← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 87

Sashe 1

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data Normal *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 0 Busar kalalo ce ta zagaye baki daya karamin garin mai sunna DOGON DUTSI Wannan busa itace ta fitar da kwai da kwarkwatar wanda ya kwana ya kuma wuni a wannan gari Busar ce ta kada hanjin du wani wanda bai tsamaci zuwan wanda ake yiwa busar nan Babu wanda ya san da zuwan ZAKIN SARAKAI garin na dogon dutsi Kusan hankali Tashe sarkin garin ke kallon wanda ya kawo masa labarin tawagar ZAKIN SARAKAI ke ratso garin nasu Mikewa ya yi tsaye a babar fadarshi ya kalli gabas, da yama, kudu, da arewa , cen ya hangi wasu tarin ciyayin ledoji farare wa'inda a da bai gansu ba sai yanzu Hankali a dan tashe ya ce" Zabga, minana naka gani a ceniya? Ka maza ku dauke duk wani tsinke ko idan Mai garin garinmu ya bar garin nan na gile maku kawunnanku !" Du a rikice aka shiga sake kimtsa fadar, duda batada wanu dati, ama a haka aka ci gaba da gyara duk wani abinda ya dace ace an gyara Nan da nan Fadar ta dauki cika, sarki ya je a gurguje ya cenzo sutura da rawani, ya dawo zuciyarsa cike da zulumin abinda ya kawo ZAKIN SARAKAI garinsa A gigice dawakai suka fara shigowa, lokaci daya kuma aka harba bingida irin ta tokar nan ta yi karra mai karfi gabas da yama, kudu da arewa, sama dau dau dau hakan ya sa wandama bai mike tsaye ba mikewa, dogaran garin suka layu layi layi, masu dawakan nan suka ringa kai hari a dandar kasa sunna danna wani irin algaita sunna hobara har sai da suka tada kura sannan suka koma gefe Wani tafkeken mutun, sanye da shiga irin ta dogarai ama ya yi dinki irin na fitsara, na kirayi dinkinsa da fitsara ne domin rigarsa ta dogarai bakinta saman hannunsa, damatsunnansa a fili suke jibga jibga da su sunna huci.......*HURRRRRR*................. Sai da ya wara kafafuwansa ya dauki algaitar dake hannunsa ya kafa a bakinsa ya yi busar da ta karra hargitsa hanjin sarkinsu , ya daga hannunsa ya dajawa kirjinsa duka ya bude katuwar muryarsa ya ce" GYARA KINTSI!, NA CE GYARA KIMTSI! GA ZAKIN SARAKAI TAFE!" Du wani jinnin sarauta nan take ya gurfana, irin gurfanawar nan ta ajiye gwuiwa a kasa da sada kai, ba gurfanawa irin ta kai hannaye da goshi kasa ba , ko daya, irin ta ba baba girman nan ce Motoci ne suka biyo bayan dawakan har su hudu, suka layi a tsakanin mutanen, sai kuma wasu dawakan a bayansu ya zamto sun sakasu a tsakiya ne Shiru wajen ya dauka, fadar du girmanta irin baban fili na masarautar garin sai da ya nemi yin kadan, a hakanma ana ta hanna na waje shigowa domin cincirodon mutane ne ke ta bibilowa ta ko'ina Dama JIRWAI ya ba Sarkin garin dogon Dutsi kan yana iya karasawa wajen babar motar da aka bude Da dan hanzari ya karaso, sai da ya rage tsayinsa sosai ya jimke hannunsa ya bude bakinsa ya ce" Hawa lafiya , sauka lafiya jinnin sarakai, barka da gannin yau cikin koshin lafiya barka da shigowa garin DOGON DUTSI *OUMOUGHLOUK ITIBEL*, Allah ya sa alkhairinka da ya yabanya a duniya ya tardo