Sashe 47
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
take yawan fadi da yaren nasara, watau CLASSSSS Hannunta ta dan bi da kallo sai kuma ta saki gashin kanta ta dan wana kanta kadan ta sake zubawa madubi ido Cikar gashin da bakinsa yanada yawa sosai, ya ishi bawa kwaliya ko wace iri ce , cen dama ta gaji iya kwaliya da gashinta, kitso ne bata so sai sun sha rikici da innarta take yi mata tafka tafka biyu, ko hudu A nutse ta saka abin tsaga daga gefen hagu na gashin kadan ta yi tsaga mai dan tsayi kadan ta ja gashin gefe sannan ta saka macaji karami a hankali ta ringa caje wanda bashi da yawan har ya kwonta luflufluf, sai kuma ta saka yan yatsunta a na gefen ta dan kara sakashi ya karra tudu kadan ta barshi zube a gaban kijinta da gefen fuskarta kadan Jan baki take ta kallo, da kyar ta iya janyo mai ruwan kasa kasa ta bude shi ta shafa dan kadan a bakinta , sannan ta dauki kwali tana ta kallo da tunanin anya ba sai ta yi kiran innarta ta saka mata ba? Domin bata taba sakawa da kanta ba ai Karshe dai dagewa ta yi ta ringa karkata kai da kyar ta saka kwalin tana tsale da ihun ta saka sannan ta koma wajen kayanta bayan ta ga takwas ai ta gota tuni t dauka ta saka pant din da rigar ta koma wajen madubin tana kallon kanta harda dan juyawa a gabansa kadan ta dora hannunta a saman cikinta dake shafe uwa babu hanji a ciki ta yi murmushi , sai dai tudun duwawunta ne suka bata mamamaki, ba kasafai ta cika kallonsu ba, aminiyarta, kawarta Yar dubu ke yawan cewa ta ringa saka sutura mai rufe jiki saboda maza lalatatu masu bata ya'yan mutane dan Allah ya bata kira, ita kuwa sai tace Aminu zai iya tarda mutun ya kashe shege a kanta Alkur'an! Murmushi ta yi tana gyada kai, idan ta koma ta labartawa yar dubu abinda ya faru da ita bata san ko zata yarda ba, ta yiwu sai ta sakata ta sha Kur'ani ko zata yarda, ama in sha Allahu ko kwana zasu yi sunna dambatuwa sai ta sakata ta yarda tunda ita ba makaryaciya bace bale a mata iya shege Turaruka ta dauka a fili ta ce" Ku zo nan yayan albarka mu bare banza, tunda an zubaku uwa ba siya aka yi ba" Karshe dai ta kai mintu talatin bayan karfe takwas din sannan ta fito da takalmi plat mai laushi ta yiwa Innarta salama bayan ta ja rantsuwar ba zata aikata aiki makamancin na jiya ba sannan ta fice ita daya babu ko yar rakiya ta bi ta babar hanya hankali kwonce tana tafe tana kallon yannayi da tsare tsaren ginnin sarautar ta garin AGADAZ, komai a al'adance sannan da tsarin zamani, kana gannin abin zaka gane an narkar da kudi fa ba abin wasa bane Bata san cewa shiga ita kadai sai ta sha wahala ba sai da ta karasa bangarensa Hanyar ta samu kanta da zubawa ido da tafka tafkan dakarun masu tsaitsaye sunna gadin wajen A lokacin da ta sanar masu itace Bahija amarya aka yi mata tambayar zata halarci cin abinci ne? Ta bada amsa aka nemi da ta bada takardar gayata sai da mamaki ya kamata A nutse ta aro halaya irin nasu, a dake ta bada umarnin a shiga a sanar da zuwanta idan an bada umarnin ta koma sai ta koma A kan dole suka aikata hakan, bayan kamar minti biyar aka bata danar shiga Baki ta tabe a ranta tana ayana' dama na zo da redion innata na saka kidan kai ku kama sana'a mata na maku habaici kitika kitikan banza kunna gafin kato...., Koda yake na san yana dan baku na sakawa na salati' Haba dai ta samu ta karasa ta wuce bayin dake zaune bayan sun zube sun gaisheta sunna mamakin ganninta ita daya kuma amsa masu harda su ya gajiya sannan ta bude madubin dake fitar da danshin AC ta shiga da salama kasa kasa a bakinta Ta tabata koda shi namijin bai kalleta ba, yan matan sun zuba mata ido, domin tana ji a jikinta kallonta ake yi, Wajen da ake sarkafe kaya idan a shigo ta karasa, hankali kwonce ta cire Alkyabarta ta rataya a jikin abin ratayawar, wanda haka sai da ya saka HUZNAH kwarewa da abinda ta saka a bakinta ta dan shiga tari kadan tana sin cire idonta a kanta ama dan jaraba tana karra kallonta Kasa kasa ya dan dago da dubansa daga abincinsa ya dan kalli HUZNAH Sai kuma ya kai dubansa inda take kallo tana fan tari hadi da kai kofin ruwa bakinta Samun kansa da zubawa yarinyar ido ya yi na yan dakiku sai kuma ya dauke kansa a ransa ya ayana' Ta tabata, yar daba ce yarinyar nan, ko irin yan duniyan nan rikaku' Tana murmushi itama a nata ran tana ayana' Haka nake so, so nake na haukataki, ki yi zaman aure da mijinki mai sunna zaman aure kafin na tatara tsumakaraina na karra