Sashe 37
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gwara ta mutu yayanta da kowa na yi mata kallon mahaukaciya, in sha Allah ba zata daina addu'a da kokarin isarwa da yayanta sakon da take so ya gane dan kankin kansa, in sha Allah ta san wata rana za'a dace, domin sau biyu tana gannin yana yin tsai da tambayarta kamar bata son Fada?......, Tana so ya fahimci ba fa a bace bata so, abinda ke cikin fadar ne da kansa Da kyar ta iya shiryawa, dan ta san ba jira yake yi ba koda itace kuwa Alkyabarta ta dora a saman suturarta, domin su saka Alkyaba ya zame masu tamkar saka hijab ne, idan babu ita a jikinsune suke jinsu tamkar tsirara Bugawar da akai mata ya sakata mikewa jiki ba karfi ta sake kallon dakin nata ta sauke ajiyar zuciya ta bude ta nufi motar ta shiga itama ta zauna ta hade kanta da abin motar tana kallon kofar da du ake jiran Yayanta ya fito Cike da kamala, tafia t kasaita, jikinsa dauke sutura shiga ta albarka, mai dauke hankali mai matukar daraja, Alkyabarsa mai ratsin golding ce hakama takalminsa irin na saraki mai ratsin golding din ne, kansa dauke da rawaninsa, hannunsa na dama rike da Sandar girma Yanaa fitowa wani bafade daga duke yana gyara rigarsa da kyau, wasu biyu kuwa na rike da lema , daga gefe wani na yi masa barka da fitowa a duken shima hannayensa a jimke yana ta faman yi masa kirari Wajen mai garin garin ya ja ya tsaya wanda ya zube shima cike da farin ciki yana sake gaisar da shi, Mikewar ya yi, domin damar hakan ya bashi da hannunsa Yana mikewa kasa kasa ASADEEK ya ce " Jiya waye ya min allura?" Mai gari ya karra sada kansa cike da girmamawa ya ce" Baban yarona ne Allah ya karra maka lafiya,likita ne ai a cen baban gari ya yi karatun" Kai ya gyada a hankali ya lumshe idannuwansa, ba laifi Allurar ta taimaka masa sosai domin kafin ta fara aiki a jiya ji ya yi kamar zai ci babu, a kasa yake a yashe hannayensa damke da mararsa baya cikin hayacinsa, a dole mafadensa ya kai maganar wajen mai gari, shine suka zo da yaronsa baban likita ne, shinema ke kula da asibitin kauyen ya duba sarkin, nan ya fice da sauri a motarsa ya fita ya shiga gari a daren nan da balakin gudu ya je ya samo allurar ya dawo ya yi masa a lokacin fadawansa sun gama rikicewa harda mai kuka, sun kama da kyar sun mayar da shi saman gado Bayan allurar ne ya samu barci , wahalalen barci mai cike da mafarkai, A hankali Mai gari ya karra sada kansa, muryarsa a mutunce, a tausashe ya ce" Yama ce da zai samu ganawa da kai, akoy mahinmiyar maganar da ya dace ya sanar maka, sai nace sai na tambayi izini" ASADEEK ya karra cira kansa yana bin mutanen da suke ta jifansa da kallo da dago hannu, wasu muryoyin na faman ambaton UMUGHLUK ITIBEL, sannan ya sake duban mai garinsu A hankali ya furta" Ka sanar da shi, abinda yake son fada na sani ba yau ba, idan shi yanada wani maganin da zai karra kashe min cutar ina maraba da haka, idan babu, ka sanar masa cewa Haka Allah ya hukunta" Mai gari ya dago ya dan zubawa fuskar ASADEEK ido,.duda rawaninsa ya tare komai, ama idannuwansa da girarakinsa na fili, ko a yanzu idannuwansa jansu ya wuce misali, haka kuma girarsa a hade take alamu ne na ransa a bace yake Kai ya sada, shi kam da zai bashi dama da ya gwada nema masa magani, irin na hausa na gida, to matsalar tsoro yake kar aje ba zai yarda da magungunnan nan ba, kar yace ba kyau, ama wannan matsalar ai ga dukkan alamu samu ne, shiga gaba ne, tunda karara a jiya ya fahimci matsalarsa, kuma a halin jigatuwa muryarsa na fitar da magana a ciciren da ya dan fahimci wani abin, sai dai ba zai yi gigin kawo masa maganar ba, sai ya karra sada kansa a tausashe ya ce" Allah ya baka lafiya ANNEMOKAL ITIBEL" Kai ya gyada a hankali ya juya dan nufar motar da zai shiga, Daga dab nesa kadan da motar ya tsaya yana hangen Huznah da Auta Huznah kallonsa take yi, irin kallon da ta saba koda yaushe, idannuwanta dauke da bege da girmamawa,du irin turetan da ya yi a hankali ya hango murmushinta sannan ya hango jimke hannunta, irin tana mai aiko masa da gaisuwa, yana sane da zuwanta da safe bata samu ganninsa ba Kai ya dan gyada a hankali sannan ya dan sada dubansa alamun ya mayar mata da gaisuwar itama, sannan ya sake kure fuskar Auta da ido Yannayinta ya saka shi jin jikinsa ya karra mutuwa, a nutse ya cire dubansa ya karasa wajen da aka bude masa mota ake jira Yana karasowa aka shiga gyara masa rigarsa har ya shige ya gyara zamansa aka gyara rigarsa aka tsaya da jiran umarninsa na