← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 87

Sashe 31

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi la'asar da magariba, idan zan dawo ina son tuwo tukin Fadimatu Zahra" Kai ta karra sadawa, NADIRAH kuwa ta saki murmushi domin mahaifinta sai yar dariya yake yi mata sannan ya daga mata hannu ya fice A hankali ta karasa saman gadon ta hau tana sake bin mahaifiyarta da kallo, wace le boye nata murmushin itama , a ranta ta ayana' Irin rayuwarku na so samu, wace koda baku da yanci a tsakaninku akoy yanci, rayuwa mai cike da barkwonci da soyaya, bama tare da ku na lokaci mai tsayi ama na san a kan daya, daya sai ya bada kansa a sare, ina matukar girmamaku, ina kaunar dadadan amincinku, na so na gabatar da haka da Aminu, domin alamunsa sun nuna shima zai kasance uba, amini, masoyi, yaya a gareni, sai kuma ga bukatarku wace na rantse da wanda raina ke hannunsa koda hakan na nufin rasa numfashina zan aikata, domin ba haramun bane, ama na tabata in da rai da rabo, koda Aminu ya auri wata ni ya fara sanni a soyaya idan na dawo zai dubeni' Sai da ya narke mamanta ta zuba mata siga sannan ta karaso ta zauna a gefenta ta mika mata tana fadim" Shanye, da innarki ta sakaltaki magani sai an narkar an zuba siga" Murmushi ta yi mai sanyi, muryarta a sanyaye ta ce" Innar Abana, toh ki baki a bakina mana, innata ita ke bani na shanye kuma ta kama min kaina" Murmushi innar birni ta yi ta kama mata ta bata da kan nata, tana shanyewa ta bata ruwa, nanma ta sha sannan ta kama mata kanta ta yi mata ADU'A, kuma ta gyara mata kwonciyarta ta zauna a gefenta tana kallonta A hankali Nadirah ta dago idannuwanta tana kallon innar Birni, Innarta tace a duniya babu mai sonta irin innar birni, wannan magana ta tsaya.mata a zuciya har ta kori tsohon tunanin dake ranta A hankali ta ce" Innah?" Fadime ta kalli fuskarta NADIRAH ta ja numfashi kasa kasa ta ce" Innah, idan na tafi, shikenan ba zan kuma ganninku ba?" FADIME ta sake zuba mata ido, ta kasa ce mata A NADIRAH ta ce" Ta yiwu a ranar da aka kaini ya gane ba wace aka bashi bace ya saka a gilen kaina ko?" Kirjinta sai da ya doka, tana kallonta ta ce " Ki fadi alkhairi mana ko ki yi shiru INDI, sannan an ce bai san BAHIJA ba, ina gannin zuwanki ba damuwa bane tunda bai san wace tale y'ar sarkin ba" NADIRAH ta gyada kanta, kasa kasa ta ce" Innata, sai nake jin abin wani iri, yaya zan rayu a cikin mutanen da duke baki a wajena?, Yaya zan iya kaucewa kaidin masu kaidin cikinsu?, Yaya zan iya kare mutumen da ban wanene shi ba?" "Dama wanda ya isa ya kare ki daga dukkan abubuwan nan wanda ya baki aron numfashi ne NADIRAHNA, NADIRAH kowace mace bakuwa ake kaita bakon wajen da zata yi zaman aure, dama kuma rayuwa ta gaji ka zauna ka birge wani, wani ya tsaneka ba tare da ka aikata masa komai ba, halinka shine zai kwaceka NADIRAH................. sai maganar shi , shi Uban gidanki" FADIME ta fada tana shafa gefen fuskar NADIRAH a hankali NADIRAH ta dago lumsasun dara daran idannuwanta da mamaki ta ce" Uban gidana?" Mahaifiyarta ta gyada kai yana kallonta NADIRAH ta ce" Innata, kina nufin ni baiwarsa?" Mahaifiyarta ta zuba mata ido tana kallonta, NADIRAH ta mayar da kanta a hankali saman cinyar mahaifiyarta ta lumshe idannuwanta, muryarta cen ciki ta ce" Ni ba baiwa bace, sannan ni ba yar kaso bace.....Innatah, ba zan rayu a gaban kowa kamar yar kurkuku ba , ciki harfa UMUGHLUK ITIFAL!" A tsorace mahaifiya *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 2 A tsorace mahaifiyarta ta dago fuskarta tana kallonta ta ce" Me kike nufi?" NADIRAH ta tsare fuskar mahaifiyarta da kallo, tsoro, tarin shaka na bayana a saman fuskar mamanta, dan haka sai ta yi murmushi a hankali ta sake komawa tamkar mage ta lafe a jikin mamanta ta yi lamo bata ce komai ba, hakan ya sa mamanta mayar da hankali, ta ci gana da tsoratar da ita wanene UMUGHLUK ITIFAL, da jama'ar dake tare da shi, da tunatar da ita wacece ita, lalle baiwar take tunda yar bayi take Ita kuma a ranta murmushi kawai take yi, tana ayana abubuwa a ranta kamar haka' Ba zan je ko'ina na rayu kamar baiwa ba Innah, ban ce a aurani a kaini ba, ba kuma zan je a matsayin yar sarki ba, zan je a matsayina na ni NADIRAH, bayanshi bani da matsala da kowani sarki ko hadiminsa!, Ki kwontar da hankalinki, bauta ce ba zan yi ba innata' ................. Wannan shine mafarin shiryawar NADIRAH da iyayenta baki daya, sannan mabudi wata sabuwar rayuwa mai cike da sarkakiya da salo kala kala A wunin rana ana kula da jikinta ne da gyaran ciki kamar