← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 87

Sashe 21

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta fice ta nufi bangarenta da mahaukacin sauri sauri mai kama da gudu gudu Tun daga nesa ta ringa hango Hindu na tsaye ta daura dan kwali a tsatsonta tana kakaba dariya tana tare tare har dai ta hango Nadirah a saman Dokin mahaifinta mai sanyin hali tana ta wahalar da shi sai aukin fadin CAI CAI take A haukace ta karaso ta damki hannun Hindu tana kallonta ido cikin ido ta ce" Maza ki dauki yarki da kayanku mu gudu!" Daga haka ta saki hannun Hindu ta nufi dakinta da gudu tana wartar dukkan abinfa hannunta ya kai kansa tana cusawa a jakunkunna idannuwanta a rufe Dagowa ta yi zata warci zannuwan Hindu da Nadirah ta ji a riko hannunta da riko mai karfin gaske an juyota A haukace ta saka ihu ta juyo hannunta a dunkule ta kai bugo a kirjin wanda ya yi mata rikon, tana dago kanta ta ga........ Oh rubutun sarauta ba fai rikici ba *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 1 *NOVEL DINMU MAI TAKEN CARBIN KWAI YANA NAN YANA TAFE CIKIN TSARI DA NISHADI, LITAFIN AKOY DUKKAN ABINDA KAKE NEMA A CIKI, SHAGALIN SAI KA LEKA, KA GARZAYO KAWAI KA SAMU NAKA HANKALI KWONCE , labarin Kwatena ne watau mai BADAKALA DA BAIWATA* A haukace ta saka ihu ta juyo hannunta a dunkule tadakawa wanda ya riketan bugo a kirjinsa tana dago kanta dan gannin ko wanene Wani ihun ta saka mai hade da barkewa da kuka ta jimke hannunsa tana sake kallonsa ta bude baki jikinta na rawa ta ce" Mu tafi, mu tafi, idan muka tsaya zasu fito mana da rikicin da ya fi karfinmu, kana ji barazanar da ta yi min cewa zata iya batar da mu, ko ta saka mu a ukun da mu da kanmu zamu nemi a kashemu?, Ita tana son y'arta har haka ni zata saka min ya a uku? Da UMUGHLUK ITIFAL take magana, yata zata mika dakinsa a matsayin y'arta? Duk ranar da hakan ta bayana da kansa zai zo ya tsire mu a jikin kanta, mu da kanmu sai ya mayar da maganarmu rikicinsa, bana ciki, babu maganar alkhairi, da ace magana ce ta alkhairi abin farin cikina ne, abanta, mu gudu ka ji?" Sake riketa ya yi a hannayensa a hankali ya janyota jikinsa ya rukunkumeta shima jikinsa na wani irin rawa tamkar zai kifa Gab gab gab haka jikinsa yake yi, muryarsa a matukar raunane ya ce" Marinki ta yi ko?" Tana cikin gunjin kukanta ta gyada kanta, numfashinta tamkar zai dauke dan tsoratar da ta yi, tunda take , tunda ta taso ba'a taba daga hannu aka sauke mata biyar ba sai yau, ikon Allah A hankali ya ce" Muna zaune mijinta na min maganar da ta maki ta fado tana sanar masa cewa ba zamu sauraresu ta laluma ba sai ta tsiya domin ita yanzu har marinki sai da ta yi da ranta ya baci, ban san dalili ba, ni dai na ga irin bacin ran da ya nuna har ya bani mamaki, domin a nan ya dauke fuskarta da mari har jikinsa na rawa......, Zahrau ban san dalilinsa ba, ama irin yadda ya nuna bacin ransa ko ni sai haka, a cikin fadansa ne ya manta wayon da ya so yi min ya fada min cewa idan muka yarda aka yi auren nan na dan lokaci ne zaki kawar da UMUGHLUK ITIFAL ki dawowarki wajenmu......., Wannan abu shi ya rikitani ya sakani kuka......." A hankali ya karashe yana kifa kansa a kafadarta ya ja wani irin numfashi hawayensa suka sauka a saman hijabinta, sannan ya karra matseta a jikinsa sosai ya ce" UMUGHLUK ITIFAL, sarki ne mai koyi da manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam , shi din bawa ne mai jin kan wanda yake wajen masarautarsama bale na ciki tsundum, UMUGHLUK ITIFAL idan ke bai kara ki ba ni ya karra ni, idan bai karra mu ba to fa in muka fita waje muka yi shela ya karra dubanmu, Fadimata na rantse da wanda raina ke hannunsa idan akace a yi fito na fito a yakin da ba za'a dawo ba dan a taya UMUGHLUK zan je ba tare da na yi tambayar menene ba'asin yakin ba, domin na sani ne shi din mai yi ne domin Allah ba dan ya karre kansa ba!, Zahrah ko ke bakya jin haka a ranki ne?" Itama tana kukan ta ce" Haba Abanta, idan akoy masu takama da sunnansa idan sunna maganarsa ai bayana suke!, Ko a yanzu da ace wata magana ce ta zuciya daya, ciki harda NADIRAH ta kasance baiwa a masaraitarsa, bani da darrrr zan saketa ta je da Adu'ar tsari, domin na san koda an sakata cikin halin kaka naka yi kafin ya yi zagayen karshen mako ne zai kwatar mata hakinta!" "Nima abinda na sani kennan, sai kuma furucinsu ya gigitani!, Ki sani maganar batar da mu bata gigitani ba, domin ni bawa ne, mai sallah, wanda ya yarda da kadara, na