← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 87

Sashe 13

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a lahira da wutar jahannama za'a gogewa masu shi, ke nu kam banma ga abin daga hankali ba Indirahna, ki kwontar da hankalinki, idan kuwa zaki bini birni satin nan mai kamawa sai mu leka mamanki mu gaisar da ita sannan mu wuce gidan kallo mu yi kallo sai mu karkato kasuwa mu dayi kayan yan gayu harda takalmi kin ji?" Kai ta gyada tanna murmushi ta ce" Inna hala asusun da zaki siya min gadon mai runfa ne kika fasa? Ko na Abana ne da yace zai min gara buhu takwas?" Yar dariya ta yi ta ce" ina ai asusun gadonki ba za'a fasa shi ba ko ana ha maza ha mata, na abankine, barama na kimtsa tarbansa dan na san yana iya kirtan ba dadi dan na taba asusun nan na gararki, zo tsefen kaina na yi sheme sheme a tsakar gidan nan ya tardomu a haka sai ace innar Aminu ta shinfideni, na tanata ba zai ji haushin kudinsa da yawa ba" Dariya ta yi ta kwontar da kanta a saman kafar Innarta, a hankali ta ce" Innata, ina yin adu'ar nan fa, ko yau da kika tadani sallar asuba da na yi raka'atanul fajr kafin a yi kiran sallar asubah na fara salatin nan, da aka yi sallar aka gama na dora na yi ta yi , na yi ta yi sai da na kai dubun nan, sannan na dora fa adu'o'in tsarin da Innar birni ke koya min, na yi azhkar sannan na roki Allah ta bani miji na gari Aminuna......." Murmushi Innar ta yi tana shafa kanta a hankali ta ce" Ki ci gaba da yi, ki yi ta yi, kin ga ni yanzu idan ban yi dubun nan kafin na kwonta ba bana iya barci, komai gajiya sai ki ga ina zabura, kuma adu'o'in neman tsari sunne makamin mumuni, babu boka ko malamin da ya fi bakinka da na iyayenka, ka fadawa Allah da kanka, to fa in du duniya zata tsaneka Allah na tare da kai, wani lokacin zaka ga kana ta Adu'ar kana ta yi biyan bukatar bai zo ba, to ka sani alkhairin ne a wani bangaren wanda Allah zai tabatar maka, kai da kanka sai ka yi mamaki, yanzu dai ai ba'a kai rikici irin na makada ba, ama ki duba ki ga Abanki kulun yana sama, makadi ne ama a haka yake neman kariya a wajen ubangijinsa, ki ci gaba da neman zabin Allah, ama ki daina cewa alkhairi Aminu dan baki san wannan mai wuyan uwa marikin lema bane alkhairin ko mai garin nan bane" Kai ta dago da sauri tana cuno baki ta mike tana fadin" Kai inna, ke dai ba za'a yi hira ta zaman lafiya ba sai kin kawo masu mulkin nan da basuda tunanin komai a rayuwa sai mulki, ni fa ko sarkin yan tasha bana so walahi in dai sarki ne!" Da ido ta rakata domin ta warci dayan tulun fa ya rage da garaje ta yi gaba Ajiyar zuciya ta dauke ta ce" Tuluna, Allah ya sa ka dawo da ranka kar wani ya tabata ta mula masa, ni kam ban san a ina Indirah ta gaji fada ba sam" ( to fah _________________________________ Shayin da ta kurba a bakinta mai dumi da dandanon zuma kamar zata yi tagia ta furzo a zabure tana sakin kofin kwalbar mai dauke da ruwan shayin ya bare a saman cinyarta A haukace ta saka ihu tana fadin" FADIME FADIME, shigo shigo bani ruwa da gishiri ciki na kone kafata" A hanzarce ta shigo ta yi kicin kanta a kasa domin Mai martaba na zaune ba zaka yi kallo irin na kure waje ba dan gudun yin laifi wajen matarsa mai haukatacen kishi Da sauri ta dawo kanta a kasa domin kunyar lamarin take ji a zuciyarta ta fan zuba mata ruwan a saman cinyarta da ta kwaye gaba daya kamar wata wace ta soye wannan tona sirrin jiki haka "Duba min da kyau na kone ko?" Gimbiya ta fada tana rinrintse ido A hankali ta duduba wajen, ya dan yi ja dai ama ba zai tashi ba tunda an zuba ruwa mai dauke da gishiri ai Kai ta girgiza da nutsatsiyar muryarta ta ce" In sha Allah ba zai tashi ba " Kai ta gyada tana cire dubanta a kanta ta mayar gefe tana saka yar yatsarta a bakinta ta dantse ranta a bace da maganar da mijinta ya zo mata da ita, ba dan komai ba sai dan tunaninta ai kashe mata ya kawai za'a yi, duda baban mutunci da daukaka ne zasu karkarowa kansu,ama kuma yarta fa? Da ido ya raka FADIME har ta bacewa ganninsa a hankali ya sake shafa gaban kirjinsa yana cire tunanin dake ransa ya sake fuskantarta ya ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 0 Ya sake fuskantarta ya ce" Kina nufin maganar nan ce ta saka ki sakarwa jikinki shayi?" Juyowa ta yi, dan a lausashe ya yi maganar yanzu ta zuba masa ido Kai ya gyafa ya sake kausasa muryarsa yana kallonta ya ce" To ki kama kanki, ki tuna babu wanda