← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 87

Sashe 22

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace ta zauna ta jiyo masu, kuma gashi ita ta ji ama ta hannata labewa ta jin itama Komawa hindu ta yi tana sake zuba masu ido Gannin da gaske kukan mijin yayarta ya yi shima sai ta nemi rikice masu, ta yi zaman yan bori tana dabar kai ta fashe da kuka ta ce" Wayo mun shiga uku,wani abu ba ka yi za'a yanke maka kai? Ko aunty ke kika yi wani abin? Ku tashi mu gudu idan laifi kuka yi ba zan rasa wajen boyeku ba babu wanda zai same ku,wayo ni Hindu kunne uwata, kunne ubana me ya aikeku aikatawa sarki bafan UMUGHLUK ITIFAL laifi? Kun sakani a uku ni da yar marainiyata? Innalilahi wa inna ilaihi rajune mun shiga uku!" A hankali Fadime ta kalli mijinta a sanyaye ta ce " ka tabata wannan hirar ta ayi ce da Hindu?" Shima idon ya kura mata yana kallo, bama irin yadda take turbuna kaffafuwanta a cikin kasa ba ta yarda dan jonanen dan kwalin kan nata a kasa kamar kace fit ta fice a dubu kota yi ciki da kai Ajiyar zuciya ya sauke ya sake rike hannun matarsa a hankali ya ce" Hindu ki nutsu mana, babu fa abinda muka yi" Hindu ta dakatar da kukan tana sake kallonsa ta ce" Kuma kake kuka? Yaya me zai zo maka da karfi ya shirgaka a kas fisabililahi? Aunty hala kukan amare ya yi? Wayo ni wayo kaina ni Hindatun Habu makadi!" FADIME ta gyara zamanta tana jan hancinta ta ce" Ka daina batawa kanka lokaci, babu abinda bata ji ba, ka je kanka tsaye kawai Abanta" Da mamaki ya zubawa Hindu ido ya ga sai micui micui take da ido da baki ta kalle shi, ta kalli FADIME Kai ya gyada yana sauke ajiyar zuciya ya ce" Yaya kike gani , me ya dace mu tsayar? Mun rasa ina muka dosa" Sai da ta yi murmushi ta gyara zamanta kamar ba ita ke share sharen hawaye ba ta dube shi ta ce" Matsalar da ta dan sage min gwuiwa har na koka din nan daya ce kwalin kwal, yaya shi zakin sarakan da bashida anfani?" Sai da suka zabura sunna kallonta su dukansu Harshen zaninta ta saka ta sake share hawaye ta ce" Na tabata sihiri ne bawan Allah na san ba uwa ba uba ba dangi masu jin kai, ama ba komai idan muka je in sha Allahu zan ringa dan bada taimako na karya tambaya da tashin tsakiyar dare ina kama sunnansa ina li'ilafikuraishi, in sha Allahu zai dawo mai anfani, in kuwa abu ya gagara sawayenmu a likafa zan nado yata mu yi LABA, tunda ai du dadin riga bata yi ya wuyan hannu ba" Da takaici Fadime ta ce" Dan Allah ki saurara da magana rututun nan haka, ke kinma gane me ake nufi ne?, Haba dan Allah Hindu me zai saka a yanzu da hankalina ke tashe ki karra tayar min har na fara tunanin ko kin haukace ne?" Hindu ta dubeta ta ce" Ni kuwa nake da hankali, ras nake tunda ni a bayane nake gannin wasan!, Bari ki ji, idan kuka kiya da maganar nan ku tabatar cewa lalle zasu batar da mu din, domin kuwa har Habu da ya auri Hindu kanwar Fadime sai an halaka da makotan Hindu bale wata hindu kayan banza da yar yata da bata taka kara ta karya ba, a cen kauyenma neman inda zan gudu da ita nake yi dan Innar Aminu ta tsaneta Aminu kuwa ya yi mata asiri shege wuya uwa marikin lema!, Na takaice maki ta kife ko ta walare ni inada amsa wa UMUGHLUK ITIFAL, zan rusa na makoki ne na fada masa cewa wuka aka dora a wuyanmu cewa ko mu aminta da auren nan ko a karmu kuma ba za'a daina neman wace zata je ta karshi ba, muka ga mu masoyansa ne gwara mu shigo daga ciki, shi Habu sai a san yadda aka yi a mayar da shi makadain babar masarauta sai a bamu bukarmu mu rabe, a haka sai a raraka kafin Allah ya bamu Sa'a a kansu, domin kin ganni nan sai inda karfina ya karre walahi, numa fa yar gani a kasheni ce a kan Zakin sarakai, aure mun yarda ba sai an kashemu ba!" Ikon Allah wanda ba'a saka masa rana, kallonta kawai suke yi, yadda take magana da karfinta gaba dayansu gani suke yi bara san irin abinda tske neman saka kanta da ita da yar tata ba Jiki a sanyaye ya ce" Da ke za'a tafi gidan na yarki?" Fadime ta yi dan tsaki tana dafe gaban goshinta dan takaicin HINDU ba zai taba kasheta ba walahi! HINDU ta yi wani murmushi watsar tana kallonsa ta ce" To kai zaka rakata yaya? Ka san dai ba za'a je da kai ba, ka bari idan muka sayi gida sai ka kauro ko?" "Innalilahi wa inna ilaihi rajune, abanta dan Allah ka tashi ka nemi wanda zaku yi shawara, idan kuwa bari zaka yi sai dare ya