tabata idan duka duniya zata taru dan ta cutar da mu sai idan Allah ya aminta, idan Allah bai yarda ba, babu wanda ya isa ya yi mana koda kwarzane ne!, In kuwa kadararmu mu gama da duniya a haka ne muna dakinmu A'lah zai kawo dalilin fitarmu!, Wannan magana kamar tsarin film? Basu tashi hawanmu ba sai da suka nuna mana dukiya, lalle basu sanmu ba, a shekarun da muka yi a karkashinsu da wannan ne a gabanmu da mun taka wani mataki mai girm, domin da mun kasance bafadai masu hada husuma dan su samu na kashewa!, Sai Dai Zahrau Uban marayu ne zasu taba!, Zahrau hakan na nufin idan bamu amince din ba, zasu samo wani wanda zai amince din, hakan na nufin idan har muka kiya din, zamu zo mu tardo abu goma da gomi ya tara na halin ha'ula'i a gabanmu!, Zahra hakan na nufin munna da hannu a dukkan abinda zai faru" Idannuwanta ta dago da tuni suka yi hulu hulu tana kallonsa ta ce" Idan muka amince din, hakan na nufin mun kasance cikin masu mugun nufi dan mu cutar da shi? Idan ta je nesa da mu, hakan na nufin mun saketa a dokar dajin da ta yiwu wata rana su yi galaba a kanta har ta aikata abinda suke so? Abanta kar ka manta yarinya ce ita karama, wace ake iya yiwa barazana da rayuwarmu ta amince da ko menene kai tsaye dan kar a cin mana!, Sannan ita din tunda ta zo duniya ta ki jinnin gidan sarauta da abinda ya shafe shi, ko a jiya ina ce sai da ta yi maka hirar Aminu?" A sanyaye ya sake riketa a jikinsa yana rintse idannuwansa ya ce" kin fi kowa sannin na fi ki shakuwa da kulafurcin NADIRAHNA, kece ke min nasiha a kan soyayar da nake nuna mata, a yanzu haka wannan shine abinda ya dakatar da ni Innarta, a yanzu haka wannan din shine abinda ya zamto min katanga da daukan matakin amsawa kai tsaye, yaya zata dauki maganar? Yaya zata iya amsar maganar? Domin idan har hakan ce zata kasance sai na fuskanceta na sanar mata gaskiya, koda kuwa hakan zai zamto ajalina!, Innarta, shekararta kwata kwata ashirin babu yan watanni a duniya, yaya yarinyata zata iya daukan wani nauyin? Na tabata akoy abinda ya tunzura su daukan wannan matakin!" A sanyaye ta sake dubansa, ta rage muryarta sosai domin tana hangen Hindu dake kai kawo ta dan leko su ta koma kamar zata saki zani dan rikita A hankali sosai ta ce" Bari ka ji abinda yake faruwa......................" Gaba daya ta dauke duka kaf abinda ta sani wanda ya saka gimbiya da mijinta daukan matakin bada yarsu daj su wanke kansu, abin ya zo da rikicin nan n yar ta kiya shine gimbiya ta zame y'arta take neman tura NADIRAH Sosai hankalinsa ya sake tashi, ya rasa me zai ce , da kyar ya iya zama yanzun ya zamto itane a tsaye jikinta na rawa A hankali ya nuna mata daf da shi sosai, ta zauna tana sake dora kanta a gefen damtsansa A sanyaye ya ce" Ina cike da tsoro Fatina, kin ga ina jin tsoron halin da yata zata iya kasancewa a ciki, ina tsoron fuskar da UMUGHLUK ITIFAL zai duba idan ya gane cewa NADIRAH ba itace aka bashi a matsayin mata ba, duda na tabata ya aminta da wannan hafi ne dan shima da wani abin a kasa, domin na sani sarai dan kar a zage shi ko sirrinsa ya fito fili ba zai taba yarda ya kashe rayuwar wata ba!, Haka kuma ban san yaya yata zata rayu a cen ba, shin zata iya kaucewa cutar bawan Allah ko zata kasa?, Abinda na sani shine yarinyar cen ita daya na malaka, kuma ina son abita fiye da kaina, a kanta ina iya yin komai, sannan a yanzu da na ji maganar dake boye a cikin son su mayar da ita matar SARKI, sai na ji dama ace zan iya na yarda ta je, da zuciya daya ba dan sarautarsa ko arzikinsa ba, ta kasance wata jigo a rayuwarsa? Ko ita din wata mahadin rayuwarsa ce?" Hindu dake kofa a tsaye kamar ta afko ta sake daga labule ta musu kuriiiiiiiiiii, a dole summa suka kallota Gaban goshinta ta murza sosai ta ce" Yaya mu fece din ne ko kuwa?" Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce "Hindu zo mana" Ai kuwa kamar jira take ta shigo da sauri, sai dai gannin sunna kallon kofar ya sakata juyawa da sauri Haba ta kama ta juya tana fadin ina zuwa Karasawa ta yi ta kama hannun NADIRAH ta mayar da ita wajen zaman ta sake bata doguwar wukar babanta ta ce" Ki zauna a nan mana yar Hindu ba kyau labe ina zuwa, wannan riketa du wanda ya maki eh yane ki auna masa yar albarka ina zuwa" Kai ta gyada hankalinta gaba daya a tashe , har yar yatsarta ta gurde wajen dirowa daga kan dokin babanta gannin mamanta na rusa kuka, kuma sai ga babanta ya wuce fuuuuuuu shima, shine Hindu
Chapter 21 · 0% Book details