← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 87

Sashe 49

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dake kallonta, ji ta yi kamar ta bude bakinta ta koya mata dukawa da bayar da hakuri, ji take yi kamar ta girgizata tace mata hakuri ake bayarwa gaba daya cikinta har wani kuuuuu yake neman yi gannin Bahija ta ki cewa uffan bayan yayanta na magana yana kuma son amsa ne Kakausun idannuwansa ya lumshe, yana danne zuciyarsa dake tunzura da sake gannin tsantsar rashin kunya a tare da ita Dubansa ya maida kan Auta, ya fitar da hannunsa mai dauke da birda birdan jijiyoyi masu girma da nuna halitar girma ya ce" Bana son abinda zai taba min ita, haka kuma bana son abinda zai taba min matata, ki kula kin ji......, Yayama sunnanki?" Auta dake wuwulga idannuwa ne ta budi baki a hankali ta ce" Abah, dan Allah ka yi hakuri ka ji? Sunnanta BAHIJA" Kakausan kallon da ya wurga mata ya sakata sada kanta sosai tana sauke ajiyar zuciya Bai ce komai ba ya mike ya nufi falonsa ya zauna cike da wani irin tukuki shima na haushin Yar, wannan yarinya ai yanaga da ya samu haihuwa da ya nasota duniya, ama dan iya wulakanci da girmansa, da darajarsa ya ringa magana kamar zai ari baki tana kallonsa ba amsa? Zai yi maganinta ne, abu daya ya hannashi babalata maganar CHEIK walahi! Bayan tafiyarsa, NADIRAH dake kallon Auta a hankali ta ce" Ya tafi fa, ki dago kanki" Da sauri ta dago tana kallon NADIRAH, sai kuma ta rafka tagumi ta ce" Yaya na magana bakya bashi amsa?, Innalilahi aunty Bahija bakya tsoronsa?" Maimakun NADIRAH ta bata amsar nan sai ta kafeta da ido, a hankali ta ce" Tun yaushe yake maki kallon mahaulaciya, me yasa kila yarda ake maki kallon wace bata da hankali?" A zabure Auta ta sake kafeta da ido, wannan karron har hannunta na rawa sanadiyar bugawar da zuciyarta ta yi, tana kallon NADIRAH, NADIRAH na kallonta Muryarta na rawa ta ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 3 Muryarta na rawa ta ce" Yaya aka yi kika gane lafiyata kalau?" NADIRAH ta yi shiru tana kallonta, bata san me zata ce mata ba, bata san ta inda zata fara ce mata komai din ba Ajiyar zuciya ta sauke tana dan kawar da dubanta daga inda suke ta hango falo, a zaune yake yana operat din computer , hankalinsa baya kansu kwata kwata A nutse ta karra fuskantar Auta , wannan karronma ta ki bata amsar tambayarta ta dubeta ido cikin ido ta ce" Idan shekaru suka fara ja, ko ba'a yi maka aure ba, ko iyayenka da rai, zaka zamto nama a gaban mahauta, idan na ce maka mahauta ina nufin du wani wanda numfashin da kake shaka a duniya ne ya zamto masa abin jin haushi da tsana a rayuwa, shekarun da suka hau kanka, ko nisa da iyayenka zai zamto ne ana wawurarka ba ji ba gani, idan har ka zama komai ka labe ko ka saki kuka yagalgalalen nama kake wanda kowani wawa zai wawura ya ce zai iya siya ya ci, ban ce maki wane ne makiyinki ba, ban kuma san kowa a cikin masu sonki da bataciyar rayuwa ba, ban san me kika rayu a cikinsa ba, ban san me kike rayuwa a cikinsa, ban san girman tsoron da kike yiwa koma menene ba, ban kuma san me yasa kike tsoron abin har haka ba, abinda na sani shine, babu bawan da ya isa ya tsalakewa kadararsa, kuma babu bawan da ya isa ya ja da hukuncin ubangiji, ka rayu kawai ba dan ka birge wani ba, ka kuma tuna da mutuwa da tsayuwa a gaban ubangijinka, wasa kike yi da sallah? Ke din mutun ce mai shagwabar da kika kasa jajircewa rayuwarki, ko me ya mayar da ke abinda ake dubanku kina da damar kaucewa, rashin sannin mafaraucinka shine matsala, idan har ka sani wayance masa zai fi komai zama abu mai sauki, kin ga ba fa fito na fito ake yiwa kowani mafarauci ba, dan wanin mashinsa ta fi karfin ya harba bai samu nama ba, ama ana iya yin wayo a gudu, harma a kama shi a cikin tarkonsa.........., Babu abinda na sani, ba kuma na son sani, a ganina bai cencenci ki ci gaba da rayuwa kamar wata yar tatata ba, ki yi aiki da iliminki dan tsira da mutincinki!" Daga hala NADIRAH ta muke ta shiga tatare kwanonin nan tana nufar hanyar da ta tabata ko yayane a nan zata samu kicin Ai kuwa a nan din ta samu kicin din da ta zama kamar mahaukaciya wajen kallo, domin kafin ta fito sai da ta sha kallo har kamar zata kwana a wajen Kayan ta ringa kwashewa tana kaiwa, sauran madarar da ba'a sha ba kuwa ta tsiyaye a kofi ta sake kafa kai ta aikata sannan ta kai kofin ciki ta fito ta nufi falo hankali kwonce dan tafia A zabure