Sashe 72
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
duda rashin kyan hanya a haka yake sarafa motar yadda ya dace , ta yqdda du inda suka tardo jami'an tsaro za'a dage masu su wuce ne dan an san sun zo ana kuma sane da a yau zai dawo domin SARKIN YANKA ya fada Direct gidan.......... *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 5 Direct gidan SHEIK suka nufa , a nan SHEIK ya jagoranci wajen da zasu zauna, waje mai tsari da tsaro Ba su su bar gidan SHEIK ba sai da karfe hudu da rabi ta yi, ASADEEK na tsaye da rawaninsa yana gannin yadda aka basu masauki mai kyau, matar SHEIK wace ke turaka a daren tana tsaye a kan kaffafuwanta dudaa bata san ainahin da wa ake tafe ba tunda ta ga Mijinta ya fitar da ita a irin daren nan ta bada dukkan kulawar da ta dace ta hanyar saukar bakin da mahinmanci Sunna komawa fada masalaci suka yada zango , sai da duka yi sallar asubahi sannan suka yiwa junna salama kowane ya koma gidansa dan hutawa, domin tafiyar ta ja masu dogon zangon da basu zata ba, ba laifi kowa ya gaji danma jiki ya saba da wasu wahalhalun ai da ba za'a iya jurewa ba Cikin nutsuwa ya haye saman gadonsa yana mai Adu'ar neman tsari sannan ya shiga neman barci ido rufe, ama abin ya gagara Yinwa yake ji a cikinsa, ama ya san ba zai iya ci a yanzu ba, uwa uba damuwar da yake kaucewa tana ta so ta yi tasiri sosai a zuciyarsa har ta hanna masa yin barci Du irin yadda yake yin karfin halin kautar da tunanin UMMA ta san tsare tsaren bafansa shin tana tare da su dan kaunar lamarin ko fin karfinta aka yi ta amince ya kasa fita daga zuciyarsa Kwarai ya san baban burinsa ya tarbeta ya tambayeta, sai dai banzan tunani irin nasa ya hannashi hakan, ya fi ganewa bin sawayenta dan ya gani da idannuwansa domun baya tunanin a irin wasi wasin da zuciyarsa ke ciki in har zai iya yarda da kalaman bakinta, ba dan ya taba kamata da wani hali irin karya ba, sam, dan kawai zargi ya rigaya ya darsu a zuciyarsa dangane da ita lokaci daya, zargi mai girman gaske Haka ya ringa cenza wajen kwonciyar ko zai ji dadin yannayin kwonciyar, ama abu ya gagara tamkar yaron dake laluben mahaifiyarsa haka ya dawo yi a saman bed din , ya kula wannan ya kunce wannan har kuraye kirayen wayar tafi da gidanka dake garkame ta fara damunsa ainun Da mamakin gannin kiran masu gadinsa ya daga yana karama a kunnensa, dan ya san dai ya sheda masu barci zai yi in ba dalili mai karfi ba kar a tashe shi, sai ga kiransu ba kakautawa Jin bayaninsu ya saka shi bada umarnin a barsu su shigo, lokaci daya kuma ya zauna yana dan dafe gabak goshinsa, sai kuma ya mike ya shige bayi dan yin wanka, ko ba komai zai so ace da dan karfi a jikinsa ta yadda zai iya fuskantar matan dake cikin rayuwarsa a irin wannan lokacin Ya dan dauki lokaci a ciki sannan ya fito da alkyaba a jikinsa mai ruwan maroon da golding, kansa caje ba hirami a jiki, daga kasan alkyanar kuwa jalabiya ce fara sol da wandonta dogo , sai lulumshe luhu luhu din idannuwansa da suke da bukatar yin barci yake yi ama abin ya gagara Tunda ya sauko sau daya tak suka yi ido hudu, a hankali ta sinne kanta ta lalubo hannun Auta ta jimke dan har ga Allah sai ta ji tsoron kallon idannuwansa jama'a kamar idan yana ganiyar cin zalin dinta wannan lumshe lumshe kamar kwarto? Gaishe da shi suke yi, kusan a tare, gaisuwa irin wace kowace ke yi masa, kowace da kalar tata , shi kuma yana amsawa hadi da dan sakin dan murmushi har ya dawo kan UMMA dake ta huci itama ta gaishe shi a yannayin da idan tana cikin bacin rai sannan wajen ya dan dauki shiru Umma ce ta ja numfashi tana kallonsa ta ce" Yarona, abinda ake neman yi min a gidan nan yana neman kaini bango ta yadda ba zan dauka ba, sosai hakurina na son zuwa karshe a gidan nan gaskiya, haba dan Allah, da girmana da darajata? Ina kawar da kai ama sai an nunan iyakata?" Nanauyun idannuwansa ya dago ya sauke dubansa a kanta, gaba daya sai ya ji irin tashin hankalin da a da yake ji idan wani ya dan bata mata yau ko diz baya ji, hasalima sai yake sin aryata abinda ke saman fuskarta A nutse ya cire dubansa yana dorawa kan HUZNAH wace itama tata fuskar har wani irin kumkum take yi, ga dukkan alamu itama kalar a kumbure take A dan sanyaye ya ce" Huznah, zan sha tea" HUZNAH ta kalle shi, sai kuma ta kalli NADIRAH wace ta yi tsuru tsuru a dan yannayi na jin haushi ta ce" To uwar iyayin