← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 87

Sashe 70

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta dawo min hankalinta tashe kan maganar, UMUGHLUK ITIBEL babu laifin iyalina a ciki, hasalima baki daya laifin nawa ne, nine na ce dole zamu bi, nine na nuna dole zamu aikata......." Ya ajiiye maganar hawayensa na sake balewa , sai kuma ya dago yana kallonsu ya ce" Na san kana shara'a ne idan kowa na gabanka a zaune ta yadda kowa zai kwaci kansa, haka kuma na san cewa kama fada a tsaye a kuma zaune cewa baka shara'a ka ware na gida, ko ka ware mai arziki, takobinka zata sari du wanni wanda ya kama ta sara, domin ka san zaka mutu , zaka tsay a gabam Ubangiji a matsayin bawa , zaka yi bayanin dukkan abinda ka aikata a duniya koda tsakaninka da tumbinka ne........." "KAI DIN MENENE DIN NADIRAH?" muryar Asadeek a sanyaye ya katse Hanzarin mahaifin NADIRAH Aba Salihu ya dago jajayan idannuwansa masu zubar da hawaye a sanyaye ya ce" Yata ce, ita dayaa tak na malaka a gidan duniya, INDI yarinyata ce" Kai ya sada yana tukar kukan da ta yannayin girgizar jikinsa zaka gane kuka ne yake shekawa abinsa ASADEEK kuwa baya ya koma ya jinginar da bayansa ya lumshe idannuwansa yana tasbihi ga ubangijinsa SHEIK ya kalli sarkin yanka ya masa alamun ya fita Fita ya yi, SHEIK kuwa ya fuskanci Aban NADIRAH a tausashe ya bashi umarnin dawowa ya zauna a waje mai kyau Da kyar da wala haula ya yarda ya hau kafet din, ama firr ya ki hawa kujera wai ASADEEK na waje ba zai hau sama ba Sheik ya yi murmushi yana kallonsa a tausashe ya ce" Bawan Allah, ka dubi girman Allah, ka yi kokari ka shinfida shinfida mai kyau a tafiyarka ta hanyar sanar mana abinda ka sani a kan auren nan da ya juya rana tsaka, kamar yadda ka sani a duniya idan bawa yanada hankali ba tsoron kowa zai ji ba sai na Allah, Akoy ranar fitar rai, akoy kwonciyar kabari, akoy tsayuwa a gabam ubangiji, ka yi kokari kaa tuna su sai ka zabi abu guda a ciki, tsoron dan Adam a duniya, ko na ubangijinka" Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya girgiza kansa, a nutse ya shiga magana kamar haka" Umarni aka bamu, cewa zamu bayar da yarmu a matsayin gimbiya BAHIJA, aka kilacemu aka shiga shiryata dan kasancewa mata a wajen UMUGHLUK ITIBEL," Sheikh ya kalli ASADEEK, yana nan a yadda yake, kansa na kallon sama, sajensa da bakin gemunsa lufluf a Kwonce, yannayin da hannayensa suke zai nuna maka a wanu hali yake mai girman gaske Sheikh ya sake sauke ajiyar zuciya ya ce" Ama, ko ka sam dalilinsu na aikata haka?" Sosai yake jin girma da nauyin dalilin da suka sani, ama ya zala wajibi ya sanar koda hakan na nufin mutuwarsa ne A sanyaye ya ce" An hada haka ne dan a kawar da UMUGHLUK ITIBEL daga doron kasa" A zabure Sheikh ya sake fuskantarsa, muryarsa har tana hadewa ya ce" Kar ka yi furuci dan ka fitar da kanka , ka san girman laifin da ka ambata kuwa?" "Na yarda cewa duniya ba matabata bace, na san da cewa idan na guji mutuwa a yanzu zata riskeni wata rana, na kuma san da cewa aikin alkhairina kadai zai sama min sasauci, da ace na yi gudun mutuwar da na gudo da iyalina mun kawo maganar, sai dai sannin da na yi kai tsaye ba zan taba yarda na tunkaroku da wannan maganar a min kallon mai hankali, da kuma sannin da na yi ina iya rufta kaina a ciki , sannan idan sun ci galaba a kaina sunna iya neman wani da aikin ya saka ni amsa, na saka rayuwar yata a hadari, ta matata da ta yar uwarta baki daya a hadari tare da yarda cewa Allah zai karemu, shi zai bamu mafita, shi zai nuna min rana irin ta yau" Aba Salihu ya fada yana sake duban ASADEEK Kan ASADEEK wani irin zafi yake fitarwa hakama kirjinsa har sama sama yake yi na tashin hankali, A hargitse ya dubi bangaren da Sheikh yake har yana hade harshe wajen fadin" UMMA, UMMA ce ta yi jagoranci a lamarin dauko amarya, shin bata san wa aka bata ba? Bata san tsare tsarensu ba?" Gaban SHEIK sai da ya yanke ya fadi, da sauri ya kalli ABA SALIHU gabansa na faduwa ya ce" Ni fa bana yi weekend fa *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 5 Gaban Sheik sai da ya yanke ya fadi, da sauri ya kalli Aba SALIHU gabansa na sake faduwa, sai kuma ya kalli ASADEEK muryarsa a tausashe ya ce" Me zai hanna mu dakatar da binciken haka? Ka fa san zurfafa bincike kai tsaye bashi da dadi fa, kuka bayan wannan ka gaji sosai dan Allah mu je ka huta" Murmushi mai daci ASADEEK ya yi yana kallon SHEIK, muryarsa a tausashe ya ce" Kana