← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 87

Sashe 39

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lalausan murmushi tana gyara tsayuwarta ta ce" To dada, inaga a nan dai kice kawai matarsa a sanina, sai innata, idan kuwa ita zan kira maki toh sai naje aikar" Da sauri ta sada kanta, wata zufa na neman karyo mata, ta sake sada kan nata a hankali ta furta" Allah ya huci zuciyarki, Allah ya karra girma, Allah ya karra daraja Sarauniyarmu, In sha Allah zan isar da sakon, A gama lafiya" NADIRAH na tsaye tana kallon ikon Allah har matar ta fice kamar zata kifa Ido ta kikifta kasa kasa ta ce" Allah mai alkhairi" Daga nan ta koma tana yiwa Innarta hira wace ta yi bake bake a wajen Four tana jira abinda suka saka ya gasu su ciro Tunda ta shigo har falo dan Umma ta bata damar shigowar a tunaninta tare suke da NADIRAH ta zube kasa, kanta a kasa ta kasa fadar sakon da ta gumtso a bakinta, domun har jikinta rawa yake yi a lokacin da ta fahimci kwarai da gaske ZAKIN SARAKAI na zaune Umma da dan takaici ta ce" Ki fadi sakon mana kin tsugunna a waje kin mana shiru bayan kin ga ke ake jira?" Kai ta sake dukarwa kamar zata kifu, muryarya a raunane kamar zata fashe da kuka ta ce" Allah ya taimakeki, sako daga sarauniyarmu, tace ace girki take yi, sai dai wani jikon" Ba Umma ba, harta UMUGHLUK dake dan kallon Huznah sai da ya yi dan tsai , uwa Uba UMMA da ta kallota a zabure, hakama HUZNAH da sai da ta kusan mikewa dan tsorata, a gangaro kan Auta da ta dago tana zarro idannuwa kamar zasu fado tana kallon Baiwar, wace tuni take share hawaye, hawaye na tsoro, domun an hore su da fadin gaskiya, bale irin wannan dole zasu sanar da abinda suka gumtso, sai gashi, sai gashi ta gumtso mai karfi, kuma Umma ta saka ta fada a gabam Uban gidansu baki daya Umma har hade harshenta take yi wajen fadin" Rufe min baki, wannan wace irin magana kike yi haka?, Na tabata wannan sako ba daga ita ya zo ba, waye zai shige kasam rigarta ya bata mata sunna run kafin ta ga mijinta? Na tabata wannan sako an yi shi ne dan a hadata da UMUGHLUK ITIBEL, maza ki tashi ki rakani wajen wace ta baki wannan sako, ko wacece na ganta, domin na tabata ba dai Sarauniyarmu ba!, Kuma ko waye a bayan haka zai bayana ne!" Shi ihun da Umma ya fi damunsa, haka kuma kafin ya yi wani abu har Ummar ta fice kamar zata kifa Juyowa ya yi zai yi magana dan HUZNAH a tsaye take itama , da niyar umartarta ta zauna sia ya ga wani murmushi ya kubuce daga fuskar Auta Dan kallonta ya yi, sai ya samu kansa da yin murmushin shima Muryar HUZNAH ce ta dakatar da shi a lokacin da ta duka kanta a kasa ta ce" Allah ya huci zuciyarka, na tabata da wani abin daban, ta yiwu bata gane sakon daga nan ya fito ba, bayan wannan me hadinta da kicin? Sam sakon ba naka bane" Ido ya dan sake kura mata , haka kawai ya samu kansa da tunanin toh daga ina sako ya same shi haka? A masarautar nan? Ko daga wata masarauta, komai rashin da'ar Yar sarki ko matarsa, ba zasu turo da sako haka ba gaskiya, ta yiwu bata gane din bane, ko kuma ba ita aka ba sakon ba, shi abinda yake dan bashi mamakima shine, bata gane waye aka aura mata bane? Ko an mata nasihar zumudi ne? Dan kwarai ya yi tunanin a kofa zai tardota tana binsa da kallon nan kamar na mahaukata, sai gashi shiru Murmushi ya sakarwa matarsa, hakan ya sakata suake ajiyar zuciya, domin damuwa ta sameta kar ransa ya bace abin ya shafe su baki daya, domin ba zata iya tuna bacin ransa ba, bata so, bata son tunawa, bata ga da kyau ba ko kadan, a ranar da ya yi bacin rai mai sunna bacin rai? Bata ga da kyau ba ita da kanta, bale wa'inda le zagaye da su ___________________________________ A haukace Umma ta shigo, bayan ta dakatar da Baiwar da ta tabatar mata nan ta shigi ta kuma kwatanta mata wace ta gani Hankali tashe, rai bace ta dubi Inna dake rauda kai tana kallon TV ta zabura jin budewar da shigowar ta ce" Ashe bata da hankali? Ta san da wace irin wuta take son yin wasa? A tarihin rayuwata ko a zamanin iyayensa ban taba gannin an bashi amsa kai tsaye irin haka ba, hala bata da hankali da zata ce a cewa UMUGHLUK ITIBEL tana kicin ba zata samu zuwa gaishe shi ba sai wani jikon?" Daga saman kujera sai da HINDU ta fado kasa warwas sannan ta dabi kai kamar mai shirin tayar da aljannu ta ce" Lah ha ila ha ilalahu muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam, wani shegen rikaken dan