gaure gyare sai ki bani ky na kawowa mijina Tea, hajia mai kwana!" Gaban goshinsa ya dafe da dan mamaki ya kalli HUZNAH, sai kuma ya kalli Umma wace tamkar ruwa ya cinyeta gannin ga maganar da ta yi ama ASADEEK yake maganar yana son tea?, Hala cikinsa ana gaba da ita yai kuma? A nutse ya gyara zamansa ya dubi Umma , a hankali ya ce" Umma, me yale faruwa ne?, Wani abu aka yi ne?" Yar ajiyar zuciya ta sauke, duda yannayin da ya yi maganar kansa bako ne a gareta , ama da sauki tunda ya tambaya, dan haka ta fuskanceshi ta ce"Dangane da matanka ne da kuma Auta, jiya mun zo a tunaninmu kana nan ashe ka yi tafia baka dawo ba, ita wannan ta nuna mana ai ka yi tafia ne, ita kuma wannan ta dubi idona tace itafa ta fadi sako ko ban samu ba? Da na tambayi wani sako fa? Sai ce min ta yi ita gaskiya ta soke cin abincin taren nan idan kwananta ne, wai ta dubi tsabar idannuwana tace min ana iya hannata sirri da mijinta?, Ita kuma wannan din ita dake baba ta biye mata harda cewa ai kwanakin nata zasu kare itama bata son gannin kafar kowa a nata?, Me kennan? Nice na zama tsohuwar banza nake gannin irin haka? Karshe sai na tambayi ita kuma Auta ina take daga shekaran jiya zuwa jiya, budar bakinta tace wai tana bangaren BAHIJA, wai ko tana som zama a cen? Bahijar dake yarinya zata iya kula da ita ne? Ka fa san Auta bata da lafia dole sai ni ke iya mata, ama haka ina ji ina gani suka tafi taren, kennan na yi abinda zan yi ko? Barci ban samu ba dan tunani , ina dakon shigowarka !" Har Umma ta kai aya yana kallonta ne, kallo irin wanda yake son sake karantar harshenta da kuma abinda ke zuciyarta A hankali ya kalli HUZNAH wace itace baba da Auta da kuma NADIRAH, a nutse ya ce" Ke din da girmanki ne kika aikata haka maimakun ki tsawatar? UMMA ce fa?" HUZNAH ta sauke kanta, muryarta na dan rawa ta dago dubanta tana kallonsa ta ce" Allah ya huci zuciyarka shin yaya zan yi ne ni? Ka ga ina zamana sai ta ringa nemana da masifa, na fada mata ni bana so ama a banza, wai tace idan kwananta ne kar ta ga kafar yarinya ko ta tsohuwa a wajen, kennan ni da Umma ko???????" Ido NADIRAH ta zarro, hakama auta, NADIRAH ta gyada kai tana sake kallonsu HUZNAH ta ci gaba da fadin" Sai ta ringa nuna kamar ta fini sannin mijina bayan bata jima da shigiwa gidana ba, ni ban yiwa Umma rashin kunya ba, gani na yi tunda hakane nima a barni da mijina ranakun girkina ko?" NADIRAH ta tabe baki a ranta tana ayana' mijina mijina, da acema ana son mijin naki ne malama sai a yi fadan?' Bakinta dake musmusmus yake kallo har ta zabga harara ta tabe bakin sannan ya gyada kansa a ransa ya ayana' Hum abama yace tuzuruwar kauye' A bayane kuwa ya ce" To ke BAHIJA me yasa kike haka ne?" A dan zabure ta kalle shi jin sunnan da ya kireta da shi kuma yanzu, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya a kasan zuciyarta tana ayana' Kai Alhamdulilah ashe gwara da ban sanarwa innata cewar wani ya fada masa wacece ni, ta yiwu an kawo masa maganar ne ya karyata, uhum ka ji dai da shi!' A bayane kuma Sai da ta tabe baki, wanda ya kula idan ya kireta da Bahija take aikata hakan sannan ta dube shi ta ce " Yo ni me na yi kuma a nan, ni fa ban ce kafar yarinya da ta tsohuwa ba, cewa na yi kafar baba da ta y'a, ina nufin Auta ai itace y'ata ko?" Daga su har Autar kallonta suke yi bayan ta dire maganar ta kuma cuno baki tana gyara zamanta a dole ita ta gama magana kennan, wai Autar ce y'arta yau kuma mai gaba daya, watau ba zata daina cusawa HUZNAH haushi ba ko? Kennan Auta na kiran ASADEEK aba, ita Mama Habarsa da ya talabe ya saki yana girgiza kansa ya ce" Uhum, Allah shi kyauta, kin ga Bahija ki kula, bana so ana raina baban mutun, Umma dai da HUZNAH sun girmeki kin ji ko? Ki daina rainasu kin ji?" Irin yadda yake maganar tamkar yana rarasshinta ya saka daga UMMAN har HUZNAR zuba masa ido da mamaki, Auta kuwa dariyarta take ci a zuciyarta, dan dama tunda suka farka NADIRAH ke fadin kar dai ta yi barci ta san Umma tace yau zata kai kararsu ya dace a yi komai sunna nan kar a zaluncesu Auta yake kallo, yannayin shigarta ta yau, irin yadda idannuwanta basa neman rufewar nan kamar yar maye kulun, labewar nan da tsoron nan, uwa uba irin zaman da suka yi ita da Nadirah na kugu da kugu hannunsu rike ya saka shi dubanta da kyau, a hankali ya ce" AUTA?" Fuskarsa ta sauke fararen idannuwanta , a nutse ta