Sashe 8
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gida ko?, Kar ka daukaka abin nan , ka yi hakuri ka ji?" Rawanin da ya sasabto kada ya ja a hankali ya mayar ya rufe har wajen hancinsa da shi sannan ya duba agogon hannunsa domin ba zai shiga gida yanzu ba sai ya gama karatunsa an gama salolin da suka rage , to mema zai shiga ya yi ne? Ya tabata Auta tana nan bata yi barci ba , rigimarta na nan tare da ita, matarsa kuwa bai san me zai je ya nema a wajenta ba tunda bashida abinda zai bata, yana so sai ya je ya dawo daga tafiyar nan zai zauna da ita, zasu yi zaman da ya dace, zai yi kokarin kwatanta mata abinda ya dace ta fahimta, sannan zai yasare mata wahalar da yake gannin tana tare da ita, domin shi dai wada yake ciki shi kadai ya san ukubar da yake ciki, baya rabo da ciwon mara, tamkar zai kashe shi wani lokacin.....ama ba komai Allah ne gatansa Dare ya cika sosai a ranar nan, domin sai kudan karfe dayan dare suka doso babar farfajiyar ta masarauta shi da makarabansa, mutun takwas sunna tafe cikin nutsuwa, haka kuma sun sakashi a tsakiyarsu Dakatawa ya yi yana duban dogaransa mutun hudu,da dima diman bodyguard dinsa mutun hudu, watau masu rike da bindiga Dan murmushi ya yi wanda bai yi tunanin a yau zai iya samunsa ba sakamakon irin bacin ran da ya hadu da shi, sai dai zama a cikin datijai da zikirin da suka yi ya sanyyayar masa da zuciyarsa harma yana jin a yanzu ko wani hukunci ya yanke bafa da bacin rai ya yanke shi ba, ba zai yi nadama ba "Duba ku ga Namiji har namiji, sai dai ba husssss.................." Ya fada daga saman dakin da ya sauka, watau bangaren bakin ahalin gidan, baban dakin da yake nasa a matsayinsa na bafan Sarki Abinda ta saka ta kare fuskarta ta sake ja ta rufe fuskar tata sosai itama ta karaso wajen labulen ta tsaya tana kare masa kallo, alkyabarsa sam bata boye cikar halitarsa ba, bama zakak gigice ba dai ka ganshi ba alkyabar, domin du wani bayanannan abu da Gymnastics ta haifar masa a jikinsa kan bayana ne, bai yi irin wannan bulewar ba har ta baci, ama wace ya yinma a nan kusa dai babu ginanen namiji irinsa sai dai a nesa Ajiyar zuciya ta sauke ta fita daga wajen labulen ta koma saman kujera ta yaye lulubinta gaba daya tana kallonsa ta ce" Munaa cikin gagarumar matsala, shirunsa da rashin hargaginsa ba yana nufin bashida kulaliya a zuciyarsa ba! Ni na raine shi, ko mahaifiyarsa ba zata fada min wanene shi ba!" Labulen Bafansa ya saki cike da jin kishin yaron da tarin kasar da Allah ya tara masa a cikin zuciyarsa ya koma ya tsaya kikam a saman kanta A amon muryarsa zaka gane ransa a bace yake ya ce" Yanzu ace, daga jin wannan magana ta bila na kasa zaune bale tsaye sai da na kawo kaina? Ni da nake bafansa kennan? Da wani ne fa?" Baki ta tabe tana duban agogo ta ce" Ba zaka gane ba, kasancewarka bafansa a idannuwan talakawansa kadai ka tsira, summa dan basu san wanene kai a rayuwarsa bane, ka ga ASADEEK? Yanada mugun daukaka a idannuwan Agadasawa!, Da ace maganar nan gari ta zaga da yan cikin garinka zasu fara kai maka farmaki !, Yanzu du ba wannan ba, da me zaka tunkareshi a goben?" Zaunawa ya yi yana fuskantarta ya ce" Da me zan tunkareshi kuwa? Tunda na taso na zo da kaina zan bashi hakuri ne kawai na koma komai ya wuce, abinda gimbiya ta aikata kuwa na mata kashedi ta min alkawarin ba za'a kuma ba" Ido ta zarro tana kallonsa cike da mamaki Da dumbin mamaki ta ce" Anya zaka iya mulkar garin Agadaz nan gaba?" Da bacin rai ya ce" Ki gyara furucinki a kaina , kar ki manta wacece ke?" Bakinta ta tabe tana cire kanta, muryarta da haushi haushi ta ce"Kaima kar ka manta me yake tsakanina da kai? Kafin ka ffara tunanin watsar da ni ka tuna da me da me zaka yi wasa!, Maimakun ka tambayeni dalilin furucina sai ka hau kan isa da iza bayan magana muke a kan SARKINKA?" wannan karron kasa ce mata komai ya yi,dan babu abinda ya fi kona masa rai irin ya ji an kirayi yaron bayansa a matsayin sarkin da ya fi shi fada a ji! Ajiyar zuciya ta sauke ta saisaita muryarta ta ce" Ka yi hakuri, ina so ka fahimci girmann laifinka, sannan mu samu mafita, ka sani idan bamu yi da gaske ba neman gira ne zai saka mu rasa ido, kar ka manta namiji kake, yaya zaka ji idan talakanka ya zagi mazakuntarka? Uwa uba a gaban wani dake kasa da kai? Zarafinsa aka ci, mutuncinsa aka ci, dole a samu hanyar da za'a wanke kai, kuma a wanke shi a idannuwan wanda