← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 87

Sashe 52

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai kuma ya dan murza goshinsa yaa ce" Kika ce, auren wani kika kiya?, Kar dai ki ce min iyayenki kika bijirewa a kan gaibu?" Bahija ta yi tsuru tsuru, jin amon muryarsa a nan ta tabata idan har hakaan ne yana iya yin fushi, kai tsaye ta ce" Aa, ba bijire masu na yi ba, su suka bada BAIWATA a kambacina" Dukkan da maganar ta yi masa sai da ya ajiye wayar a kasa ya zuba mata ido yana kallonta Afkawa da ya yi a tunani ya saka shi manta waya yake yi har ta kashe a rikice ta sake kiransa kusan sau hudu sannan ya mika hannunsa ya dauko yana sake kallon sunnan ya daga ya sake kusantata da kunnensa ya yi shiru *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 3 Ya daga ya sake kusantata da kunnensa ya yi shiru yana sauraro "Dan Allah ka saurareni, bana so ka yanken hukunci kai tsaye, ka sani ni ban taba soyaya ba, ban taba sannin yaya take ba sai a kanka, iyayenaa kuwa ba bijire masu na yi ba, kuma mijin da suka so bani ba sonshi nake yi, na tabata shima haka, ka ga hakan bashida wani anfani ko?" Ta fada muryarta na nuna tashin hankalin da take ciki A hankali ya iya bude bakinsa, ya ce" Baiwa?, Baiwarki?" Tambayar ta zo mata a wata iri, dan haka ta nemi karrin haske A tausashe ya ce" Kina nufin ke din jinnin sarauta ce?" Amsar da Bahija ke tunanin a gaban kowa tana iya badata da takama da isa domin abu ne na isar da takamar kasancewarta yar sarki, a yau sai ta samu kanta da mugun tsoro da zulumi, bata san me zata ce a matsayin amsa ba, tana tsoron ta fadi abinda ya saba muradin Balarabenta ya bace mata kamar yadda ya saba, hakan ya saka ta cewa" Baka son famillyn sarauta ne?" "Kusan haka, kin san ni lamarin sarauta ne bana so, bale auren yar sarakuna? Anya zata iya yin biyaya? Gashi inada aiyukan da basa son ciwon kan mace!" Ya fada yana sake danne zafin da kirjinsa ke yi masa Muryarta ta tausasa sosai, a sanyaye ta ce" Sarautar ba wata mai karfi bace, idanma da hali mu bar maganarta , ka dauka ni ba jinnin sarauta bace in dai hakan ne zai faranta maka, dan Allah ka zo gidanmu, ko ni ka fada min a wace kasa kake da gidanka, zan zo, zam zo walahi" Da kyar ya sake iya bambarar bakinsa ya ce" In sha Allah, zan saka rana na zo, zan yi kiranki domin bani da isashen lokaci" Haka yauma, tans ji tana gani, bata koshi da sauraronsa ba, bata san matsayarsu ba, bata gane zai zo din ba da gaske ko aa?, Ya katse kiran da nufin yana busy, haka kuma ta damu kanta da sanyaya zuciyarta, da fadawa kanta cewa ai da sauki, wanda zai tashi ya taka leda, ko ba komai sannu sannu bata hanna zuwa, ta tabata a yanzu da ya ji saboda shi har ta ki auren wani zai dubeta, ta tabata kuma zai aureta idan suka zauna, in har maganar sarauta ce baya so ba sai ta fada gaskiyar asalim sarautar tasu ta yayane suka sameta ba?, Tunda abin na neman hadawa da farin cikinta komai na iya faruwa, ciki harda iyayenta walahi! (To dai, baki ke yanka wuya) .................................................... *BAIWA?* Baiwarta? Wace irin baiwa? Baiwa dai? To ama, shi kansa ya shiga cikin duhu Bawa fa du yancin da zai samu kansa kasa yake gaisar da uban gidansa Babu mutumen da ya san darajar sarki da tsoron sarki irin bawa Bawa komai fitsararsa fa son duniyarsa a tsorace yake da sarki Du arzikin da bawa zai yi a duniya kuwa idan ya tashi gaishe da sarki sai ya duka Wacece ita a duniyar bayi? Wace irin wayewa ce da ita a lamarin bayi? Ta yaya zata kasance Baiwa bayan idannuwansa take kallo ta ki bashi amsa? Ta yaya zata zamto baiwa, bayan ta yi sa in sa da Huznah? Wacece ita a duniyar bayi? Su waye iyayenta a tarihin bayi? A hankali ya sake gyara zamansa Afkawa ya yi a tunanin me yasa za'a aura masa baiwa to? Yaya sunnanta na gaske? Me ta zo yi? Shin Umma ta sani ko bata sani ba? Tabas wani abu ya dan tsaye masa a rai na hargagin da Umma ta yiwa yarinyar nan a jiya, Koda karama ce, koda Umma uwa ce a wajensa, Yarinyar sarauniyarta take, a laluma ya dace ta dakatar da ita .......ama, ama sai......... Da sauri ya kore wannan tunanin yana astagfari, domin ya gane shedan ya fara kawowa tunaninsa hari Wayarsa baba ya dauka ya yi kiran number Umma A tausashe ya sanar mata a sanarwa HUZNAH da Auta yau ba zai yi zama da su ba a falo Ta tambsyeshi tana fata lafiya yake? Harda nuna masa cewa zaman da yake yi da auta tana jin