Sashe 58
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya faru wanda yake abu ne da ko a gida yana yawan faruwa da manyan mutane da ita, jta fa matsalarta kawai kar a shiga gonar iyayenta, idan har ka kiyaye wannan babu mai dadin zama irinta, haba ranki shi dade ina ita ina rasaki a gefe bayan kece uwa kece uba kece makarbiya tata? Kece fa ja gaban tafiyar nan, idan har hakan ya bata maki ki yi hakuri in sha Allah zamu kiyaye, yanzu haka rashin fitarta dan bata sani bane, nan fa muka wuni da ita yanzu barci ya nemi kifata da kas sai ta shige ta kwonta, tana farkawa zan sanar mata fa ga baban sake sai ta je idan lokaci bai kure ba" Umma ta wani saki murmushi, babu abinda ya fi dadada mata sai jadadawar Hindu cewa itace gaba daya tafiyar nan, uhum tana jin dadin ace itace komai fa a waje, tana matukar kishin ace wani ya kamo kafarta ko zai gogi wajen da take sarauniya ce, take mulki a wajen, ba zata taba manta a lokacin da ran mahaifiyar ASADEEK, idan matar na tafe tana take mata baya sai ta ji kamar ta saka hannu ta maidota baya ita ta shige gaban A gadarance ta ce" Na yafe mata, ai ba zan jima ina fushi da ita ba, sai dai a yau kar ta fita, zan san hanyar da zan bi na goge tunanin da bayi ke iya farawa da jama'ar babar masarautar, ai sallar BIYANO ke tunkaromu, zan gani abinda ya dace a yi dan ta karra siyan zuciyyoyin WA'INDA suka isa su fada magana ta yi tsauri" Innarta ta karra gyada kanta ta yi shiru ta koma tunanin abinda zai fisheta har Umma ta gama yatsine yatsinenta ta mike ta tafi A hankali ta koma dakinta ta zauna ta shiga buga wayar Fadime Ta yi bugawa ya kai sau uku da kyar aka daga FADIME na dagawa kasa kasa ta ce" Wai HINDU meye kuma?" Inna ta yi murmushi tana sauke ajiyar zuciya ta ce" Ba maganar abin dadin bane zan maki, maganar da nake son yi maki Aunty a kan Indi ne, kin ga hankalinta a tashe yake, gaba daya rikici take yi wai mu koma gida, ta tsorata da shi ne inaga, kuma bakinta har yanzu yana ambaton sunnan Aminu wai, bana so kai tsaye ta tona mu fa? Kin san Indi kuma idan hankalinta na tashe komai yi take yi" Shiru ne ya wanzu na dan lokaci, a hankali Fadime ta ce" A tsorace take sosai ne?" Hindu ta ce" Gaskiya a tsorace take, domin ban taba gannin cutar da ta kwontar da ita haka ba, kina gani fa ko ciwo take yi tana tsaye a kan kaffafuwanta ne, ama yanzu sai a hankali" "Shi din, ba cewa aka yi bashi da lafiya ba?, Ko ta ji ciwo ne?" FADIME ta fada da kyar kunya na lumlubeta, dan so take yi ta fahimci damuwar yarinyar HINDU ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Kamar baki fahimci abinda na fahimta ba, kamar baki zauna a gidan sarautar ba, ba maganar rashin lafiya, kitumurmura ce ai malan ya fada min!" A hankali Fadime ta sake fadin" HINDU hala banda amsar maganin har wajen boka kika je?" Shiru Hindu ta yi, sai kuma ta ce" Kashhh, a bar maganar kawai ama ba ni na je ba, Habu na aika gaskiya, kuma ban yarda da maganar ba dai, na dai shirya diyata ne shikenan" Ajiyar zuciya ta sauke, a hankali ta ce" Kina ji?, Dole zaki sanar mata cewa ko me yake yawo a cikin kanta ya dace ta daidaita tunaninta ta gyara harshenta ta kiyayi kama sunnan wani da auren wanu a kanta, Dole zata bar maganar nan dan kar ta kona kanta garin shirmenta, Dole zata daina tunda tana jin tsoron Allah taba kuma burin gobe kiyama ta samu sakamako mai kyai, aure ibada ne, ba abin wasa bane, du D'a na halak zai kiyaye yin wasa da igiyar aure, ido zaki murje ki fada mata gadkiya, sannan ki sakata a hanya kawai ki yi kamar baki gane komai ba dangane da yarenta, sannan idan da hali kar zama tare da su ya gagareta, ta koma hanyar da aka dorata sannan ta dora daga inda ta tsaya...." HINDU ta sake sauke ajiyar zuciya, hakan ya saka Fadime a tausashe ta ce" HINDU, na san a gaban matsalar yarki baki da karfi ko dabara, ina so wannan karron ki jajirce kin ji kanwata?" Kai take gyadawa tamkar yayar tata na gabanta, haka kuma ta ji ta samu kwarin gwuiwar tarban yar tata Mikewa ta yi ta koma falon tana ci gaba da tsara yadda ya dace ta biyo da Yar tata dan samun kanta, bama baban rikicin watau komawarta dakin mai babar fada ........................................................... *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 4 A nutse Sheikh ke yi masa bayani, bayani ne yake yi masa dala dala ta yadda zai fahimta, bayan zamansa a fada da taron da suka