gaba Alkur'an, ama kina abu kamar wata bagidajiyar da bata da ilimin adini? Ilimi ai haske ne, kuma ko ni da nake kauye a wannan fannin na san me nake yi sarai!' Bata tashi idasa neman rikita masu lisafi ba har Auta da ta karra zarro ido, Uwa uba Umma, matar dake bata mamaki, zaman cin abincin dare da ya dace ace ya yi daga shi sai matarsa a dakinsu abinsu aa, ga wata mai zarro ido kamar mai farfadiya, sai wannan rusheshiyar mata mai ruwa da munafukai a saka su tsakiya, ita kuma matar kai a kasa uwa tsohuwar algunguma a gaban mijinta? Uhum, sam basu da tsari gaskiya sai da ta karaso facing din da yake ta dan kama gefe da gefen rigarta, ta dan baje tsayuwarta kadan sannan ta saki dayan hannunta tana murmushi ta yi wani yannayi da hannun da muryar murmushi tace" Barka da warhaka Aban su Datawa......" Yanzun kam Umma ce ta ji miya miyar zata sarketa, a dan rikice ta cire dubanta daga kan Nadirar ta maida kan abincinta tana yin iya yinta dan hanna kanta sumewa da tashin hankalin da take kallo Auta da du take a hali na rashin jin dadi dan an sakata cin tuwo mai nauyi bayan ita bata cika son tuwo irin haka ba , asalima nonon sanuwar dake cikin katon flask na yayanta take so a zuba mata, ama Umma tace wannan zata ci dan maganinta sai ta samu kanta da sakin boyayan murmushi tana sake satar kallon yayanta da abin al'ajabi irin na mahaukatan zamani ya saka shi dafe haba a bayane, duda rawaninsa iya bakinsa da habarsa kadan ya bayanar yana kallon rikakiyar yar gajaliyar nan Dagowa ta yi tana fadin" Kai kuguna" Sai kuma ta karasa ta kalli HUZNAH ta sakar mata murmushi a takaice ta ce" Sannu fa" Sai kuma ta kalli Auta itama ta zarro mata ido yadda take ta zarro mata ta ce" Ke kuwa gyara dubanku mana haba" Sannan ta sake kallon Umma, ta sakarwa Umma murmushi wace idannuwanta tamkar zasu fado dan kallo itama a takaice ta ce" Sannu dai Ummanmu" Kujera ta ja ta zauna tana sauke numfashi irin ta sha aikin nan sannan ta ce" Walahu nake fada maki aunty dan kwali na nema na rasa karshe dai haka na taho kar aje na yi lati 'Latti? Dan kwali? Ya Allah ka sakani gane wannan mata tun kafin ta kasheni, wannan wace irin mace ce? Wani lati bayan sai da sarki ya zauna ta zo?, Wani dan kwali a tarin suturunta?, Ta rasa me zata saka sai wannan rigar?, Ta zo ta mana gaisuwa k amar sa'o'inta? Koda yake shima sarkin ga yadda ta gaishe shi uwa uba Umma?, Ya Allah menene wannan ne? Wacece wannan matar ne? Allah ka shiga lamarina da ita ya Allah ka dorani saman kanta kar ta rikita min zamana, ni dai banida matsala da ita, ama sai wani haroni take yi!' HUZNAH ta ayana a ranta sannan ta dauke kanta bata ce mata komai ba, dan baya so ana saman table a ringa yawan magana haka Baki NADIRAH ta tabe, ita fa ba fa za'a yanka mata baki ba har ya zo yanai mata tsami dan bakin hali da rainawa kai wayo ba walahi, tsaf bakinta na magana ne Allah walahi Abincin take kallo Kaf abincin nak babu abinda ya yi mata, ba cika son abinci ta yi bama a rayuwa, hakan ya sa ta fara yin tsuru tana kallonsu daya bayan daya ta ga dai abinci kowa ke ci banda Auta dake dan fama da nata ta kasa ci da kyau A hankali ta ce" Bakya son tuwon ne?" Auta ta dago da sauri ta kalleta, a hankali ta saci kallon sauran, gannin babu wanda ya kalleta sai ta amsa NADIRAH da ido NADIRAH ta dan karra kallonta ta ce" To ki bari mana ko dole ne?, Kina wani abu kamar an wanka maki mari" Umma ta dago ta zuba mata kakausan kallo kafin ta budi baki a sanyaye ta ce" Allah ya karra maki lafiya, i ya zama dole ta ci abinci dan ta sha maganinta" NADIRAH sarai ta karanci sakon idannuwan Umma, ama sai ta watsar Hasalima mikewa ta yi ba kwaramniya ta shiga dan bubude abincin tana rufewa, yannayin da take yiwa fuskarta kamar ta ga wani abinda bata son ci mai warin nan ke karra kunna HUZNAH Karshe ta maida dubanta kan abubuwan dake gabansa A soyayarta da nono ko a me aka saka shi kallo daya zata yi masa ta gane menene Murmushi ta yi ta dauki manyan kofuna na kwalba biyu ta ajiye ta mika hannu ta dauko nonon da ake tofe masa da addu'a daga wajen SHEIK sannan a kawo, nonon da ko Umma bata tabawa bale HUZNAH, ta bude ta cika a kofi daya ta mikawa Auta sannan ta cika a daya tana murmushi ta rufe ta koma ta zauna ta sake kallon Auta ta ce" Ki ajiye abincin sai ki sha wannan, yanada anfani sosai ga lafiyar dan Adam" "A kan wani dalili zaki taba abin madarar mai martaba?" Muryar HUZNAH, da yannayi na ta