tunanin a irin yadda nake cakule da al'uma akoy abinda zai sameni daga dan Adam ya summar da ni?, Ina iya jiran komai daga dan Adam, kaine ilimina, nine alkalinsu, babu irin kwababiyar rayuwar da ba'a kawo min, ka daina yi kamar zaka yi kuka fan kawai na ambaci abinda kake son na gani shekara da shekaru, ka sani tunda na ji ba ita aka aura min ba nake bibiyar UMMA!, Tabas a da ina kin hakan dan na ga irin tsakaninta da Auta, kar ka manta UMMA ma'aikaciyar ANNA ce, watau amintaciyarta ta dogon zamani, ka fi kowa sannin amintacen bawa kan iya zama makashin sarki,nawa aka yi, tun kafin a haifeni ake yi, babu abinda kudi baya haifarwa da mulki, ka barshi ya sanar min matar da kuka zo tare shin ya ga wani abu da ta sani a cikin lamarin ko an rufeta a baibai ne?, Ka barshi ya rufa min asiri ya sanar min wanene AMINU?, Wadinnan abubuwan sunne suka kawo ni garin nan idan na ji su a yanzu a yanzu zan juya kasata, idan ban ji su ba kuwa ba zan koma ba!, Ba dan ina tsoron kar a cin min ba, ko daya, hasalima ji na yi ko menene ai bai isa ya riskeni in ba Allah ya hukunta min ba!, Magauta kuwa a cikinsu muke zagaye, ba wai ni ba harta baran gidana!, .......DAN ALLAH ka sanar min ita matar nan mai dan haske gajeriya mai dan jikin kiba kadan wace suka zo tare ta san wani abu a cikin lamarin?" ASADEEK ya karashe yana kallon ABA SALIHU, wanda shima tunda ASADEEK din ya fara magana ya fahimci tabas matar a kusa fa shi take sosai, kuma ya ji sunnan AMINU dainda cikinsa ya so rikicewa, kai jama'a wannan Aminu dai yana wahalar da shi ainun A sanyayensa ya ce" Allah ya taimakeka, in dai matar da suka zo tare ce kake nufi, wace tamkar itace ja gaban komai a lamarin, ita ta yi tuwo ta yi miya a tafiyar, domin a nanma zuwan sarki biyu wajenta sunna tsare tsarensu, ranar da za'a tafi da NADIRAR ma da kyar matar ta yarda mahaifiyar Nadirar ta ganta, wai kar ta lalata masu shiri a yadda ta sanar min" Hannaye biyu SHEIK ya saka a gaban goshinsa ya dafe goshin nasa, dan irin dukan da kirjinsa ke yi masa ba na wasa bane, gaba daya bai so ace ASADEEK ya ji irin maganar nan haka ba, ya so ace a hankali ya fahimta da kansa ba wai ya ji daga bakin wani ba ASADEEK kuwa jajayen idannuwansa ya daga sama yana kallon oankar dake gudu da dukkan karfinta tana busar masu da zufar jikinsu, ama sai yake ji kamar wace take tsatsafo masu da zufa ne, dan a wajen babu wanda baya alamu na zafi yake ji Idannuwan nasa ya mayar kan Aba yana mai jimke hannunsa, a hankali ya ce " Kana nufin, tana cikin shirin da suke yi?" "ASADEEK" SHEIK ya fada bayan ya dago kansa ASADEEK ya dubi SHEIK, ya sake kallon Aba Kai ya girgiza yana neman soke kansa kasa ya ce" Ba zaka barni na gama jin abinda nake son ji a nutse ba? Ka barni na ji mana ko zan iya musalta abinda nake tunani a kanta, kar ka manta da sunnan da muke kiranta, kar ka manta kanwata a hannunta take, kar ka manta nakan ce da kai ban san dalilin da yasa idan ta zo waje kanwata ke nutsuwa ta daina magana ba, nakan ce da kai ita kadai ce maganin kanwata idan ta rikice da maganar sai ta koma gidan mijinta ita kadai ke rarashinta ta bar maganar sai ta warke, kar manta bata da shamaki da bangarena a kowani irin lokaci, kar kuma ka manta tana da damar da HUZNAH bata da ita a fadata!, Ni a uwa na dauketa shi yasa nake kiranta UMMA, shi yasa nake zama a ci abinci da ita da iyalina!" Ya karashe da wani irin yannayi mai dukan zuciya Aban NADIRAH gaba daya sai ya ji shima nashi hankalin ya tashi a irin furucin UMUGHLUK ITIBEL Kennan wannan matar har haka take da kusanci da shi?, Lalle da ace zai bude masa dukkan abinda ya sani a kanta tabas zai ji masa mugun ciwo haka kuma idan har ya ci gaba da ganninsa zai ringa kallonsa matsayin wanda ya kawo masa mugun labarin nan, masoyi masoyi ne a zuciya fa A sanyaye ya sada kansa ya ce" Allah ya huci zuciyarka, bakin abinda na sani kennan" Da mamaki UMUGHLUK ya tsareshi da ido, kwarai ya fahimci ba gaskiya ya fada ba, ama kuma sai ya gaza fitar da hanyar da zai saka shi karfi da yaji yin biyaya, hasalima ji ya yi zai iya kyale shi ya zabi abinda yake so, fada masa ko kin fadi ya isa da hakan! Ajiyar zuciya ya sauke yana hararan SHEIK wanda ya sake soke kai yana sauke ajiyar zuciya da bawan Allahn nan ya gane abinda yake nufi, gaba daya baya so tashi daya ASADEEK ya san irin haka, lalle jarumi ne shi, ama babu wanda d ception irin haka ba zata yiwa ila ba,
Chapter 70 · 0% Book details