gabatar bayan sallar La'asar suka shigo falo, SHEIK ya dube shi yana fadin" Rabonka da zagaye kauyuka irin su Itar, Timiya, titibe ka jima, akoy dukiyarka a cen na kiwo da noma da ake gadi, ka kuwa san garken rakumanka sun zama arba'in da uku a garin Timiya?, Ya dace ka je ka ga yadda arzikin ya yabanya UMUGHLUK ASADEEK ya yi dan murmushi bai ce masa komai ba SHEIK ya sake zuba masa ido a hankali yana kallonsa, a nutse ya ce" Kamae baka jin abinda nake fadi fa?" ASADEEK ya sake dubansa , a hankali ya ce" Allah ya bamu iko" SHEIK ya amsa da amen, sannan ya ce" Maganar da na yi maka dangane da rike maganar nan sirri ina fata kana kai?" Asadeek zai bashi amsa aka sanar da shigowar UMMA Shigowar Umma dauke da wani gora mai dauke da rubutu ya saka SHE IK yin shiru yana kama kansa hadi da maida dubansa wajen TV yana dan kallo duda ba magana dake fita ta tvn sai hotunan larabawa dake karatu kawai Zaunawa ta yi cike da isa ta gaishe da Sheikh bayan ta gaishe da ASADEEK tana cire kanta a barin SHEIK din Kwata kwata a duniyarta ta tsani wannan malamin walahi, mutun ne shi mai shegiyar akida da dan banza iya yi wai shi SHEIK, ta yi kisar, ta bi ta kasan kasar dan ta hadasa masu fitina har ya kore shi ama ya gagara, akoy lokacin da ta so kakaba masa sharin zina karshe ya aure matar ta zama sirri a gareshi, idan ta shigo wajen da yake gaba daya sai ta ji ta tsatsamta da shi, kwata kwata ta tsane shi walahi, wannan fa shine mai yin shahada idan za'a kashe mai aikata laifi irin nata, shine mai jawo masa ayoyi kala kala yana bashi fasara shi kuma yana zartarwa A dan gagauce ta sanar da adadin kudin da take da muradi saboda kicin , domin kiri kiri HUZNAH ta nuna ta amshi kicin din MAI MARTABA, shine ya sanarwa Umma idan tana sha'awar girki bayan na HUZNAr da dayar matar, tana iya fadin dukkan bukatarta a je a siyo ko kuma ta yanke adadin kudin da take da bukata ta bude kicin din bangarenta, dalilin zuwanta kennan har ta biyo masa da rubutun da ta saka ake yi masa na malaka ne wanda cijn ttsafe tsafenta ne dan ta malakeshi tsaf Mikewa ta yi da shek din kudin dake hannunta cike da gadara ana yiwa SHEIK tunkaho ta juya zata tafi, sai kuma ta dawo da kula kula ta ce" Yarona, gaba daya yau sai nake gannin kamar kana cikin farin ciki mai yawa? Ko nice ke tunanin haka?" Murmushi ya yi yana sasauta rawaninsa a hankali ya furta" Alhamdulilah Umma" Sake zuba masa ido ta yi, sai kuma ta ce" Allah ya karra kawo abinda zai kawata fuskarta da murmushi na farin ciki irin wannan" Murmushi SHEIK ya yi bayanane yana gyara zamansa sannan suka amsa su biyun a nutse, Wani kallo boyaye ta sakarwa SHEIK, sai kuma ta fice tana ji kamar ta dawo ta tambaye shi to me ya saka shi farin ciki haka? Sannan ta tambayi Sheik shi kuwa murmushin da ya yi na meye? SHEIK ya ce" Ina fata ka fahimci alkiblata?" Asadeek ya tabe bakinsa yana gyara zamansa a nutse sannan cike da fitar da harufa a tausashe ya ce" Ban san dalilin da ya saka kake karra nanata maganar nan cewa ta zama sirri ba, duda abu ne da ba zan falaso shi doron duniya ba domin sirrina ne, ama kuma abu ne da ya dace ace na wuni ina sukuwa a saman doki a garin nan a wunin yau baki daya dan nuna tsantsar farin ciki da samun yanci, ya dace ace an wuni ana sadaka a bayane ba a boye ba,.....SHEIK ka san na rasa me ya dace ace na kaamanta mata a matsayin karamawa?" SHEIK ya yi yar daria ya ce" Kyauta?" Asadeek ya dan gyada kansa kadan yana cijewa kadan dan yau gaba daya SHEIK bai barshi ya huta ba SHEIK ya ce" To ama, idan aka yi kyauta abin ba zai yadu a fada ba?" ASADEEK ya koma ya jingina, cike da tarin lamari irin na sarautar dake yawo a jinninsa, cike da basarwa tamkar ba zai yi magana ba, ya sake bude bakinsa ya ce " Gaba daya ban ga wanene ya dace mu ji tsoro ko shakun ya ji ba, " Ya dan saurara yana shafa daidai kirjinsa yana jin wani irin yar yar yar a dukkan gabobin jikinsa sakamakon tuno lamarin yarinyar da ya yi, subahanalah wani irun daukaken abu ke ratsa shi ba ji ba gani, a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya dora da fadin" Du yadda zaka yi, kana da dama, abu daya ne na sani shine ta cencenci karamawa domin koda kowace mace nada damar yantani ita ta kai ga ci,, Ban sani ba, ita din makashina ce, ko mai tona asirina ce? Koma mecece ita na san tana da baban matsayin da ba kowace ta samu ba, shine zamtowa sirrina, sauran maganar