Sashe 43
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
daga tsugunnin? Ta tuba a gafarceta" Baki NADIRAH ta turo kai kace zaa saka mata ribom ne a daure ta kalli Auta da kallo irin na harare harare wanda hakan ya saka Auta zarro ido tana kallonta Bai ce komai ba ya mike a hankali ya juya ya shiga haurawa sama, wanda hakan ya saka Matarsa mikewa da dan sauri ta bi bayanshi NADIRAH dai da ta dafe kugu sannan ta kai zaune a fili ta furta" A gayasssss" wanda sam bata san ya fito fili ba Auta ta sake wangale baki da zarro idannuwa kamar zata fado dan mamaki tana kai hannunta daidai bakinta ta furta " Lah " NADIRAH ta dago tana kallonta, samun kanta ta yi da karra kallonta itama , sai kuma ta ce" Yo tsakaninki da Allah me na masa ni, tun dazu kuke cewa na tuba kuma bakwa fadin laifina, shikenan dan nice bakuwa sai a cuceni? Haba dai" Da mahaukacin mamaki hadi da wani zarro idon Auta ta ce" Aban ne zai cucekin ko wa?" NADIRAH ta yi shiru tana kallonta, sai kuma ta mike tana kabe Alkybarta kamar ta yi kasa din nan ta ce" Babanki ne kennan?" Auta ta girgiza kai tana murmushi itama ta mike tsayen tana kallonta ta ce" Yayana ne" NADIRAH ta kama haba da mamaki ta ce" To fah, shi kowa Aba yake ce masa ne?" Auta ta dage kafadu tana jin mamakin yadda Bahija ke magana a sake, irin ba abinda ya shafetan nan NADIRAH ta ce" To sai an jimanku, bara na koma na san ana cen ana jirana" Auta ta yi saurin fadin" Da wuri haka zaki koma? Ga fa abincin da aka tara mana saman table" NADIRAH ta waiga wajen abincin, tsarin kwanonin kadai abin birgewa ne, sai dai a ranta ta ayana' kai ina, aje an zuba gubar a ciki' a bayane kuwa sai ta ce" Aa a koshe nake fam da kika gani a nan, a ringa bismillah dai in za'a ci abinci...... Daga haka ta yi ficewarta hankali kwonce, ta bar Auta cikin tatauna maganarta Haka kawai sai Auta ta ji kamar da wata manufa tace a ringa yin bismillah Sai kuma ta koma ta zauna tana murmushi, rabonta da ta ga rikicewar Umma haka an jima walahi, Ama wannan matar ko wacece ta birgeta, sai ta ji kamar kar ta tafi , kamar ta yi ta zama da su a nan din, tunda ta shigo wajen ake haba haba gwanin dadi A tsaye take a gefensa, bayan dogon hakurin da ta bashi har ta rufe bakinta bai bata amsa ba Sai da ya gama yanke shawarar abinda zai yi ya dubeta yana murmushi ya ce" Ba komai fs, ki je ku ci abinci" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya ta tafi Wayarsa ya dauko yar karamar ya zauna a bakin bed yana warware nadin Rawanin dake kansa A hankali ya shiga wajen tarin uban miscall din da yake samu na number da aka duba masa aka tabatar ko ta wacece Number ya dauka ya turawa yaronsa sannan ya rubuta masa mesage cewar a yi gagawar yi masa tracen number nan zai yi kira a sanar masa ina mai number take? A nutse ya gyara zamansa sannan ya danna kiran ya ajiye wayar a kusa da shi yana dan shafa gemunsa idannuwansa sun kada sun cenza launi Wayar na fara kuka aka daga, ringin ko na biyu bata yi ba aka daga hafi da sauke wata nanauyar ajiyar zuciya murya a birkice da kukan dadin gannin kiransa ta ce" Asalamu alaikum yah habibih" ASADEEK ya sake murza sajen habarsa cike da takaici a takaice ya amsa salamar da lalausar muryarsa da karyewar harshensa tamkar balarabe BAHIJA ta kai zaune tana kashe TVn dake kida ta dora hannunta daidai zuciyarta ta ce" Ina ka shige? Dan Allah ina ka shige? Har na cire rai, na yi kukan har na hakura, kulun cikin tunaninka nake, ka bani number na kira na kira ba amsa, tun bata shiga ta zo tana shiga, mamana tace ta yiwu aiyuka sun maka yawa, dan Allah ka fada min a wani gari kake a NIGAR zan zo, idanma baka da lokaci ni zan zo" 'innalilahi wa inna ilaihi rajune, ya Allah ya Allah me yake faruwa da ni ne? Wace aka daura min?...........' A kala ta dauki minti daya tana ratabo zance na rashin kamun kai, har ya tabata ko menene sun gama masa a sanyaye ya furta" Zan yi kiran ki, zan je na dawo" Muryarta a sanyaye ainun ta ringa magiyar dan Allah kar ya manta ya yi kiranta dan Allah tanada wata mmagana mai mahimmanci da zata sanar masa Uhum kawai yace ya katse kiran, A nutse ya mike ya shiga cire kayansa dan ya fara jin sun masa nauyi Ya rage daga shi sai karamar rigar ciki da wandon shadar da ya cire Kiran yaron nasa ya shigo, nan yale sheda masa daga garin Tanut ne, harta da anguwar sai da ya sanar masa Wayar ya tsurawa ido, still kirjinsa na dukan tara tara A hankali ya lalubi number