsin uwar kowa a gidan nan, ta yiwu bamu san inda su Auntyn suke ba za'a yi tsirenmu da ranmu, kun saka mu a masifa muna zamanmu a lungunmu, na tabata ba zai saurari maganar kowa ba zai hada jiji da jan kanwa ne ya mana cakuden luguden surfen uwar kishiya, innalilahi wa inna ilaihi rajune Indi zuwa kika yi wajensa ki ce masa me?" "Wace Indi? Ta je ina?" Umma ke fada bakinta har yana hadewa Inna Hindu ta ki bata Amsa, da kanta ta gane wace ake nufi, hakan ya sakata kaiwa kasa tana dora hannayenta bibiyu a saman kanta idannuwanta tamkar zasu fado kasa ta ce"Ban gane ba, me zata je ta yi? Tana ina? Dama mahaukaciya ce ita? Bata san ba'a wasa da wuta ba?" Guguwa ce? Kusar kan INNA TA HABU MAKADI ce ta kunce? Menene ya sauka a kanta mai karfin da bai ji komai ba, ya kwasheta daga inda take ta rarafa ta dauke fuskar UMMA da wani mahaukacin marin da ya saka Auta faduwa ta yi zaman yan bori sannan ta dora hannayenta saman kanta tana neman haukacewa Bata gama tantance hannun surfe ba inna ta rike hijabinta da kyau ta ce" Kwarankwatsa ki ce tak na tataka ki a wajen nan, ke baki san na jima ina dakon fuskarki ba zaki dubi idona ki ce yar Hindu mahaukaciya? Kin kusa gama aikata laifi a duniya in dai kina hadawa da irin wannan dan ni ba zan kyaleki ba kafin ki je mai sama ya tambayeki, banza shashasha abinda kike tunani ta je ta yi in dai Indi ce, sai mu zauna gaba dayanmu mu jirayi sakamako dan na tabata a yau yau din nan ba juma'a ba ba litinin ba zamu je inda ba kofa bale taga a ci ubanmu!, Dilla sai tsamin kwartaye kike yi!" "Wayo Allahna, Mamah wai me yake faruwa wayo na shiga uku me yake faruwa ne?" Hindu ta saki wuyan Umma dake kici kici din kwace kanta Umma ta mike tsaye fuskarta har ta nuna alamu ranta a bace ta ce" Ni kika mara? Ni kika daukewa hannu a fuskata? Zaki gane maganata da taki ba daya take ba a wajen yarona , zaki gane ke din ba kowa bace ba idan na je na same shi na fada masa su waye ku, zaki san shari iyawa ne idan kika samu kanki dumu dumu a cikin laifin da baki san hawansa baki san saukarsa ba, harta laifin kisa a yau sai ya hau wuyanki zaki gani" Inna ta daga murya tana rakata da fadin" Sai me, da kisa da ba kisa ba mun san yau sai an ci ubanmu, ki fitar da kan naki, dama ai mun san hakan na iya faruwa !" Tana bacewa ganninta sai kuma ta dora hannayenta biyu tana fadin" Wayo Allahna, ta yiwu habunma ba zan kuma gani ba, Yar Hindu an yi y'a gatanan dai ba tsari, maimakun ki tsaya a san ta inda za'a hau kya tarda zaki ki kai masa nama? Yanzun ko a wace take ciki? Ta yiwu ya yi gunduwa gunduwa da ita, bale ni yar tsurut da ni kamar sauran maye" Hawaye na balewa a saman kumatunta ta kuma cewa" Mamah ina ta magana kin kyaleni, gaba daya kin min shiru, bayan ina ta jin maganganun da ba dadi daga bakinki da bakin Umma?, Mama me yake faruwa ne? Sai na ji wai kamar wai wai wai......" Wasu hawayen suka kuma balewa a saman kumatunta shap shap shap tana kallon Hindu, wace itama jikinta a mace yake ainun ita din take kallo Hannayenta ta miko mata , hakan ya sa ta rarafa ta karasa inda take zaune ta zauna hadi da dora kanta a saman cinyarta Ajiyar zuciya take saukewa, a sanyaye ta ce" Auta, Dole fa sai kin yi yaki da kuka, da rikicewa, da saurin nuna tsoro, sannan sai kin dage da addu'a, na dan kina yi, na kuma san kina da hakuri, ina so ki ninka ne, in ba haka ba kema shafeki zata yi daga doron kasa kin ji?" Auta ta dago tana kallon Inma, muryarta a raunane ta ce" Mamah, tsoronta nake ji sosai, ama yanzu da kuke nan na rage jin tsoronta walahi, kin ga Mamah na tabata ba zaku bari ta cuta min ba ko?" Hindu ta lumshe idannuwanta zuciyarta na yin rauni A sanyaye ta ce" Mu fa bamu isa mu saka ko mu hanna ba, muma da kika ganmu a nan ta ranmu muke , kin ga an wayi gari babu danginmu, babu mahaifiyar NADIRAH, kuma babu mahaifinta, gashi ta je ta tona mu da kanta, bayan shi din baya ragawa masu laifi irinmu" Irin yadda ta kureta da ido ne ya saka Hindu sauke nata idannuwan, a raunane ta ce" Bari ki ji su waye mu, ta yiwu ke zaki yarda da mu, sannan ki yi mana kyakyawar fahimta ko?" Auta dai gaba daya magangannun bakinta sun shafe sai kallon Inna take yi Inna ta shiga warware mata dukkan abinda ya faru a sanyaye, tun tana fada idannuwanta na kallon kas