← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 87

Sashe 30

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

biyu bata ga umanta ba! Mahaifinta kuwa yana fama bawon Allah, idan yana tare da ita kowani lokaci ana iya tashinsa dan aikin uban gidansa!, Ashe duka wannan bautar bata isa ta basu daraja ba? A banzan dai suke? Shine za'a tura yarsu yin kisa? Ita babu ruwanta da wani wai shi ANNEMOKAL ITIFAL!, abinda yake gabanta yaki da azaluman nan, dama ta rayu cikin farin ciki dan su zo tashi daya su wargaza? Lalle sun siya da kudinsu da suka saka Innar birni, Aban birni, da innarta kuka ris ris, ita kuma suka sakata summa! Maganar innarta ne, ba maganar soyaya bace, idan kuma taa gama aikin zai salameta! Wannan tunani ya kai hankalinta saman dardumar dake shinfide, a lokacin har asuba ta fara sanyo kai domin karfe hudun dare ta yi Jiki a sanyaye, kwonya cike da tunanin abinda yske kamar film ta shiga gabatar da sallalinta tana fatan wanda ya san inda ciwonta yake ya warkar mata, ........... Tabas BATA FARA DAN TA DAINA BA!, Aminu kuma yana nan daram a zuciyarta ba wai ya gogu ba, sai dai tana tunanin biyayar da zai yiwa innarsa itama zata kamaanta yiwa nata innar , sai dai shi ya fita cin riba, tunda shi aure zai raya, ita kuma CETON RAI za'a turata! Yanzu za'a fara *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 2 Kusan haka suka kwana, kowa na kaiwa Allah kukansa da neman sauki a wajensa Kamar yadda aka saba daukanta da duku duku hakan ce yauma, sai dai yau abinda ya sakata jin zuciyarta zata tarwatse Abanta kadai ne ke tsaye har aka karasa da ita dakin gyaran, bayan a da innarta na gefe, innar Birni na kai kawo abinta Kai ta gyadawa Abanta dake yi mata magana kasa kasa cewar ta yi kokari ta samu barci domin idannuwanta sun kumbura hulu hulu, hakama kumatunta Da ido ta raka shi, sannan ta gyara zamanta jiki a sanyaye tana jira ta ji an fara yi mata abinda aka saba Abanta na fita ya rasa ina zai nufa, shi kam tunda yake bai taba gannin yayar da kanwar sun yi fushi irin haka ba, Jiki ba karfi ya nufi ciki da niyar nufar dakin Inmar birni, sai ya tsinkayo maganarsu a kicin A hankali ya karasa ya dan labe yana sauraronsu, a tunaninsa har yanzu a cikin fushin suke tunda har ya ga babu wace ta damu da lekawa gannin an kai yarsa wajen gyara da sauransu "Aunty, aa, kar ki cire idon zakaran nan, sakashi walahi" Hindu ta fada da sauri tana tarewa ta saka shi a cikin dahuwar da suke yi FADIME ta dafe gaban goshi ta kai zaune tana fadin" Kin fi karfina Hindu, wannan dahuwar zaki ba yar taki? Walahi zaki sakata a uku bayan kin san komai" "Ni babu abinda na sani, hasalima babu abinda muka sani mu dukanmu aunty, ina kankanar mai yusufan? Gaskiya zuwa zan yi na kai mata tun jiya rabona da ita fa" Hindu ta fada tana turo baki FADIME ta yi yar dariya tana tafa hannu ta ce" Kin manta mun saka jaka goma goma, walahi idan kika je sai kin bani kudina, dan Allah ki barta mu gani ko ta yi hankali mana!, Haba kema, ke kin ce in na je wajen mijina kin ci jika goma, ni kuma in kika je wajen yarki na ci jaka goma, ehe" Yar dariya ce ta subuce masa har yana kama baki, kai kai kai, matan nan ba zasu taba girma ba idan sunna tare, watau haka aka dora dan a kuntata masa shi da y'arsa ko? Wani sukuni ya ji a cen kasan zuciyarsa, na ganewa da ya yi ba fushi mai sunna fushi suke yi da su ba, summa sunna ransu Juyawa ya yi ya nufi ciki zuciyarsa cike da dana sannin ihun da ya yiwa matarsa a kan abinda ta fi shi gaskiya,, ama in sha Allah zai bata hakuri, domin rayuwarsu da suka gina bisa aminci ne ba bisa fin karfi ba da zalunci irin na wasu mazan Abincin kari HINDU na mikawa masu mata gyara ta juyo ta komo suka ci gaba fa lamuransu ita da y'ar uwarta, hakan ya karra sakawa NADIRAH ciwon kai da zafin jiki mai zafin gaske, har ya zamto a yau gyaran safe kadai suka yi mata suka rakota da nufin ta koma ta huta , domin kana ganninta zaka gane bata yi barci ba , idannuwanta sun nuna Jiki a sanyaye ta idasa shiga falon da salama a bakinta, a lokacin HINDU na tsintar Zogalen da ta sa aka kawo mata danya sabuwa fill zata yi mata hadin tumaturi da kwai , shima gyara ne na musaman Muryarta bata fita da kyau ta sake yin salama sannan ta idasa shigowa jikinta ba karfi tana baza idannuwanta dan gannin Innarta ce kadai ko harda Innar birni? Gannin bata ga innar birni ba ya sakata sakin shagwabar da ta saka innarta zuba mata ido tana kallonta Raurau ta yi, nan da nan sai ga hawaye