SHEIK Wayar na fara ringin shima ya daga a kamilance ya yi masa salama da gaisar da shi ASADEEK ya bude idannuwansa yana fadin" Da wa ka daura min aure ne Sheikh?" Sheikh ya yi shiru dan bai fahimci hausar ba, sai kuma ya dan gyara zamansa ya ce" Da yar gidan Sarkin Tanut ko? NADIRAH wace ake yiwa kiranye da BAHIJA?" Wara manyan idannuwansa ya yi, da karfi ya damki abin rufar gadonsa ya jimke yana rintse idannuwansa, hakan ya sa jijiyoyin jikinsa mikewa birde birde Muryarsa a cinkushe ya ce" Karfe bakwai ina son ganninka a sashena in sha Allah" Daga haka ya kashe wayar ya sake gyara tsayuwarsa yana ta aunawa, abinda yake ta korewa baya son kawowa ransa shine, Umma ce ja gabar auren nan fa, me hakan yake nufi? Umma ce fa? ...........( Uhum )................. NADIRAH hankali kwonce ta bude bangarenta, watau baban kofarta ta shiga, domin ta hanya sak ta biyo tana salama a saman lebenta Mikewar Umma kawai suka gani, sai saukar yan yatsunta biyar a saman kuncin NADIRAH, wanda hakan ya kusan gigitata, domin wani ihu ta saka wanda ya saka innarta zaburowa hankali tashe ta nufo wajen tana kama sunnan Nadirar da karfi Umma ta nuno su gaba dayansu ranta bace ta ce" Wannan shirmen, da gidadancin, da kauyancin da kika yi yana daf da tashin hankalinki, da cire numfashinki, daga ke har iyayenki, domin ni nan da kika ganni ba zan taba daukan wahalarku ba walahi!, Me yake damun kwakwaluwarki? Ko mahaifinki ne kya masa wannan gaisuwar bale wanda ya fi shi daraja?, Ina ce an ce maki idan baki san abin fada ba ki yi shiru?, ASADEEK zaki duba ki ce masa barka da saukowa?, Yana saman kujera kina bakuwarsa zaki haye darr ko zauna?, Yana cikin fushi kike kallon idannuwansa?, Karya kike yar talakawa yar bayi! Karya kike idanma kina nufin ke baki iya bane!, Mu zaki kawowa shirme? Mu zaki kawowa maganar banza?, Idan har gangancinki ya haifar da rashin yarda sai dai ke ki kwana ciki, yanzu ki fada min bayan fitata me kika karra aikatawa na hauka?" NADIRAH da ta fashe da kuka a jikin innarta, innarta ta dagota murya a shake ta ce" Ki kama min baki, ki min shiru, marin na waye baki sani ba?, Ki min shiru nace!" Kukan nata ta ringa shanyewa, idannuwanta jajari ta kai dubanta kan Umma Zata yi magana Innarta ta tareta tana rufe mata baki Innarta ta dauke Umma ta yarfa da asakaran kallon da ya saka Umma zuba mata ido Rai Bace HINDU ta ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 3 Rai bace Hindu ta ce" Mari? A fuska? Waje mai daraja? A kan laifin da ba'a koya mata laifi bane? Ita fa bata rayu cikin gida irin naku ba, a sake ta rayu fa, hakan bata san laifi bane ba fa!" Umma ta sake zubawa yannayin Hindu ido, tabas ta karanci ranta a mugun bace yake, a yannayin da take magana tana dan bari zai tabatar maka tana hanna kanta wani abu mai girma ne Umma ta sake kallonsu su dukansu sama da kasa, sai kuma ta juya ta fice ba tare da ta karra furta komai ba HINDU ta juyo kan Nadirah, stilll ranta bace ta mata nuni da dakinta a kausashe ta ce" ki je ciki" Nadirah ta juya jiki amace tana jin kamar fuskarta ta sundume ta shige dakin nata HINDU ta tafi ta rufe falon ta dawo ranta a bugun bace ta ringa doka hannunta a kasa tana cije lebenta har sai da ta samu hawayen sannan ta hade kanta da gwuiwarta tana shashekar kuka Wannan shine daidaikun kalubalen da y'arta ke iya fuskanta Rayuwar rashin yanci Wannan shine abinda ke iya zuwarwa Nadirah a ba zata , domin a tunaninta haka din abu ne marar tsauri, ba wani laifi ta aikata ba a tunaninta, idan har aka yi duba da wajen da ta tashi, za'a iya yi mata uzuri Gannin ta kasa daina kukan zuciyarta na daci ya sakata shigewa ciki ta dannawa yayarta kira Rai bace take labartawa Fadime abinda ya faru har zuwa marin FADIME ta lumshe idannuwanta a sanyaye ta ce" HINDU, tsaya ki ji, a irin hukuncin da ya dace yarki mari an mata mai sauki, sannan kar ki ji wai, idan har ta yi sake ya gane tabas zai fito neman ba'asi da karin haske, domin abinda ta yi ba aiki bane na an sarauta" HINDU ta ce" Aunty, ama kina tune, abinda aka koya mata an koya mata gaisuwa? Ko ta yi zaman da zata ga yadda kike yi? Ba ita ba, nima fa ban iya ba" Fadime ta ce" Haka ne, ama abinda nake so da ku baki daya shine, yanzu ya dace ku zauna ku karanci damuwarku, ku samawa kanku mafita, kar ku ringa manta abinda ya sakamu shiga bakin kura mana, ya dace ta aro halayan yayan sarakan koda bata sansu ba, ya dace a yanzu ta koyi kamantawa, in