Sashe 44
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sha Allah da safe zan mata dogon kwatance na gaisuwarsa, dole ne ta bi dan gudun tonuwar asorinmu baki daya kin ji Innarta?" HINDU ta gyada kai bata ce komai ba Fadime ta ce" Ki daina kukan haka, ke da zaki karfafeta, Mari ai da sauki a kan abinda take iya samu matsayin hukunci, ta yi garaje Innarta, ba'a haka, ai Allah ne ya nada sarki kuma yace a yi masa biyaya ko?" HINDU ta gyada kai, a hankali ta ce" Kuma Allah ne ya halata wasa tsakanin miji da mata, ya halata sakewa da hira tsakanin miji da mata, wace ta zarce tsakanin kowa, bai bambance cewa matan sarakai kar su yi irin haka a tsakaninsu ba ko?" "HINDU, kar ki manta tsakanin da abinda ke boye, " Fadime ta fada Hindu ta ce" Shinema abinda ya fi sakani gannin idan yata ta kula alaka ta sabo da shi, zai zo mana da sauki, ina gannin a yadda ake zuzuta daukan mataki a kan laifi a wajensa ta fito da gala mai girma tunda bai dauka a kanta ba, Aunty sabo yana da dadi" FADIME ta ce" Haka ne, ama ta iya takun rawarta, kar ta bata ta da tsale, ta iya kame bakinta kar a yi mata kallon wace tale da sakin kai da halaya irin na yan gajaliya, ta kasamce mai taushi dan mace take, uwa uba kar tace zata takaita tafiyar dan zuwa ta yi ta koma, babu abinda ya gagari yarki, kin sani sarai, idan har ta saka gagawa ko raini a ciki, zata sa a gane da wuri a daura mata laifin komai da komai, bayan ita laifinta daya ne tak a tafiyar nan, yiwa iyayenta biyaya" A sanyaye HINDU ta amsata, suka ci gaba fa zantawa, a yau din Fadime din da kanta tace lalle tana so HINDU ta fan karra zama kadan, ba dan komai na, sai dan ta wanke kanta, abinda NADIRAH zata fara da shi dan wanke kanta shine aikawa da sakon zata ziyarci kishiyarta, daga nan idan sun je ta nemi alfarmar ta mata rakiya ta ba UMUGHLUK ITIBEL hakuri domin rashin lafiya ta dakata yin wasu abubuwa mararsa dadi, harta abinda ya dace ta fadi a gaban UMUGHLUK ITIBEL FADIME tana ta sanarwa HINDU, har dai ta dan fahimci wasu abubuwan sannan suka yi salama ____________________________________ Washe gari daga masalaci yana dawowa ya shige ciki ya kimtsa sannan ya sauko dan ganawa da SHEIK Umarni ya bada kan kar wanda ya shigo, yana da bako Sheikh dai kallonsa yake yi, dan ya fuskanci ko barcin kirki bai samu ba A nutse ya dubi SHEIK ya ce" Yarinyar da suka aura min, ba wace na sani bace" A nutse Sheik ya dake fuskantarsa, a hankali ya ce" Bam fahimta ba, Allah ya taimakeka" "Ina nufin wace aka ce da kai itace Bahija, ba ita bace" ya bashi amsa yana dan hade hannayensa Sheikh ya dake dubansa da mamaki ya ce"Ban fa fahimci yarenka ba, Allah ya karra maka lafiya" ASADEEK ya ce" Abinda kake ji shi nake nufi, ita yarinyar ta wajensu mun yi tafiya da ita Haji, na ganta, na kuma santa,wace na gani jiya ba ita bace" Gaban Sheik sai da ya fadi dan abin wani iri ya ji, ya gyara zamansa shima da kyau ya ce" Wannan wace irin magana ce, gaba daya na kasa gane inda ta dosa, ba ita bace? Wacece? Me hakan yake nufi? Yaya aka yi ka iya ganewa cewa ba ita bace kai da baka yiwa mutun kallon tsaf?, Mahaifinta fa ya jadada min cewa ita ce, sunnanta na kirki ne NADIRAH, ama ana mata kiranye da Bahija a lokacin da na tambayeshi dama Bahija sunnanta NADIRAH? Duba da ka sanar min sunnan yarinyar" Komawa ya yi ya zauna da kyau yana lumshe idannuwansa, ya jima a haka sannan yaa sake budar bakinsa a nutse ya ce" Idanma wacece wamcen, wata ce daban, wace ba Bahijar ba, domin bahijar a yanzu haka tana Tanut, wannan kuwa zan iya ce maka kamar ba yar cikin gida bama, dan ta fi kama da yar fashi!" A zaburw Sheikh ya sake dubansa da yannayi na mugun mamakin sunnan da ya hada yarinyar da ita Bakinsa har yana hadewa ya ce" Subahanalah yar fashi kuma?" ASADEEK ya gyada kansa, sannan ya nunawa SHEIK wajen kujerar da yake zaune ya ce" Ka ga a nan, a nan ta kalleni shekeke tace min sannu da saukowa,wai sannu da saukowa, ko daga ina? Kamar ta sha kwaya a lokacin dan na kula tana ta layi, sai da aka rufa mata alkyaba fa, kowa na duke yarinyar tsayina da nata a laye, inaga in ba yar fashi ba to bata da hankali" Sheikh bai san lokacin da ya ringa juya kai yana ambaton Allah da mugun mamaki ba, toh fa, gaskiya ne akoy matsala a tare da yarinyar, yo ko ba yar sarauta bace ai mugun mugun girmansa na sakawa a duka gaishe shi