Sashe 32
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sam, yaya NADIRAH zata tsaya kanta da kan Gimbiya? Kai subahanalah Sai da gimbiya ta samu rantsatsen daki aka saka kayan BAHIJA dake ta aikin waya sannan ta dubi Bahijar da sam bata damu ba ta ce" Daughter, kin dai ji abinda na fada maki ko? Ki yi kokari ku shirya da abanki, sannan ki yi iya yi ki ki rike kafarki da wayarki, ba kowa zaki yi hira da shi ba, ba kowa zai san inda kike ba" A dan kagauce tana magana da kawarta ta dan dakatar da ta ce" Momcy na fahimta gide, shima Papa din bai hadu da gayen bane, na masa uzuri da zarar sun hadu da kansa zai saka min albarka, momcy kin san Fadime ba zata iya aikina duka ba ko? Gaskiya ki san ta yadda zaki sama min baiwa ko dan murzawar jikina da susar baya, ita sam bata iya sosa baya ba gaskiya" Kai mahaifiyarta ta gyada tana kallon yar ta gama abinta ta shige dakin tana mayar da iPhone dinta kunnenta Ajiyar zuciya ta sauke tana ji zata yi missing din yarinyarta, sai dai ba komai zata jure in sha Allah ( uhum) Har bakin mota Fadime ta raka Gimbiya, har ta kama zata shiga ta juyo ta sake fuskantar FADIME a kausashe ta ce" Ina fata yarki bata fi karfin ki ba?" Fadime ta sake kallonta da mamaki Gimbiya ta dage kafadu ta ce" Dan bana son abinda zai je ya dawo, kar ki manta a hannuna ikon ci gaba da walwalarku take!, Na ga ta cika tsaurin ido ko rashin kunya ne? Kaina da nata a daidai da junna bata duka ba" Ajiyar zuciya Fadime ta yi, a sanyaye ta shiga bata hakuri , ita kuwa ta ja tsaki ta bude ta shige tana umartar Dorevmban kan su tafi Jiki ba karfi ta dawo dakin nata, dan sai take ji gaba daya gidan kuma a yanzu ya zama ba gidan da zasu wala ba, domin ita ta san wacece Bahija tun yarinyar na zannin goyo Tana bude dakin ta saka kafarta guda ta ji muryar yarta, kamar tana fada fada tana fadin" Kowani wawa sai ya taka mahaifana? Bayan biyayar da ta masu zata hakura da komai ta barwa Allah sai an biyota da shashashar magana? Idan Innar Abana ta yiwa wancen abar da ka kawo bauta Allah ya tsinen ......" "Cuta da malati dan ubanki makadi indi!" HINDU ta fada tana tareta hadi da buge mata baki NADIRAH ta janye tana kama abin gado ta ce" A lokacinda tace ASADEEK yake ko wa? Kiris ya rage na dauke yamutsatsen bakinta da mari!" "Lahaula wala kuwata ila bilah, NADIRAH, NADIRAH!" HINDU ta fada tana kaiwa zaune hadi da zarro ido Fadime da ta ji kamar zaninta zai kunce ya fadi dan tsorata ta tare a rikice ta maka kofar ta rufe ta karaso itama ta yi zaman yan borin a kusa da kanwarta Muryarta a raunane ta ce" Anya kuwa zata iya aikin nan? Innalilahi mun shiga uku,sunnan UMUGHLUK ne fa NADIRAH!" NADIRAHN ta tsare su da kallon mamaki, sunnansa? Haramun ne kamawa hala? Tsuru tsuru ta yi tana jin yadda mahaifiyarta ta cenza yare zuwa buzanci take fada makar zata ari baki, sannan ta nuna masu kofa ta kore su ita da Innarta, domin ba zata bari NADIRAH ta saka mata hawan jinni bs! Daga wannan ranar Nadirah ke gannin abin takaicin da ya fi kona mata zuciya Yarinya karama, ko wanka sai an cudata Sau biyu tana satar jiki da nufin zuwa ta cudata dan ta ci uwar babanta a bayin ana kamata a hannata zuwa! Yarinyar kan mike kafa innar birni ta murza mata Abubuwa dai da duka saka ta tsani sarauta!, Sai dai kashhhhh.....lamarin normal ne Fadime dai baiwa ce, Bahija kuwa yar sarki ce Yin hakan ba laifi bane, idan babu rashin mutunci da wulakanci, domin Bahija ke sanye da alkyaba, ita kuma da hijab irin na bayi. Kwonci tashi har ya zamto daurin aure za'a gabatar a gobe ranar asabar a sabuwar shekarar musulunci Cikin gari ya dauka, domin baki sun karaso an sauke su a manyan hotel da manyan gidajen masarautar Baki ne na gani na fada, baki ne masu daraja, domina ciki harda CHEIK wanda ke rike da sadaki, duda zuciyarsa cike take da zulumin rabuwarsa da UMUGHLUK ITIFAL, domin irin abinda UMUGHLUK ya nuna masa kamar auren nan da wata manufarsa ya amshe shi, uwa uba ya dauki Gimbiya da Auta sun tafi kauye wai, abinda bai taba yi ba, Umma kuwa itace ja gabar matan da zasu amshi yar sarki a matsayin matar UMUGHLUK ITIFAL su sadata da dakinta........................ Cikin masaurauta kuwa karya karyar da ake yi kai zaka yarda cewa eh lalle Bahija ake aurarwa idan ka gani, domin kai da fata baki da bayi sun mayar da hankali sunna gabatar da nasu kalar shirye shiryen aurar da yar tal , kwalin kwal yar gata yar sarki wa baban Sarki, wa zai bari a barshi a baya? A cen cikin falon mai martaba kuwa su uku ke tsaye, magana suke tamkar zasu kashe kansu, UMMA, SARKI, GIMBIYA Rai bace ya warci alkyabar da Gimbiya ke bashi wace za'a lulube NADIRAH da ita ya juya ya fice ta cen hanyar dake boyayiya a gidansa ya shiga motar da munafukin amintacensa ke jiransa suka dauki hanya............ A cikin falon kuwa UMMA ta maido dubanta kan GIMBIYA rai bace ta ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 2 Rai bace Umma ta ce da Gimbiya" Me yasa kuka cika yin sake da lamarin ASADEEK?, A kan me zaku yarda maganar nan ta fita daga bakunnanku? Dole sai kun sanar da wa'inda ke kasa da ku abinda yake faruwa?, Ashe karfin mulkin da kuke da shi a garin nan ba mai karfi bane da sai kun sanar da bayi da mutanen gari uwa uba mutanen dake karkashinku sunna cin shinkafa abinda yake faruwa?, Yanke hukunci naku ne, su kuma yin biyaya nasu ne, basu da zabi, basuda abin fada!, Ki san kin saka an yi yadda za'a yi da wa'inda suka san ainahin maganar nan, domin ba zan taba yarda maganar nan ta fita ba da sunna na a ciki!" Itama gimbiya cike da tashin hankali da kuma bacin rai ta ce" Ki daina yi min ihu a kai malama!" Da gautsi Umma ta ce" An maki ihu me zaki iya yi? Na ce me kike iya yi dan an maki ihu?" UMMA ta fan matsa dan har yawu Gimbiya ke patsa mata irin ranta ya yi mugun bacin nan Murmushi ta yi tana kare gaban fuskarta tana kallon Gimbiya, a tsanake ta ce" Ki tambayi mijinki girman darajata a zuciyar UBAN GIDANSA!, ki kiyayi hawa kan abinda baki sani ba, ba kowani bori ake yiwa dirar mikiya dan a sauke ba, wata jarabar ta fi karfin mutun sai dai Allah, Ki tsoraci baiwar da ta zamto Uwar sarki, ki sani kafin ta kai matakin sai da ta kawar abubuwan da ba zasu irgu ba......., Ta saka zuciyar sarki tafarfasa kuwa abu ne mai sauki GIMBIYA!" Daga nan ta koma wajen zamanta ta harde kafa tana jiran dawowar mai gidan Gimbiya haka take huci kamar zata fashe dan bacin rai, itama ta koma ta zauna tana sake cije lebe, wai wannan matar ce zata ce a kan me aka bar y'arta a cikin garin nan kuma aka barta da waya? Lalle itama bata san me take iya aikatawa a kan y'arta mace cilo ba! __________________________________ Da sauri ya karra shigowa ya kuma kallon matarsa dake tsaye a kofar bayi, a tausashe ya ce" Fisabililahi Innarta ace tunda asubahi nace ta zamto a shirye sai yanzu da mai martaba ke filin gidan nan ace min ta shiga bayi? Mai martaba ne ya zo daukanta ba aike ya yi ba fa" Itama yannayin fuskarta a dan rikice ta dube shi, ta sake komawa kusan bayin ta tsaya ta sake kwonkwasawa a hankali ta ce" Indin innarta, shin ba mun gama maganar nan bane da ke? Ki fito mana Indin innarta ko cikinki ne ya kunce?" NADIRAH dake tsaye ta sake hade bayanta da jikin kofar ta yi shiru, bata amsa su ba Mahaifiyarta ta fita da sauri ta janyo hannun HINDU dake kuka kamar zata mutu dan rabuwa da NADIRAH ta dungurota ta ce" Ba mun gama magana ba? Ban san me kuka tsara ba ki ce mata ta fito Sarki ke jiranta fa?" HINDU ta ja hanci ta cire kai ta ce" Ace, kamar yar da aka tsinto a jejin sambisa? Kowa na tsoron kar aje yar oga ce ta giga ta zama oga? Haba dan Allah ku ce masa a je da ni mana, fin karfin a ya yi yawa, banfa ce zan bita gidanta ba, ama a je da ni har a daura auren azaluman su tafi da ita mana ina tsaye ko?" Da takaici FADIME ta budi baki zata balbaleta da fada Abanta ya dakatar da ita ya ce" Ki je ki ce gatanan fitowa bara na bambare kofar tunda ba zata fito da laluma ba, ke kuwa Hindu Allah ya shirye ki" Kasa motsawa ta yi, ta je wajen sarki ita?, Har sai da Aban NADIRAH ya sake waigowa sannan ta fice da dan sauri ta fita Wajen motar ta nufa tana ta addu'a a cikin zuciyarta ta dan tsaya daga wajen direba zata buga sai gani ta yi an bude bayan da wannan kallon nasa na wuce gona da iri ya yi mata murmushi ya ce" Bata son rabuwa da ke ko Fadimata?" Da sauri ta ja baya sannan ta duka kasa gaba dayanta kanta a kasa ta furta" Barka da warhaka Allah ya karra maka lafiya" Ido yake kallonta da shi kamar zai cinyeta, sai kuma ya yi murmushi ya kada kai ya ce" Ban taba jin bana so a min kirari ba sai a kanki, tashi dan Allah ki sanar min bata son zuwa ne ko?" Fadime ta sake sadda kanta ta girgiza kanta da sauri ta ce" Allah ya karra maka lafiya wace ita zata ki bin umarninka? Allah ya hucii