kamar an kunna pampo yana zuba ba kakautawa , sannan tana tsaye tana kallon Innarta, watau jira take yi sai ta fara zuwa inda take domin ai a ganninta itace ua dace su lalaba ba a ringa neman kasheta ba ko? Innarta ta kalli yayarta, ta kuma kallon NADIRAH Gefe ta matsar da zogalen tana mikewa ta ce" Wayo Allahna jaririyata, zo zo zo nan zo, wayo haka kawai saboda abin duniya na ki nemanki tun safe, zo, aunty zan biyaki kudinki bari mu yi waya da sarki!" Dariya ce ta kubucewa Fadime ta kirki, dan walahi har fruits din da tale yankawa ta ajiye tana rike ciki Dama ta san ba zata taba iya wuni bata nemo y'ar ba, ko a yanzu ta cikata da hirar Nadirar, uwa uba wai sarki, in Hindu ta takarkare tana labarin mijinta in bako ne kai sai ka duka ka gaisheta dan zaka yi tunanin sarkin garin gaba daya take nufi, koda yake, sarkin yake, sarki ne a rayuwarya, mutun tsayaye a kan lamarin iyalinsa, rashin karfinsa bai sakashi rayuwa a matse da iyalinsa ba, yana yin iya yinsa dan su rayu cikin farin ciki, ya daure mata kugu ita kuwa sai shagalinta take ita da y'arta Kuka NADIRAH ta barke da shi tana shigewa kirjin HINDU ta ce" Innata, fushi kike yi da ni? Innata shine ko ki leko ni?" A hankali ta dagotatana sake taba jikinta ta ce" Indi baki da lafiya ne? Kin ji jikinki kuwa?" NADIRAH ta mayar da kanta ta dora tana sake rintse idannuwanta ta ce " Innata, ki cema innar birni dan Allah ta yafe min kin ji? Ki ce mata ba zan bijire mata ba, ki ce mata ko me take so zan yi kin ji? Ta daina saurin yin kuka idan na bata mata kar aje na zama yar iska kin ji innata?" A hankali FADIME ta tsagaita dariyar da dama ba wai tun karfi bane ta daki murya take kyakyatawa tana kallonta A sanyaye ta dan kawar da kanta, daga garesu kirjinta na wani itin dokawa fat fat fat na tsagwaron kaunar gudan jinninta Bata shirya ba ta juyo da dubanta sanadiyar jin hannun NADIRAH a saman cinyarta ta rike a hankali ta ce" Innar Abana, ki yi hakuri kin ji? Ki yi hakuri innar Abana, tunda har Innata tace auren nan ba maganar soyaya bace, ceto ne, kuma idan komai ya wuce yana iya sawake min bayan ya gode min, Innata ba sai na zo na samu Aminun ba mu yi abinda ya dace?" FADIME ta zubawa fuskar Yarinyarta ido, a hankali ta ringa hangen tsagwaron yarinta a tare da yarinyar bayan ta daurari furucinta A hankali ta janyota jikinta ta rungumeta da runguma mai zafin nan, ya zamto kanta a saman kirjinta tana shafa bayanta kanshin turatenta gaba daya ya gogu a jikinsu kamar sunne suka shafa turaren, A hankali Innar birni ta ce" Allah ya yi miki albarka, Allah ya baki ikon cin galaba a kan makiya, in sha Allah daga yanzu da kika san komai zamu dawo ne munna gabatar da shirinmu bayan sun gams nasu, kafin nan mu tafi ki kwonta ki yi barci kin ji yar gidan innarta?" Wata irin ajiyar zuciya take karra saukewa tana jin wani dumi special daga kirjin mahaifiyarta marar cutarwa yana ratsa fuskarta, haka kuma murmushin mahaifiyar tata idan ta dago kai sai ta ji dama ya tsaya haka ta yi ta kallonsa kar ya katse Ajiyar zuciya, hadi da lalausan murmushi HINDU ta yi tana jin wani irin farin ciki na ratsa mata zuciyarta ta dubi FADIME dake dubanta niyarta ta kai NADIRAH ta kwontar da ita A hankali ta sakar mata murmushi tana girgiza kanta ta ce" Aunty ni da zan yi wancen, kaita dakinki dan Allah ta huta , na tabata bata yi barci ba, Indin innarta sai kin farka zan baki wani labari mai dadi kin ji?" NADIRAH ta gyada kai tana biye da mahaifiyarta nesa nesa kadan tana jin banbarakwai , domin bata saba haka ba sam Sunna shiga ta tsaya tana kallon maman nata dake gyara mata shinfidar Bayan mamanta ta gama ta juyo tana kallonta Wani murmushin ta sakar mata mai sanyi ta ce" Indi zo ki kwonta mana?, Cire wannan rufar ki kwonta ama banda safar , bara na gani cikin maganin Abanki ko akoy na zazabi na baki........" Motsin da ta ji a bayanta, kusa da bayi ya sakata juyowa da sauri Gannin mijinta ya sakata dan sada kai hadi da murza goshinta kamar wace kunya ta rufe din nan, sai kuma ta ce" Dama, dama innarta tace na shinfideta a wajena, kuma, kuma sai na ji kamar jikinta akoy zafi, shine nace bara na bata magani......" Murmushi ya saki yana kallonta, shi dama ya san harfa kunyar kar ta ja y'ar a jiki ace tana nunawa yar fari so yake sakata aikata wasu abubuwan Zagayawa ya yi yana sake dubanta ya ce" To ke da dakinki, magungunnan mijinki, da kuma yar hindunki sai kin fada min, kin ga ni na tafi masalaci a cen kuma zan
Chapter 30 · 0% Book details