fa, kuma gaisuwar ce kanta sai a hankali gaskiya, oh ya godewa Allah da baya nan Sai kuma ya samu kansa da damuwa da tunanin ama me ya sa Bafan ASADEEK zai aikata haka? Da yannayin damuwar ya fitar da tambayar ASADEEK ya dube shi ya ce"Ni bama wannan ba, Bafa ina iya ajiye haka a wani bigiri daban, tambayar da nake son yi yanzu shine Umma, shin UMMA bata san Bahijar bane kafin auren ko menene?, Na ga ita ta amso yarinyar ita kuma ta ci gaba da gabatar da ita matsayin Bahija, ina so a kirawota yanzu dan kaina ya fita daga duhu" A hankali SHEIK ya fuskanceshi, a sanyaye ya ce" Ni kuwa da zaka amince da na kawo wata shawarar Allah ya karra maka lafiya" Dubansa ASADEEK yake yi, har ya yi niya dan kansa ya furta" Ina sauraro" SHEIK ya sauke ajiyar zuciya , cike da yannayi na son convincing dinsa ya ce" a lamarin nan ina hangen wata sarkakiya, wace da son samu na yi, mu bita a hankali, sannan mu hadata da ayar Allah, Allah ya taimakeka na tabata ko a yanzu da muka dan fahimci wani abin, ina nufin wanu abin ya fito fili Allah ne ya haska mana, ba isanmu, da dabararmu ba......, " UMUGHLUK ITIBEL ya sake dubansa, a nutse yana fitar da harufan a daidaice ya ce" Kana nufin, na yi shiru ko Umma kar na fadawa maganar nan?, Kana nufin na yi shiru a gaban yarinyar nan karama kamar mai shigar aljannu ina kallonta a matsayin wace ba ita ba?, Kennan ni abinda nake jirab sani da wancen din fa ya fadi a banza? Sai na salameta ta tafi tunda babu amfani dama wannan ne anfaninta" Ido Sheikh ya tsura masa, duba yake yi masa irin na dama na san da wata manufar ka aminta da maganar auren nan, Fuska ya hade sosai yana dauke kansa, irin baya so a sake dauko maganar kwata kwata, domin ba irin tsarewar da Cheik bai yi masa ba a kan maganar ya nuna masa ba wani abu a kasa aure aka bashi ya amsa, CHEIK ya gyada kai yana sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Ko me yake boye a cikin lamarin nan kamar yadda nace ne, ba rikicinmu zai bamu ba, sannan ka sani a yanzu ina so ka rufe mata wannan magana, ko me take kunshe da shi ka kyaleta, kuma wannan yarinya da daya rana kar ka nuna mata ka san komai, hasalima ka jata a jikinka ko zamu fahimci abinda yake boye, kar ka manta Allah na fitar da fari a cikin baki, yakan kuma fitar da baki a cikin fari, Allah ya karra maka lafiya da nisan kwana bamu san me hakan yake nufi ba, ama zamu bashi damar bayanar mana da kansa in sha Allah " Numfashi ya sauke , ya mayar da kansa ya jinginar, A hankali ya furta" Zan yi tunani a kai" CHEIK ya amsa da "Allah ya baka ikon yarda da abinda na ce" Shi dai daga nan bai ce masa komai ba, girmama girman rainin yake yi a zuciyarsa, kuma yana tunanin anya zai iya boyewa Umma kuwa? Idan ya boye mata anya ba zai hadasa masa wata matsala ta rashin yarda da ita ba kuwa? Abin ya tsaye masa a zuciya ainun, har CHEIK ya yi masa salama ya tafi yana fadin sai ya fito Fada in sha Allah _________________________________ Yadda Umma ta ga dare, haka ta ga rana Wayar da ta kwana bugawa tun jiya sai yau aka daga Bata tsaya wata wata ba ta ce" Kina tunanin yarinyar nan da wace ta rakota sunna iya hadasa min da matsala a kan abinda nake gannin mun kawo ga ci?" Gimbiya ta yi siririn tsaki, da wata masifar ta kwana, BAHIJA ta rikice wai sun yi waya da balarabenta ama yace zai kira shiru har safiya bai kira ba, sai kuka take yi gana ta kira ya ki dagawa, ita kam wannan masifa ta balarabe anya ba zuwa zata yi a nemo mata inda zata ganowa y'arta shi ba?, Wannan abu ya fara daga mata hankali sai ga wani shirmen kuma A dake ta ce" Ban fahimci yarenki ba" Umma ta sanar mata dukkan abinda ya faru, daga farko har marin nan na jiya Da takaici Gimbiya ta ce" Wannan wani irin sake ne? Ita wace ta rakatan me take yi har yanzu a cen? A kan me zaki bari har haka ya ringa faruwa ? Ina fata ba wani tunani gareki a kan yarinyar nan ba ko?, Dan kina iya janyowa kanki wani abin, kuma ki sani idan har muka yi sake mune a ciki, dan haka zan tado mutun ya kawo maganin nan, zan amsa daga wajen Aban Bahija a kawo a saka masa ya ci kowama ya huta!, Ita din bamza yar talakawa zamu yarda ta kawo mana cikas din ne? Bata isa ba, uwartama bata isa ba bale ita, ke kuma idan haukanki ya saka ki aikata aiki irin na sake ai shikenan!" Da wutar ciki itama ta ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 3