yi ka fitar da mu mu samu mu gudu to, ka daina magana da Hindu, hindu fa tunaninta daban da na mutanen kirki!" Fafime ta fada tana neman fashewa da kuka, ita kuwa Hindu ta tabe baki tana gyara zamanta , ita gani take auntun tata ce sam bata gannin me take nufi, ai walahi ko ana ruwan muzuru ba zata yarda a tafi da yar nan ita kadai cikin mayu ba!, Ina, ai tass za'a je da ita, basu sanni bane , basu santa bane walahi, ba zata taba yarda a dauki Nadirah a mikata ita daya ba, koda sun yi haka ita zata je daga baya a matsayin yar shishigin bayi! A hankali Aban NADIRAH ya dakatar da matarsa dan baya so su fara fada a yanzu da zuciyarsa ke karye, bar ga Allah yana iya yi masu kuka A sanyaye ya ce" To Hindu yaya zaki yi da yar taki? Ta yaya zaki shawo kanta?, Yaya zaki yi da hakkin Aminu? Shin kunna cin kudin Aminu kuwa?" Caraf Fadime ta cafe ta ce" Ahaf, cin kudinsa ai sai dai kar a kuma kaima malan walahi da wani zance kake" "Ki yi shiru mana Fadima menene haka ne?" Aban Nadirah ya fada a sanyaye Hindu kuwa ta yi tsuru tsuru tamkar zata kifa A hankali ta ce" Na shiga uku, riginar duka a Indina da Aminu take innalilahi " Ta kalli Fadime ta kalli Aban NADIRAH A hankali ta ce" Walahi ni dai ba zaku aikani fada mata ba in dan wannan nema kuke min rarashi ba zan je ba, yi abinda tace sai ta gudu idan aka hanna mata Aminu? Ai aunty ce kadai zata iya wannan aikin dan walahi abanta kaima kuka zaka mata dan na kula baka hanna kanka kuka yanzun, babu mai hadani da yata walahi" ta karashe tana sharar hawaye na gasken gasken ta dora da fadin" kuma mu bama cin kudin Aminu, Allah na tuba gori ba kyau ni fa na dora masa teburin da Indirah tace a bashi jari, kuma babarsa yanzu haka wannan cirar da kuka ga na mata mun gudo a bakin da baya karya na hi ance babarsa ta kai jaka uku da rabi kudin an gani ana so na yar makotansu, ai ba wani ciwon hannu da yake ihun ba zata masa auren dole bane ya sa na gudo da yata dan na shiryawa kowani dan iska da kyau, ni dai yanzu ta yata nake ba ta rigima ba da kike nemana da fada!" A hankali Aban NADIRAH ya ce" Ku daina rigimar nan mana dan Allah, innar Indi kina nufin shi Aminun na Indinki ne za'a yiwa aure? Ya Allah " Hindu zata yi magana muryar jakafiyar cikin gida da muryoyin maza biyu ta karade gidan da salama A tsorace Fadime ta fara mikewa, hakama mijinta, bale da suka jiyo muryar NADIRAH tana fadin" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* *LABARIN UMUGHLUK ITIFAL, BAN DAUKO SHI DAN CIN ZARAFI WA KASATA KO JAMA'AR KASATA BA, SALO NE NA MARUBUCI DAKE BUDE TUDU DA GANGARE DAN HADEWA A MAHADA GUDA, KO KUSA BAN GOGI ADALCI DA KARAMCI IRIN NA SARAKAN KASATA BA, NA KAMANTA RUBUTUNA NE A SAMAN IDEA DINA DAN KAWAI NA ISAR DA SAKONA DA KUMA SALON ALKALAMINA, IDAN HAR A RUBUTUNA NA TABO MASARAUTAR GARINKU KUMA ABINDA YA HAU KANTA BAI MAKU BA , KO YA YI DAIDAI DA HALAYAN DA KUKE FUSKANTA KU SANI BAN JE NA BINCIKA BA, BAN KUMA YI DAN NA CI ZARAFI BA, NA DAUKI ALKALAMINA NE NA KUMA YI AIKI DA DAMATA NA KASANCEWA YAR KASA, VIVE L'IND PENDANCE, VIVE LE NIGER, MERCI* 1 A tsorace Fadime ta fara mikewa, hakama mijinta, bale da suka jiyo muryar NADIRAH na fadin" Aa gwara dai ku dakata din innata tace wanda ya wuce na wuce da shi, sirri suke yi" Da rarafe HINDU ta fito tana lekowa ta ce" Ke zo nan zo" a ranta kuwa tana ayana 'na shiga uku Gimbiya da sara suka, kar ta ja a fasa' Muryar Jakadiyar ne tana fadin" Ke kauce mana daga hanya ko mu babalaki aikomu aka yi wajen sarkin Dogarai!" Ya saka Abanta saurin fitowa yana dubansu yana kakaro murmushin dole ya ce" Jakadi yarki ce, ta wajena NADIRAH " Da mamaki ta sake kallon NADIRAH dake tsaye tana sake turo baki Murmushi ta yi ta furta" Masha Allah, Allah ya raya ya fitar da miji mai takaici" Hindu kawai ta amsa sannan ta kama hannun NADIRAH suka shige daki suka zauna sunna kallon kallo Jakadiya ta sake gaisar da su da mutunci, domin su din mutane ne da suka san darajar kansu kuma suke kiyaye dukkan abinda zai iya zubar masu da mutunci, Bayan sun gama gaisawa ta dube shi ta ce" Mai martaba ne ya turo mu da kansa, yace ace da kai yana wajen sirrin da ka sani, ka je masa da sakon GAGARA yana son gannin idan ya cencenta, yace a ce da kai yana kan bakansa, maganar na nan daram yadda aka yanketa, yace ace da kai
Chapter 22 · 0% Book details