ni a yau Adalin sarakai" A kalla ya dauki minti biyar da kawo gaisuwarsa sannan wata kafa, mai dauke da dinki irin na sarakai, yadi ne mai haske Sararin samaniya hakan ya sa sai walwal yake, ya dauki dinki na bakin zare da yelow mai dan kyali, kafarsa cikin takalmi kafa ciki irin na sarauta mai lulube da Ado irin na sarakai, ba'a gannin kafarsa ko daya ba'a gannin kalar fatarsa sai hannunsa da ya fitar mai dauke da kira baba, watau yanada girma hannun da kuma jijiyoyi a tsaitsaye a jikinsa, haka kuma hasken farin hannun ba mai ja bane, aa mai haske ne fassss, ya kai shi saman goshinsa ya hangi ranar garin, rana mai zafi mai kwalar kai , rana mai nadar fata sannan ya idasa mikewa ya fito a matsayinsa gaba daya ba tare da ya bar wani saura na jikinsa a cikin motar ba "Adalin kennan, sarkin Kasata, mai tafe da ikon Allah, mai takama da Ayar Allah, namu gwani bai fito dan ya birge wani ba, namu gwani Allah ne ya nadashi ba mutun ba, NA CE GA OUMOUGHLOUK ITIBEL a gabanku!" Wancen mai darjejiyar muryar ya sake fada yana sake hade hadadiyar fuskarsa ta yadda ya karra rikita zukatan masu saurin sarewa da abin tsoratarwa Sarkin dake gurfane ya dan zubawa idannuwansa da su kadai ake iya ganni a bayane, Alkyabarsa ta rufe komai, ga rumfar da karti hudu ke rikewa sunna tafe idan yana tafia, Cike da iza ya waiga Hagu, da damarsa yana kallon Malaman da suka yi tafiyar da su, uwa uba Sarkin dakin duhu dake sanye da bakaken kaya shi din da kansa bakin jikinsa ba abin dadin kallo bane, uwa uba Sharbebiyar wukar dake hannunsa mai walwalwal din alamun kaifi da kaifafa A nutse, cikin tafiar da Allah ya haliceshi da ita, ba tafia ta wulakanci bace dan shi wane ne, tafia ce da Allah ya nada masa ya bashi a jinninsa, RAWANI ne a kansa ba na siya ko na kwace ba!, RAWANI ne a kansa nadin gado da jama'ar garinsa, RAWANI a kansa wanda ya gagari zamani da gwamnatin zamaninsa, shi din da ake kiransa OUMOUGHLOUK ITIBEL ba shi ya nadawa kansa wannan sunna dake nufin Zakin sarakai ba, SU SARAKAN sunne suka bashi wannan sunna, ba dan su birge shi ba, ba dan fin karfi ba, Magana ce ta cencenta..... Eh lalle shi din *ANNEMOKAL ne mai Adalci da Hatsari!* A daidai wajen da aka tanadar masa da kujera ya ja ya tsaya ya karewa kujerar kallo An kawatata da irin ado nasu dan birge shi duda ya zo a lokacin da basu zaci ganninsa ba, ga kuma rantsatsiyar rana a saman kansu Kansa ya dauke a kan Kujerar, wanda hakan ya saka Dogaransa, Malamansa, Sarkin garin nan, dogaran sarkin garin da du wani wanda ya fahimci Nufinsa ba zai zauna ba kallon kallo da kuma sake gyara yannayi, domin idan bai zauna ba, babu wanda zai zauna, haka kuma babu wanda zai mike daga tsugunon nan Tsoho, mafi kusanci da sarkin garin DOGON DUTSI aka yiwa iso, ya karaso ya duka a gaban sarakan biyu dake tsaye, daya na dan nesa da daya kadan, ana faman fifita masu fifitun da ba ratsa alkyabar jikinsu yake ba bale rawanin fuskarsu Takardar dake hannun Dogari ya warware ya bude Rubutu ne a tausashe , mai isar da sako a hargitse Tanbayoyi ne masu