← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 87

Sashe 86

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shamaceta ta maka siga , ta ce" Abah, wani abu ya faru ne ama ko?" Dan dakatawa ya yi da abinda yake yi ya dana kalleta, sai kuma ya yi shiru bai bata amsar nan ba, dan gani yake yi maganar kamar ta fi karfinta , ko yace ba maganar da ya dace ya yi da ita bane Dan murmushi ta yi, zuciyarta na mintsininta da son sanar masa maganar cikin, tana cikin shakun idan ba cikin bane ba fa? Ama kuma irin yadda Inna ta fada da tabatarwa sai take jin kawai ta sanar masan "Dama maganin da take baki, kwaya ce ba asalin maganin samun lafiyarki bane?"..................... Ya fada da air na seriuss bayan ya ajiye plate din hannunsa bai dauki Cake din ba yana fuskantar Auta Gabanta sai da ya fadi, dan magana idan dai ta shafi Umma ko yayane daga mata hankali take yi Jiki ba karfi ta kalli Abahnta, sai kuma ta sake sada kai Ko yayane Abahnta ya gano wace Umma tunda har ya kawo wannan matakin a bincikensa Muryarta a raunane ta ce *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 6 Muryarta a raunane, kanta na kallon kasa sosai ta ce" Abah, sai bayan an mayar da ni gida, an sake dawo da ni na fahimci maganin ba na taimakona bane, na kwaya ne, daga baya ita da kanta ta sheda min hakan" Idannuwansa ya rintse, lokaci daya kuma ya bude a dan zafafe ya ce" Ta shaida maki haka? Kuma kika yi shiru baki ce min komai ba?, Bayanshi me da me take yi maki? Idan tana nuna maki soyayya a gabana du ba haka bane a bayan idannuwana ko?, A kan me zaki boye min? Me yasa?" Dan matsawa ta yi, dan irin yadda yake maganar a zafafe har ya fara dan daga murya, alamu na ransa a kololuwar bace yake ya bayana a tatare da shi Hankali tashe ta duka kasa kanta a kasa, hannayenta a jimke tana girgiza kai kuka na fitowa daga bakinta ta ce" Abah, ta yaya zan sanar maka cewa , Matar da Mahaifiyarmu ta yi mana nuni da mu kirayeta UMMA dan ta isa ba dan mun hada dangi da ita ba sai dan tsabar yarda da kaunar da take tsakaninta da mu baki daya cewa ta rikide ta koma aljana a gabana, tana zalintata , ta tsoratar da ni da kalamai masu muni a ranar da ta nuna min zata so aikata sabo mafi muni da ni, sabon da take aikatawa da wasu matan, na bijire na nuna ta rufa min asiri ko me take so na zama zan zama in dai zata rabani da wannan maganar, ta ju haushina a kan haka, ta kara kaimin yaki da ni da farin cikina, ta hanyar nunawa duniya mahaukaciya na zama sakamakon mutuwar mahaifana dan ina jahila wace bata da tawakali?, Take muzanta min ba dare ba rana , ta sakani zamtowa mahaukaciyar domin tsananin tsoronta da nake ji ya da ko maganarta aka dauko nake rikicewa, bayan ba za'a iya yin hira ba maganarta ba a cikin gidanmu, a cikin fada ana mutuntata dan ana mata kallon Uwa a garemu, a gabanka kana mutuntata dan kana yi mata kallon Uwa a wajenmu, Abah a yadda take da tasiri a rayuwarka ta yaya zan maka da maganar nan ka gane me nake nufi, bayan a cikin tsoratarwarta ta min nuni cewa idan har na yarda na sanar maka maganar nan ta yi alkawarin zata dora min shari mafi muni a rayuwa, sharin da kai da kanka zaka jefeni a matsayina na matar aure idan na aikata domin kana zartar da hukunci ne bisa koyarwar adinin musulunci, sannan ka dawo bakin ciki ya kasheka?, Wannan matar ce zan iya kokowa da ita Abahnah........." Da zafin rai, har hannayensa na bari ya katseta ta hanyar tafka mata tsawar da ta saka su dake ciki kamewa waje daya sunna kallon junna Muryarsa da fada fada ya ce" Kina nufin a cikin kazantaciyar rayuwar da take yi har ke ta so yi da ke? Kina nufin tsoratarwar da ta yi maki harda ta zata iya yi maki sharin Madigo?" Auta da ta hade kanta da gwuiwoyinta tana sheka kuka hankalinta tashe ta gaza furta koda A ne, domin zata iya rantsewa rabonta da ta ga bacin ransa haka tunda aka ce masa ta haukace, zai kwaso bacin ransa sosai ama fa zai yi kokarin boyewa a gabanta dan bata iya jurewa yanzu ne zata rikice masa da koke koke, sai gashi yau ya rikide mata tamkar ba shi ba , tamkar wanda zai iya zaneta idan ta yi wasa, sai hankalinta ya yi kololuwar tashi ta rasa yaya zata yi masa Zuciyarsa da ciwo, hankalinsa tashe, kirjinsa na tafarfasa yake kallonta, har Inna Hindu ta gaza jurewa dan ta gama fahimtar Auta kuma ta tsorata fa ba zata iya kare kanta ba, bayan yau din rana ce da ya dace ta kare kan nata, a dole ta fito da