Auta ta mike daga zaunen da take, kamar an tasheta a barci ta biyo bayanta da sauri tana fadin" Aunty, Aunty, Aunty BAHIJA " Har ga Allah bata tsaya ba dan ba sunnanta bane BAHIJA sam bata gane da ita take ba sai da ta karasa ta ciro alkyabarta ta ankara itace BAHIJA fa, hakan ya sa ta juyo tana murmushi ta ce" Ni ba zakina ce min Mama ba?" Rubutun da yake yi a computer ya dan dakatar , tunda Auta ke kwala kiran nan ya bisu da kallo har furucinta da ya saka shi jin kamar ta gaura masa mari, Mamah?, Sai ya samu kansa da dagowa ya dan zuba masu ido, zai iya rantsewa Auta ta girmi wannan abar, ama ta dubi idannuwanta tace ta ce mata Mama? To a kan mema? Itama Autar abinda ke ranta ta dan kawar tana dubanta ta ce" Mamah?, To ke ba auntyna bace?" NADIRAH ta rage murya tana dage girarta daya tak, dayar kuwa ta yi kasa da ita ta ce" yo mana, matar Abah ba mama bace?" Auta ta saka hannunta ta rufe bakinta tana yar dariyar da ta saka yayanta kureta da ido, Sai kuma ya saukar da dubansa kan hannayensu, a lokacin da NADIRAH ta saka Alkyabar ta ja hannunta ta ce" Mu je " Maimakun ya ga Auta ta kiya, kamar yadda take yi a lokuta da dama idan yace ta je Umma ta rakata, ko yace ta je HUZNAH ta rakata, sai ya ga ta yarda a bakuwar fuska, ko dan ta ji ance har uwarsu ce zata saki jiki da ita?, Subahanalah idan haka ne kuwa ya zama wajibi ya dauki mataki da wuri wuri, domin ba zai yarda ta saki jiki da matar da ba ita bs, ajema zuwa ta yi ta cutar da ita a banza a wofi, gashi Auta ba lafiyar kirki ba ta yarda da ita a banza da wofi Yana ji yana gani suka fita, hannayensu rike da junna, bai hanna ba, bai yi ihun da yake ji yana son masu ba, ya kame girmansa ne dan kar ya cika hayaniya a gaban yarinyar ta raina shi, rainin da ta yi masa a yanzuma ya isa, ama in sha Allah a gobe zai yi kiranta daga shi sai ita ya ja mata kashedin da zata fahimta, ko da me ta zo ya fita iyawa, ya sarara mata ne dan ance ya saurara, da ba dan shi ba ta yiwu da yanzu tana kurkukun azalumai! ___________________________________ "Ta yaya zan iya ganar da yayana ni ba mahaukaciya bace?, Dan Allah ki fada min?" Auta ta fada a lokacin da suka karasa bangarenta NADIRAH dake bin falon da kallo, bai cika hayaniya ba, haka kuma da dan kwaliya irin na yara anana, kayan dakin dai gasunnan dai, tarkace sai hamdallah Kallonta ta yi da mamaki ta ce" Haka kike son dakinki ya kasance ne?" Auta ta bi dakin da kallo, kai ta girgiza ta ce" Umma ce ke sonshi haka, wai tace tunda baki da hankali a zuba min abubuwam yara zan fi sakewa, kuma du ta cire hotunan iyayenmu tace a boye kar su ringa rikitani" NADIRAH ta gyada kai, zuciyarta cike da mamakin matar da makircinta Kasa kasa ta ce" Ki duba ki gani, kina iya sakawa a cenza maki kayan, a hankali kuma sai ki san ta yadda zaki biyowa yayanki, dan ni ba sanninsa na yi ba ai kin gani, ama abinda zaki fara yi shine daina hadiye maganin nan, idan an baki, ko waye ya baki, ki makale shi a kasan harshenki ki sha ruwan ki faki ido ki cire, ai kin fahimta ko? Kuma gaskiya ki daina irin kallon na kamar mai farfadiya inaga harda shi da kike yiwa yayanki ya yarda kin tabu" Murmushi ya subucewa Auta, domin a yadda Nadirah ta fada din abin murmushin ne A hankali ta zauna ta ce" Dan Allah ki kwana a nan kin ji?" Ido NADIRAH ta zarro, sai kuma ta girgiza kai ta ce" Innata na jirana, kun ga, sai da safe" Daga haka ta fice, tana fitowa sarai ta hangi mace ta yi saurin bada baya, irin daga tsaye da take tana hangen bangaren AUTA ta juyar da bayanta Baki ta tabe ta yi gaba, itama ta yi kamar bata gane komai ba ta nufi bangarenta, a zuciyarta tana cike da tunanin wata jarabar na cen tana jiranta Ajiyar zuciya ta sauke har ga Allah wani lokacin tana jin kamar tsoro na son kamata , sai dai kuma in ta ga zalunci karrara sai ta ji bata tsoron uban kowa! A hankali ta bude bangaren nata bayan ta yi salama tana sake kallon dogaran dake gadin bangaren nata, A yanzuma, ko idasa rataye Alkyabarta bata yi ba, ihun maganar matar da ta tabata dama tana jiranta, da tasowarta a hargitse da nufin maimaita haukan da dakikin kanta ke bata cewar zata ci gabaa da cin bilis ya sakata juyowa a zabure, a lokacin ne kuma Innarta ta fara saka hannunta bayan ta sha gabanta ta tare marin da ta yi niyar sake kwada mata Da sauri NADIRAH ta zagayo ta tare hannun Umma da ta so sauke wani marin a fuskar Innarta
Chapter 49 · 0% Book details