aka zageshi a gabansa!, Dole zaka duka a gabansa ka nemi kanka, dukawa wada baya hannawa a mike da tsayi, ka fuskanci furucina ka samawa kanka sauki, idan har ba haka ba zaka sakawa kanka damuwa ne!" Ikon Allah shi yake kallo, ransa a matukar bace ya mike daga zaunen da yake ya nuna mata hanyar fita a kausashe ya ce" Kin ga, tashi ki tafi" Da mamaki take kallonsa A tsawace ya ce" Na ce ki bace min da gani, tunda a yau ni zaki zagarwa mutunci ki dubeni ki ce na je na dukawa yaron da na haife shi da cikina? Tashi ki tafi!" Murmushi ta yi mai ciwo da ma'ana da dama a zuciyarta, tabas idan ta daki kirji ta ce ta fi kowa sannin wanene UMUGHLUK ITIFAL bai dace a yi mata gardama ba A nutse ta mike, cike da ita ta gyara hijabinta da yannayin shiga irin ta bayi dan yin bada sau ta sake rufewa da kyau kasa kasa ta ce" WANDA BAI JI BARI BA, ZAI GA UWAR BARI!" A labe ta fice a boye ta samu ta koma bangarenta ta ringa kai kawo dan bacin rai, tamkarma abin ya fi damunta fiye da sarkin, sam baya gannin abinda take gani, ama ba komai idan da rabon su sake zama sa zauna! Washe gari *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 0 *Washe gari* Da misalin karfe tara da dori kadan A hankali ya sake debo abincin a cikin spoon ya sake nufo bakinta da shi yana murmushi , cikin tausashiyar muryarsa kasa kasa sosai ya ce" To naji, zaki bi ni ko? Ha sai kin koshi tukunnan kin ji?" Idannuwanta ta lumshe, idan yayanta na irin abubuwan nan takan ji hankalinta na sake tashi, idan ta tuna dukkan abinda yake yi a kallon mahaukaciya yake yi mata irin a lalabakan nan, sai ta ji duniyar baki daya ta fice mata a ranta Yawun bakinta ta hadiye ta sake bude bakin nata ta amshi abincin a hankali ta ringa taunawa still tana kallonsa Murmushi ya yi yana sauke ajiyar zuciya ya dauki tissu ya goge mata bakinta sannan ya dauki ruwa mai dan sanyi sanyi kadan ya nufi bakinta da shi A hankali ta amshi ruwan, ta fara sha kennan aka shigo da salama Kwarewa ta yi da ruwan dake bakinta da sauri ta shiga tari, sai dai abin mamakin, ba ta tarin da take take ba, watau tana tarin yayanta yana riketa da yi mata sannu da kokarin kafa mata ruwan a bakinta dan ya sasauta ama ita ta rike hannunsa kakam tamkar zata shige cikinsa , lokaci daya kuma jikinta ya dan dauki rawa rawa tana dake kankameshi Da sauri Umma ta karaso tana fadin" Subahanalah, my baby ruwa ne ya kwarar da ke, yarona ka bata mai sanyi da yawa ne? Ka dan bana bata mai sanyi dan yana dakata tari, yannayin jikinta sai ana kula Yarona, fan sako min ita na gani? Zo nan na gani autana?" Da karfi ta dake dantse hannunsa tana rintse idannuwanta hawayen cikinsu suka samu zirarowa daga gurbin idannuwan nata ta kifa kanta a gaban shadar dake jikinsa ta ja numfashin dake nuni daf tale da fashewa da kuka A hankali ya sake zuba mata ido yana nazartarta, sai kuma ya dago ya kalli UMMA dake kusansu sosai Hannun UMMA dake dan taba Auta, Auta na warcewa ya bi da kallo, a hankali ya sake kallon UMMAN wace ke aikin da ta saba, watau nuna mata kauna da tsantsar soyaya Idannuwansa ya cire a kanta yana sake duban Dogari da ya sanar da son shigowar Bafansu, haka kuma ya sake duban Umma Dan murmushi ya yi a hankali ya ce" Yauma fada kika yi da mamanki ko?" Da sauro UMMA ta dago tana kallon fuskarsa, furucinsa ya tsoratar da ita, hakan na nufin ya fara gannin wani abin dake tsakaninsu ne? Watau turetan da Auta ke yi? Dan murmushin yake ta saki ta dan ja da son taba Autar ta zauna tana fadin" Ai ka san halin Auta, ita fa damuwarta a kan shan magani ne, jiya har ta kwonta na tayar da ita , shine aka yi ta kuka da kyar na lalabata ta yi barci" Murmushi ya sake yi bai ce komai ba, domin Bafansa ya shigo tuni yana tsaye yana kallon Auta da irin abinda ke faruwa Dan tsaki bafansa ya yi yana dafe kai ya kai zaune ya ce" ASADEEK , na rasa me yasa ka ki a kai yarinyar nan asibitin masu irin ciwonta, gata abu sai karra yin gaba yale, wannan rukunkuma haka kamar wata yar yarinya bayan mace take magidanciya? Ai gwara ka yi hakuri a kaita a ringa bata magani ko abin ya yi sauki ko?" Jimke hannunsa da Auta ta yi ya saka shi sake dubanta a hankali, domin hakan da ta yi ya sheda masa dayan biyu ne, Au ta ji abinda bafanta ya fada har ya mata ciwo, ko kuma bata son jin muryarsa ne. A hankali ya sake riketa yana sake gyara mata hijabinta dan kar ya shaketa, murya a tausashen da ita kadai