za'a cenzata baki daya Daga bakin lokacin da zata kasance da iyayenta su kuma nasu salon sunna kokarin karra taurara dukkan wani tsoron da zai sakata aikata aikin da za'a zo mata da shi dan a cutar da mutumen da suke kira Uban kowa ne....., Takan yi murmushi tace banda ita, ita kam ba ubanta bane gaskiya! Da zarar innar Abanta ta matsa kuwa wani rikitacen yare innarta ke yi mata mai tafe da rikitaciyar tafia mai wuyar fasara a kwakwaluwarta ita NADIRAHn innar kauye A gaban Innar birni sukan nuna mata Uban kowan nan uba ne ko kallonsa bai dace ta yi a cikin ido ba, innar birni na matsawa fakat Innar kauye ke fadin mace take, Allah ya gama bata komai tunda ya haliceta mace, a matsayinta na mace tana iya mayar da UBAN nan na Kowa dan jaririnta, ba aure ba, Allah ya sa mace dubu ya sani a duniya sannin ragage ne tunda mu'amalarsu ba ta sha ar iskar junna bace, ta sunna ce!, Wai innar kauye ta dubeta duba irin na basira tace da ita zata fuskanci kamar bashi da lafiya, wannan rashin lafiyar tasa idan har ya yarda ya shiga harkarta zata yi wasa da ita, da rawa irin ta disko danser kugu a daure kafa a sama?, Ira innar Kauye ke cewa ta karkada kugu kamar zai tsinke fiye da dandali idan UBAN KOWAN cen ya shiga harkarta, to ira maganar gaba daya a duhu take zo mata kuma a dunkule, sai dai ta cira kaita kada kai ta fadawa kanta cewa ba zata dauki hudubar innarta ba, domin a hilacewar Innarta kamar tana son nuna mata zata je zaman aure, kamar yadda takan koya mata a da, bayan zam ne na ceto da rabuwa in sha Allah Tana cikin hayacinta da bin takun kowa a gidan nan, har yau da ya rage kwana uku a daura aurenta, sunna zaune tana jin yadda mararta ke mata wani irin nauyi aka zo da mota baka sidik da direba daya tak sai GIMBIYA, wace tana fitowa ta ga ikon Allah irin yadda mahaifiyarta da Innarta suka yi dan yi mata barka da sauka Kanta a sama, ko tace hancinta a sama ta yiwa NADIRAH kallo a hanzarce, sannan da ido ta yiwa Fadime alamun da ya saka Fadime saurin kama NADIRAH suka shige ciki watau uwar dakar FADIME Cike da isa ta idasa shigowa, fuska babu fara'a a tsaye tana kallon FADIME ta ce" Ina fatan, kin jadada mata wacece ita, haka kuma kin shaida mata me zai kaita BABAR FADA?" Fadime ta karra sada kanta ta ce" Na sanar Mata Allah ya taimakeki" Gimbiya ta karra duban NADIRAH sama da kasa tana mamakin kira, kyawun halitar yarinyar, sai ta ji a zuciyarta tana son yin kiran UMMA ta fada mata lalle lalle itama wannan a bata abinda aka ba matarsa ta farko ta sha, kar aje kilu ta janyo masu bam! Yarinyar ba abin wasa bace, bale a yanzu da take tsaye darrr Mahaifiyarta na duke? Ta saka mata wani shaka da tunani mai yawan gaske a ranta Kanta ta sake cirewa ta kuma duban FADIME ta ce " A nan zaku zauna har bayan auren, a yanzu na zo da BAHIJA, zata tare a nan, Fadime zaki kular min da yarinyata, dukkan abinda take so kamar yadda kika saba, ki sani da waya a gefena, kuma kasamcewarki a nan ba yana nufin kin tashi daga matsayin da kike bane kin fahimta?" NADIRAH ta sake saka idannuwanta tarr cikin na Gimbiya da ta sake juyowa ta kalleta, Gimbiyar ce ta cire idannuwanta tana kada kai ta dora da fadin" Kar na ji ko na ga labarin an barta ta fita, kuma kar ta yi bako ko bakuwa, domin jarida tuni ta fara yawo cewar za'a daura aurenta da ASADEEK!" a zabure FADIME ta dago ta kalli Gimbiya, sannan ta mayar da kanta kasa, subahanalah, Gimbiya ce ke kama sunnansa a waje gatsau hankali kwonce? Lalle ta shirya NADIRAH kuwa baki ta samu kanta da tabewa, a saman lebenta ta maimaita sunnan sannan ta watsra ta sake fuskantar matar nan da ta jima tana fata Allah ya nuna mata ta dauketa da mari a rayuwa "Sarki ya yanke cewa , ana gobe daurin aure zai zo ya dauketa da kansa ya wuce ta falonsa da ita dan gudun yan magana, ki karra jadadawa yarki biyaya itace makulin samun lafiyarku baki daya!" Ta sake fada a kausashe tana watsawa Nadirah wata mahaulaciyar harara, sai dai kikim din nan irin na yara masu taurin kai haka Nadirah ke tsaye bata sanyaya ba, a dole Gimbiya ta gama dukkan sharudan ta ta juya ta fita tana leleka dakunnan dan gannin wanda y'arta zata iya rayuwa a ciki! "Innah ki tashi mana ta fita " NADIRAH ta fada muryarta a raunane tana kallon mahaifiyarta Innarta ta dago tana murmushi ta ce" To indin Hindu bara na je na ga me zan mata?" Da sauro NADIRAH ta ce" Aa ki zauna bara na je na yi koma menene kin ji Innar Abana?" Kai ta girgiza tana ficewa, dan ta kula y'ar nan kamar bata jin nasihar a duka a gaban manyan nan
Chapter 31 · 0% Book details