a rufe a dauki hanya Motar dake gabansa wace Auta ke ciki ta fi daukan hankalinsa, hakan ya sa a hankali ya dan yi alamun zai yi magana Sosai bafadensa ya kawo kunnensa yana sauraro A takaice ya furta" Fatima ta dawo nan" Kasa bafaden ya kara dukawa yana fadin" An gama" sannan ya je ya sanar aka bude mata ta fito ta karaso da dan sauri tana dan sakin fuskarta kadan Shiga ta yi gefe aka rufe sannan ya bada damar a tayar su tafi Sai da suka dauki hanya sosai, a hankali ya rike hannun Auta yana kallonta, muryarsa a nutse ya ce" Menene?, Bakya so mu je gidan ne?" Auta ta kalle shi, a hankali ta shagwagwabe fuskarta, irin wannan kulawar sai idan Umma bata kusa take samu, idan tana kusa komai tarewa take yi , komai Idannuwanta ta lumshe hawayenta suka zubo, hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya dan jimke hannunta sannan ya mayar da dubansa bakin titi, Bai san yaya zai kwatanta irin raunin da jarabawar kanwarsa ke hadasa masa ba, Kanantarta, da innocense dinta na matukar saka shi a hali na tunani, uwa uba yakan rasa me take so, me take so ne a duniya? Mutuwa ai dole ce, itama zata mutu fa, ya dace ta yi hakuri shekara nawa da rasa iyayensu? Ama Auta ta kasa yin hakuri, shi kuma ba zai mikata wajen mijinta a irin wannan halin ba, a wajen mijin natama idan ta koma koda yaushe maganarta shine, bata da aiki sai tambayar ko yaya yake? Ita a kaita wajenshi kar wani abu ya same shi, idan aka kawotan an yi ta tambayarta mafarkai take yi ne wani abu ya same shi ko mene? Amsarta daya ce ba komai.....Yana rokon Allah ya sako hasle a cikin duhun dake tare da lamarin Kusan sallar La'asar suka karaso har fada, domin kafin su shigo sai da ya yi ta fama da jama'a, duda yau ba wani lafiyar kirki ne da shi ba, gaisuwarma sama sama yake amsawa, ama sai da ya fan tsaya yana dan amsa murnar karra aurensa, a ransa kuwa yana ayana' karin aure......karin yar matsala dai' A lokacin da suka sauka a falonsa, bayan an gama gaisawa, su Umma du sun zagaye su, Auta na like da shi irin abin nan na da wanda a kwana biyun nan sam bata yi ba, Umma ta dube shi tana murmushi da son cusawa matarsa haushi da kuma sin fara shinfida yarda tsakaninsa da amaryarsa ta ce" Yarona, lalle wannan biki shi ake kira tuwona maina, yar manya ce yarinyar, ba zaka ji kamar a aljana kake ba sai ka ganta, masha Allah ga ladabi, ga biyaya, ga salihanci a wajenta kamar kamar me, ka san meye ga kyauta, tana son talakawanka, masu tarbe sarkar zinarin nan ta basu da awarwarayen gaba daya, baka ga yadda talakawa suka dauketa ba, kwananta daya tak a fadar nan haka ake layin zuwa gaisheta, sai da na takatar dan kar ta kwashi gajiyar da zata kasa gaisheka yadda ya dace" Dan dagowa ya yi bayan ya gama tofawa Auta addu'a a yatsarta karama ya dan kalli Umma Dan murmushi ya sakar mata bai ce Um ba, bare um um, sannan bai kalli HUZNAH bama bale abin ya tsaye masa a rai Umma ta yi murmushi ta karra yin wata yar dariya tana sake satar kallon Huznah ta ce" Yanzu haka, tun kafin magariba aka gama shiryata, kanshi irin na an tubawa ke wasa a tufafinta...., Iso kawai take jira dan ta zo ta gaisheka" Auta ta kara lafewa dam a jikinsa , tana dan karra rike alkyabarsa da hannunta dan bata so ya tashi ya barta da Umma, matarsa kuwa shi kawai take kallo tana ta dannar zuciyarta da addu'a Wannan karron bai dago din ba ya ce" TA JIRA" Daga haka ya shiga kokarin tashi, zurbat Auta ta tashi tana cicira ido da kallonsa Gefen fuskarta ya shafa kadan ya ce" Kin sha maganinki kuwa?" Auta ta gyada kai da sauri, dan haka ya sake yin murmushi ya ce" To ki je wajen umanki kin ji? Tun dazu tana maki oyoyo kin shareta?, Ki tafi ta raka ki dakinki ta maki addu'a, kema ki yi kin ji autana?" Kai ta sada, ta dane kukanta, a hankali ta ce" To Abah" Murmushi ya yi ya juya yana fadin" Allah ya tashe mu lafia" Umma kadai ta iya binsa da iya yin da ta saba da adu'o'in da ta saba masa har ya shige sannan ta juyo da wani irin murmushi a lokacin da Auta ta yi wufff ta fita , HUZNAH kuwa na kokarin ficewar itama Dan takowa ta yi kasa kasa sosai ta ce" Sannu da rashin sannin ciwon kai, na ga harda kokari aka yiwa kishiya, sai dai ta bayar dan inaga bata yarda da ke ba, domin ko sakawa bata yi a wuyanta ba, gashi ita din shi yace yana so kin ga bambancin da nisa sosai" Du irin tsoro, da shayin Umma da take yi takan mayar mata da magana, dan hakane yauma ta dan gyara rufarta ta ce" Hakane Umma, na ga soyaya , domin tsabar so din nema ya