dadinsa domin Auta na kwontar da hankalinta idan tana tare da shi Ya tabatar mata lafiya kalau, yana da bukatar hutu ne A dole ta hakura ta yanke kiran Wayar tafi da gidanka ya janyo da kansa ya sake zaunawa yana dan tunani A nutse ya bude litafi ya saka code din bangarenta A irin wannan lokacin zaune suke sunna hira da kyakyata dariya ita da Innarta, Kukan shigowar kiran sai da ya saka suka tsorata sannan suka zubawa abinda ke ihun ido Da kyar a kira na biyu Innarta ta yi shahada ta karasa tana fadin" Ki tsaya ke dai daga nesa, idan kiran mai sama ne ya sameni kya fadi ga abinda ya kasheni, ama ni kamar ma gani a wayar Habu wani lokaci muna kallon masu jan kunne kamar salula ce, bara dai na gani" NADIRAH ta yi tsuru tsuru, ita dai ta ga abin nan har a dakinta, har a kicin dinta, ko'ina fa, tace kwaliya sai yan birni, sai ga abu na kuka kirrrr kamar tsohon keke mai rubabiyar kaca?, Allaaj jishe su alkhairi Takarkarewa Inna ta yi tana dagawa ta ce" Hallo, Hindu ce a kan layi waye ke magana?" Shirun da ya biyo baya ya saka Hindu cirewa ta kalli NADIRAH ta ce" Indi anya waya ce? Kin ji shiru kamar mutuwa ta gitta" Karasowa ta yi, da sanyayar muryarta wace idna ta yi magana da ita kamar ba zata tofa komai ba sai zikiri ta amsa gana fadim" Innata bara na ji, Mutun ko aljan daga ciki muna sauraro" Gaban goshinsa ya sake dafewa a hankali yana shafawa yana tunani a zuciyarsa A hankali ya furta" Da dare, ina son ganninki a Bangarena" Wata zabura da ta yi ta fancakalar da abin wayar a zabure, kasa kasa sosai ta ce" Inna Abanku ne Fa" saurarawa ya yi sosai yana jin abinda suke fada, Abansu? Aban su wace inna toh? Innarta kuwa sai da ta wuntsila tana dora hannayenta a kai ta ce" Kin ga NADIRAH zan ci ubanki Habu bilahilazi, yaya zaki ce Zaki ne ya kira?, Ta yayama zaki zai kira?, Bayan wannan ina yan aike da takarda? Ke kam inaga dole na fara neman na aljanu kuma, abin na rikecewa a hankali bamu gane ba" NADIRAH ta dauki abin ta mayar ta makala ta zauna kusa da Innarta ta ce" Innata walahi muryarsa ce, abinda na san muryarsa yadda kika san rusheshen kato idan yana magana, bobobobobo abu a hade dai kin gane ba kamar maganar Aminu aminu ruwan sanyi ba, jiyan nan ma fa ya ja min kashedi, cewa ya yi da dare na je, na je na yi me kuma? Ni mai kaurin sunnan nan,ban yi bama ance na yi?" Da kyar innarta ta yarda, sai kuma ta shiga yi mata nasiha tana cewa ta yiwu wani abin ne , sannan ta shiga tsoratar da ita da kiyayewa da yi masa haye, sannan ta kyaleta ta mike ta shiga tunanin me ya dace yau yar ta saka? Lamarin ne kowa na kula nasa a boye, itama tana tura NADIRAH da su kwaliya su gyara jiki su matsewa a zuwan ta saka abinta ta more, kayanta ne, kuma ba haramun bane kafin su tafiyarsu ta san ta mora, ita kuwa gaba gadi ta yarda. A bangarensa kuwa sunnayen nan uku uku ya kawo ya hade da maganar da ya yi da BAHIJA Kai ya girgiza yana dan tunani, sai kuma ya mike a nutse ya haura sama domin ya hanna kowa shigowa dan hidimta masa wani abin idan ba shi ya bukaci hakan ba ____________________________________ Zuma ce farar saka, irin sabuwar nan mai kyan gaske Hindu ta juye a cikin hadin da ta yi na gumbar mata ta dameta sosai sannan ta rufe a kwano mai kyau ta sake nufar dakin INDI Kwonce take a kasa, watau saman kafet barci na wartarta, jikinta wando ne irin mai laushin nan mai lafewa a fatar jiki , sai riga mai siririn hannu wace ta dauke mula mulan mamanta , domin mamanta ba yan biri biri bane gaskiya, ta baje tana barcinta hankali kwonce HINDU ta zauna tana tashinta a hankali Dagowa ta yi tana shanye lumsasun idannuwanta ta ce" Inna barci fa nake zaki tasheni?" HINDU ta ce" Na sani, ki tashi ki je ki ji kiran da yake maki mana" Baki ta turo ta ce" Inna, na fara barcin? Ki bari sai gobe mana" Kai ta girgiza tana talabota ta ce" Kin ga damu na yi ungo shanye ba yawa, kuma ki je ki dawo ki yi kwonciyarki, kin dai ji abinda Aunty tace ko?" Sosai ta sake bata fuska ta amshi abin sai turo baki tale yi ta dan kafa a bakinta Dandanon zakin ya sakata bude bakin da kyau ta shanye sannan ta nemi neman komawa ta kwonta, bata san abinda ta shawa kanta ba, Gumba ce VIP, gumba ce ta gagararum matan da suka san kansu suka kuma yarda da kansu, a hadin gumbar ana saka sinadarai na mugun motsa sha'awa, ko budurwa kike idan kika sha sai lamari ya motsa maki bale wace ta san hanya, gumba ce mai
Chapter 52 · 0% Book details