← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 87

Sashe 74

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

fa ishe shi fa yawan maganar ya sakata mikewa ta yi masa salama ta tafi Bayan ta tafi maganin Auta dake hannunsa ya cusa a cikin aljihun jalabiyarsa, sannan ya cire alkyabar gaba daya a hankali ya ci gaba da jan carbinsa yana neman sauki a wajen ubangijinsa har sansanyan barci ya dauke shi a nan saman kujerar, domin kafafuwansa kawai ya hauda sama ya shiga hutawa __________________________________ A ranar UMMA bata kula kiran da aka yi ta yi mata ba, a tunaninta so syke su ji ko an saka masa maganin a abincin, har sai da wata safiyar ta waye, da sanyin safiya ta daga kiran da abin barci a idannuwanta domin ko salllar asubah bata yi ba, yawancin lokutama idan ta tashi ta ga rana ta yi bata yi kwata kwata gaskiya Muryarta a ciki ciki ta ce" Wai dan Allah ku idan kuka so abu kamar Da ya so fita daga cikin uwarsa ne? Haba dan Allah ban saka maganin ba a gaba fa, ama sai wani kirana kuke yi ba dare ba rana ?" "Ke dan Allah ki min shiru da banzan maganarki, ke har kin san yadda da yake yi idan ya so fita daga cikin uwarsa ke da baki taba haihuwa ba sai na kashi?, Ba maganar magani ake son yi maki ba, so muke mu sanar maki abinda ya faru da iyayen yarinyar nan, an neme su an rasa yau safia ta biyu kennan wai sun yi fada da wani mutun, mu muna nan cikin tashin hankalin abin ke kina cen kuna hauka!" Muryar mahaifiyar Bahija a zafafe ta fada har tana huci da takaicin Umma Gaba daya Umma ta rigijo daga saman gadonta lokaci daya kuma jikinta ya dauki mahaulacin bari gab gab gab , haka kuma kafafuwanta suka dauki mijirya A rikice ta ce" wani irin an neme su an rasa, gidan uban wa suka shiga yo? Ina masu tsaron nasu?" "Gidan ubanda kika aikesu!, Fada ya yi da wani mutun mai kama da yan ta'ada, a yadda yan anguwa suka ce mutumen ya masa alkawarin batar da shi da danginsa, maganar da nake maki harta BAHIJA sai da ta wuni a summe bale masu gadinsu, sai da likitoci suka wuni a kansu baki dayansu sannan suka dawo hayacinsu!, Ki gagauta bincikar yarinyar nan dan ni abin nan na kasa amincewa da shi, gashi kina nan kinaa shirme kin ki maida hankali a kan dan aikin da aka baki ba wani ba, ni kam babu abinda zai mayar min da aiki baya na fada maki, wayar uwar ke hannuna sai kira yar uwar tata take yi, ki je ki sanar masu gaskiyar lamari cewa an sace yan uwansu mu babu hannayenmu a ciki, kuma su mayar da hankali su mana aikinmu ko suma da suka rage mu kuma mu salwantar da rayukansu!" Ta sake fada a kausashe Wata ashariya UMMA ta lailayo ta lailaya mata a haulace ta ce" Ke ama mahaukaciya ce !" "Kece mahaukaciyar daba da baki san abinda kike yi ba!" Ta rama itama rai bace, hakan ya saka Umma mikewa tana rarumar tufafi domin zannin kansa watsewa ya yi tsabar firgicewa da kidimewa Zata yi magana Muryar sarkin tanus ta dauke tata muryar, cikin hali naa bacin rai da daguwar hankali ya ce" Salam
Chapter 74 · 0% Book details