ya sakani a wannan matsalar sai ke......, Bakida hurumi a wannan maganar, bakida abinda kika isa ki ce a wannan maganar sai fatan na shawo kan yata ta aminta da maganar nan, idan har kika kuskura kika yi wani abu na rantse maki sai kin kasa gane kanki bale har wani ya ganeki!" Da ido ta rakashi har ya ficewarsa Bayan fitarsama ta dauki minti biyu kafin take mikewa tsaye ta yi dakinta Wayarta ta lalubo ta zauna ta ci gaba da doka wayar sarauniyar dogon dutsi, sai dai amsar daya ce wayar bata shiga Wurgar da wayar ta yi ta doka hannunta a jikin abin gadon nan ranta bace ta ce" Ni zaka dauka , ka kaini gaban dan cikina ka gurfanar da ni, n bashi hakuri sannan na bashi yata kyauta? Yar da nake da burin a aurenta na tara dukiyar da ban taba tarawa ba a duniya? Yar daya mace kwalin kwal ka zo min da maganar wai idan ta shiga ba zata dauki lokaci ba zata zamto itace magajiyar garin Agadaz? Ta yaya? Ta ina? Lalle yau da na same ki a wayar nan sai na fara maki alkawarin idan har aka aurawa yata UMUGHLUK ITIFAL Walahi walahi sai na halaka ki da kaina kafin zakin sarakai ya kama ki,!" Ta idasa tana cure daurin dan kwalinta ta zauna ta shiga tunanin abinda ya dace da hanyar da ta dace ta bi dan magance wannan matsala, ta san waye mijinta, tanada iko a garinsa ama fa a wajen talakawa, bata isa da shi ba, abinda ta fi karfi kishiyoyinta ne, summa dan ta tara yaya da shi fiye da su, dan a cikinsu daya tak ce ta haihun itama shamatarta ta yi, ama idan abu ya hado su magana daya yake yi baya sake bi ta kai kuma ta zauna dar ba maganar dagawa ____________________________________ *Madina garin manzo, BAYAN WASU KWANAKI* "Ya salam ki daidaita numfashinki, dage nikaf din ki shaki numfashi haba BAHIJA!" Kawarta ta fada a dan rikice a lokacin da ta shiga wani irin numfarfashi sama sama tamkar zata sume Yadda tace din ta yi, watau ta dage nikaf dinta domin ba zata iya shakar iska da kyau a rufen nan ba, sannan ta mike ta dan yi gaba kadan ta lumshe idannuwanta har numfashinta ya daidaita sannan ta sake dawowa ta zauna ta sake zuba masa ido tamkar zata ciro idannuwan nata ta lika a fatar jikinsa A nutse yake tsaye ya basu baya, shigar dake jikinsa yau sak irin ta larabawa ce, wato ya daka alkyabar nan tasu mai ruwan yelow, ya dora hirami a saman shigarsa ya dan nade hiramin baya, haka kuma a tsayen da yake hannunsa daya a bayansa haka a jimke, dayan kuwa daga gaba sunna magana da wani mutumen da kana ganninsa ka san shima baba ne Kai ta dora saman table din cin abincin a hankali idannuwanta suka ciko da kwallah tana sake yi masa kallo wanda ya wuce misali A tausashe balaraben da suka yi aikin umurar tare ya sake dubanta duba daya tak ya dauke dubansa yana dan sake kallon restaurant din a ransa yana ayana shi yasa hotel din nan wani lokacin takeda matsala, domin akoy dan wajajen da ake hadewa mata da maza ba wajen ibada ba, hakan kuwa ba dadi, dan yanzu matan da mazan duka sai a hankali, Dogarinsa ne ya karaso ya yi masa bayani kasa kasa sosai, a kan maganar juyawarsu gida ne A tausashe ya ce" Aa, ka daukar mana na gobe idan da hali, garina na zuciyata, ga kuma Auta" Kai ya gyada ya juya cikin takun karfinsa, shima shigar larabawan ce a jikinsa abinsa Kujerun alfarmar dake ajiye suka karasa suka zauna, a nutse ya lankaya carbinsa a hannunsa ya sake duban Abu huzaifa ya ce" Sosai sunna saka abaya, zan iya ce maka a yanzu a garina Abaya da lafaya ta zama kayan ado a wajen yan mata da kuma matan aure, ai sunna son shiga irin ta larabawa" Kai ya gyada yana murmushi ya sake duban ASADEEK ya ce" Ka san me ya fi bani sha'awa da kai?, Irin yadda kake nema, kanada dama sosai, ama kuma kana nema sosai, babu ruwanla da kwonciya a nemo a kawo maka ka ci ka tada kai, idan dai zaka mayar da taro kadago baka tsoron hakan" Murmushin da ya yi a yanzu shi ya saka BAHIJA furta" Wayo Allahna, zan je, walahi yau zan je, zan tunkare shi" Kai kawarta ta girgiza tana dafe goshinta ta ce" Dama ki daina ba kanki wahala, irin larabawan cen ba zasu taba auren bak'ar fata ba, bayan wannan irin yafda kike tsoronshi ina tsoron ki zamto baiwarsa, ki duba ki gani sati biyu kennan ke ko masalaci baki je ba, tun baki san lokacin da yakan dan wulgawa ba har kika sani, sau nawa kina yinkurin hakan bakya iyawa, uwa uba kwaliyar yi kike yi ama kamar bai san da ke ba, ki yi hakuri kawai ki........."
Chapter 13 · 0% Book details