rikita cikin mai laifi kamar haka" Asalamu alaikum wa rahamatullah., Menene dalilin da ya sa mai laifi bai amshi hukuncin kisa kamar yadda ya dace ace ya samu ba?, Ko sakon takardar a yanke masa hukuncin kisa bai isowa masarautar Dogon Dutsi ba?" A rikice Sarkin ya kai dubansa kan Zakin SARAKAI, sannan ya sake mayarwa kan Datijo zuciyarsa na dokawa Datijon kansa zufa ce ta shiga karyo masa a fuskarsa Yaya zai yi? Me zai ce? Maganar da ta saka shi sake sada kansa da budar bakinsa a rikice ya ce" RAINA fansa ne ga doguwa idan har ni Datijo Rabe na zama daya daga cikin WA'INDA suka take dokar Zakin SARAKAI!" Ido Sarkin garin ya sake zuba masa, mamaki da tsoron kar dai Datijo ya fitar da kansa ya saka shi bude baki ya ce" Da doguwa kake Rantsewa Datijo? Doguwa fa? Kar ka sako doguwa a kan laifin da muka aikata baki daya!" Ido Zakin sarakai ya rintse, takaici, mamakin mutanen na kama shi, Doguwa, ace har daga bakin sarki sunnanta da nuna ita din wata ce na yawo a fili a gaban jama'arsa? DOGUWA din nan Aljana ce da suke rantsuwa da sunnanta!, Doguwa din nan aba ce wace suka yarda da ita, Doguwa din nan itace babar damuwarsu da shiga a duhunsu, sai dai basu sani bane, bai zo garinsu ba sai da ya shirya, yau sai ya kona gawon doguwa da hannunsa, idan ya so ya kama da wuta dan Girman Allah! Doguwar Banza doguwar wofi? A kausashe, maganarsa ta farko, tunda aka fara kwaramniyar nan, ya bude bakinsa kai tsaye ya yiwa sarkin magana, sarkin kadai, domin mutanen dake nesa babu wanda ya ji furucinsa, na kusan kuwa a lokacin da ya fara sun dode kunnayensu dan ba maganarsu bace A kausashe ya ce" Kana Musulmi? Dan musulmai, jikan musulmai, ja gaban talakawa kake danne hakin wanda aka cuta, wanda ya tarda matar kanninta ya afka mata, ga laifin Fyade, ga na zina, ga na kisa dan ta kiya ya shaketa har ta mace..........? Lalle idan baka yi wasa ba zan zuba maka petrol a jikin bishiyar doguwarka na kone ku tare AMIRU!" Shiry Sarki ya yi yana yawo da idannuwansa zuciyarsa na bugawa, subahanalah, bai san yaya zai yi ba, dama wannan maganar ce ta taso da Zakin sarakai? Ya Allah yau ina zai saka kansa? Sai da magana ta tardo shi cewa a zartar da hukunci daidai da yadda adini ya zo da shi, aka ringa cewa a kasar nan ai ba'a kashewa dan an kashe, ga koken matarsa a gefe domin danta ne na wani gidan kafin ya aureta, sai ya yanke masa zama gidan yari, nufinsu idan tafiya ta yi tafiya aka manta sai su fitar da shi ya gudu, sai gashi wannan abin ya faru? A nutse ya maida hankalinsa wajen Ustaz AL'AMEEN A yanzu sai ya dan bude muryarsa ta yadda du na kusa kusa zai iya ji ya ce" BISMILLAH Ustaz, menene hukuncin wanda ya kashe bawa ba tare da wani laifi ba? A hukuncin an zo da maganar Zamani ne? Ina nufin zamani irin naku wanda hukunce hukuncen adini suka zamto abin gaba a wajenmu?.....Bismillah" Ustaz AL'AMEEN, baban alkali ne ne na kotun musulunci na kasar ZAKIN SARAKAI A nutse Ustaz AL'AMEEN ya matso ya shiga bayani kamar haka" _"A shari'a kisa ba tare da ha i ba babban laifi ne,
Chapter 1 · 0% Book details