zumbulelen hijabinta har yana jan kasa domin Hijabin NADIRAH ne ta dauka dan a dakin Nadirar suke Tana zuwa jiki a sabule ta duka daf da Auta, hannayenta ta saka ta dago Auta ta rungumota jikinta , sannan ta sada kanta sosai, muryarta ba nauyi, a sanyaye sosai , kanta a kasa ta ce" Allah ya huci zuciyarka, ka yi hakuri ka yafe mata, ka gafarta mata ka yi mata uzuri, dole sai a hankali koda zata dawo yadfa kake so, ka tuna fa babu abinda ke saurin zama gaske irin yin abu da gangan, ko ciwo ka dorawa kanka da gangan yana iya rikide maka ya zama gaske, , Matar nan ta fi kowa kusanci da ita, rana tsaka ta wayi gari take haduwa da ainahin fuskarta, ta kuma fi kowa sannin ta inda zata biyo ta daureta gaba da baya, Auta kuma yarinya ce, a duniyarta kuwa ku hudu kawai ta sani, sai mijinta da yake bako a gareta, da wahala ta iya gane rayuwa ko ta gane cewar idan ta sanar maka kana da girma da hankalin da ba zaka tashi ka warware maganar kai tsaye ta yadda matar nan zata fahimta har ta yi mata sharin ba, ba zata iya gane cewar Allah ya azurtaka da ilimi irin na sarakuna, wanda yake banban da wasu kwakwaluwar, a dole idan abu ne aka fada maka zaka saurara ne na farko, zaka kuma yi duba irin naka ba wai na mai fadin ba, ka yafewa kanwarka domin a dole ta tsorata da makircin matar cen, idan kuwa ta kula ka jefe AUTA lalle kai kuma zuciyarka zata buga, kennan an bar talakawa a hannun su wa?, A irin wulakantar da Auta da ta yi sai da ta rabata da kowa, babu kawaye bale miji ko danginsa, uwa uba ta fitar da fuskarta a matsayin mahaukaciya, dan Allah ka fuskanci baiwar Allahn nan da ta zubar da komai ta hakura take yaki dan gannin ka take makiya, take kaiwa Allah kukanta ba dare ba rana har yanzu adu'arta ta karbu ta ga wannan ranar itama da ranta da lafiyarta, Ka yi hakuri dan Allah na shigo hurumin da ba nawa ba, ba dan na isa ba, ba kuma dab matsayina ya kai ba, ......ama Auta a nan muke zaune da ita, ta bude bakinta ta sanar min abubuwa da yawa wa'inda suka sakani kuka du irin kwamacala tamu ta kauye sai da lamarin rayuwarta ya gigitani...........idan a yau ka kasa fahimtarta ka karra rufeta ne a cikin hali na kaka naka yi, bayan kaine ABAHNTA......" Inna aka kare hawaye na bin kumata, sannan ta mike jiki ba karfi ta karra neman afuwarsa ta fice gaba daya a falon dan ji take yi idan ta zauna tana iya rushewa da kukan da za'a dawo bata hakurin itama, gwara ta he cen wajen bayi ta karra cakudewa da su ta yadda zata idasa nununa munafukan cikinsu wa y'arta saboda rayuwa ta yau da gobe da ta kama y'ar tata a gidan, dan kuwa babu gidan ubanda INDI zata je da cikin dan masu gida, ai it yanzu kuma tashin hankali ya kau, Auntynta da rai tana hannu mai kyau, sai shagali yanzu zata sake fuskantar karamar arniyar cen Sosai jikinsa ya karra yin sanyi, hankalinsa kuma ya karra tashi A birkice ya dawo kasa inda Auta ke dukunkunne bata daina kukanta ba, haka da Inna zata fita yana gannin yadda ta yi kamar zata bita, kennan tsoronsa ta ji da ya yi mata ihu? Shi kuwa ya yi ne a rashin control din kansa, a ganninsa ta yi wasa da shi ta yadda take tunanin zata kawo magana mai girma irin wannan ya wani banzatar da ita ta zauna shekara da shekaru tana shan wahalar arniya banza da wofi! A hankali ya dagota ya matsota gefensa kamar yadda yake yi mata a dama idan tana hali na rikicewa, A sanyaye yake taping din bayanta yana dan riko hannunta dake jimke a cikin nasa Muryarsa a raunane, hankalinsa du a tashe ya ce" Ki yi shiru haka Uman Abahnmu, haba Mariya mai baban daki, haba matar Lamido , dubi nan, dubi ban fa yi fushi ba dan wanu abu sai dan jin ciwo a zuciyata, Auta ina gefenki, ina tare da ke ba dare ba rana ina fita da isa da takama na je garin wanda na ga dama na kwato yancin wanda aka cutar na dawo kasata na kuma ja layi na tsaya na zartar da hukunci a zauna lafiya ama na gaza gannin hali na ukuba da aka saka min kanwata?...........kin san me haka ke nufi a wajena?, Auta na yi karatun rayuwa tunda na hau karagar mulki, abinda yake karkashin tunanina ni da kaina na san wani lamari ne na ubangiji, mutun kuwa na yi masa karatun da yake da nisan gaske, na riga na san cewa babu abinda ke gagawar juyar da kwakwaluwar dan Adam irin abu ukun nan *ARZIKI, MULKI, MACE*, a kansu dan Adam na iya mance kansa da asalinsa, a kan neman duniya da abinda yake cikinta dan Adam na iya mantawa ba matabaciya
Chapter 86 · 0% Book details