iskan makaryacin ne ya gilawa Indi karyar nan? Allah na tuba yar da ko fitowa bata yi ba muna ciki muna dahuwa? Ka ga shari irin na masharanta, in itace a yau a yanzu yanzu in zama wancen TVn a ringa jona ni dan Annab............." "Innata" Indi ta fada da dan karfi tana zarro ido dan gaskiya ba zata iya yin shiru innarta ta yi rantsuwar alkaba'i a kan gaskiya ba, Ido ta ribga kikiftawa, hakan ya saka HINDU yin wuki wuki murya a raunane ta ce" ki bari na karasa rantsuwar nan kin ji yar indi? Ai ba kina nufin na yi shiru bane ko?, Ba zaki aikata haka wa babanmu ba ai ko?" Indi ta yi shiru tana murza hannunta, sai kuma ta ce" Gani na yi muna girki a lokacin ne innata" "Karbi nan, na ce dambulaninki Indi zo nan dan ubanki na gagaura make mari, so kike a shake mu muna ihu har mu daina? Zo nan" HINDU ta fada tana rarumar abu ta mike dan ta shako Yar........... Mun shiga uku *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 2 Ba edditing NADIRAH ta yi tsuru tana kallon Innarta, da Umma dake salalami ta kasa tsayuwa a waje daya Innarta ta sake kallon Umma, sannan ta kallo NADIRAH ta ce" Yar gidan Habu makadi ki zo ko na zo?" NADIRAH ta sake shagwagwabe fuskarta ta ce" Innata, gani na yi magariba ta shigo, kafin mu karasa ai ta yiwu kuma ya shiga barci dan ai baba baya jira barci na iya daukansa koda yaushe ko Innata?" Hindu ta karra tafa hannu tana sumurtu, lokaci daya ta dage zanninta ta haura shi saman ciki sannan ta nemi tsalaka kujerar dake tsakaninta da Nadirah Ido NADIRAH ta zarro, ta sake kallon innarta Da gudu NADIRAH ta fala cikin dakinta ta rufo harda saka Ky sannan ta karasa wajen kujera ta zauna tana sauke numfashin gudun da ta sha sannan ta dan tsurawa waje daya ido tana dan balancing din kafafuwanta Samun kanta ta yi da mikewa ta karasa gaban madubi ta dan rankwafa kadan tana daure gashin kanta a baya Dan murmushi ta yi tana girgiza kanta kasa kasa ta ce" Amarya , Amarya ce, koda ta auren dole ce, koda ta karkara ce, in ba abinka ba baban su Inna ai mu mutanen karkara mun fi kowa riko da al'adu, a gida ba mace ke fara zuwa wajen miji ba, koda sarki ne, kasancewarka bako koda wanene kai ba shi zai saka a kwasheni a kaini gaisheka ba....., Duda ba maganar fahimtar junna ko tare yawun tsufa zan yi ba, ama a ji labarin nan a labba ai na fadi ba nauyi, Idan har da rabon mu gaisa zamu gaisa in la zo nan da kanka Babansu" ( kuturu abinda kike shiryawa kennan? Lalle kin traro match) A falo kuwa zaman dabar Innarta ta yi tana salati tana sanar da ubangiji tana kallon Umma ta rasa me zata ce mata Umma ta dafe kai itama da takaici ta ce" Ta kula, ta ajiye shirme da yarinta da wasan dake dawainiya da ita, ta ringa bambance baba da kuma dan gidan baba, ki fahintar da ita shi din baba ne, ba maganar wargi tsakaninsa da matarsa, ko waye ba zai rainashi ba, koda matarsa ce shi din sarkinta ne!" Hindu sai ta samu kanta da jin maganar wata iri, ko matarsa ce shi din sarkinta ne? Toh mutane, yo ai itama da ta tsorata dan Indi bata riga ta zama matarsa a aikace bane, da hakan ta faru ai tana gannin abu ne daka iya faruwa tsakanin mata da miji ko? Ama yaya Umma ke dan so ta nuna kamar Indi ta yi sabo? Umma ta dora da fadin" Bale a gaban kishiya take, matar da ta ci hakuri ta kora da ruwan zurra ido,matar nan ni na tabata hakurinta zai kasheta wata rana, kin kuma san maza na masifar son macen da sai yadda suka yi da ita ko?" Hindu ta karra yin tsuru, ita Umma na magana ne ira tana aunawa a kankin kanta, Allah ta tuba ita din nan karan kanta maganar ba wata ji take yi ba, tsakaninta da Habu wani lokacin sai ta zo barci take lalabawa ta tashe shi a yi zaman tsakiyar dare a yi magana a yafewa junna, bama idan wata ya raba tsaka ya zama tulelen nan, takan ji komai a fili yake Alkur'an, takan bashi hakuri shi kuma yakan ce in bai yafe mata ba ai shi zai shiga uku dan idan ta tire daga yadda take yanzu ta yiwu a mata sarauniyar makada......., Gaskiya a nan tana iya cewa Umma kamar ta yi daya, wasu mazan ai a lokacin da kika zama sai yadda suka yi da ke din nema suke cin kaniyarki, Allah mun tuba a rayu da tunnanin za'a mutu kawai, in ba shi ba ai har a dambatu da makocin raba gado Umma ta ci gaba da fadin" Mema ya hada fatarta da girki?, Ina ita ina aikin da aka zuba mata bayi dan su yi mata? Wanka kansa bai dace ta yi da kanta ba, ya dace ta dauki
Chapter 39 · 0% Book details