← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 87

Sashe 40

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

girman dake kanta fa, bana son abinda zai zamo tsegumi da tsuguri tsoma a cikin bayi, bana so kuma wancen ta yi tunanin ta samu hanyar da zata iya shiga tsakaninta da UMUGHLUK, uwa uba shi din da kansa idan ya fuskanci akoy maganar raini sai ya tsireta walahi!" A zabure HINDU ta zarro ido , lokaci daya ta ce" In sha Allahu Bama za'a kai cen ba, yanzun ma sharin shedan ne, yar da bata cewa komai? Yar mai tsantsar biyaya? Na tabata rashin fahimta ne, yau zan kwana ina fada mata kuma zata dauka, a yafe mana ba zamu kuma ba" Umma ta tabe baki tana sauke ajiyar zuciya, tabas yarinyar nan kamar ta mata ila ita din da kanta, a tunaninta yau da wata ce daban ta aikata haka ba wace take ji har kasan zuciyarta ba, da bata san abinda zai iya faruwa ba walahi! Juyawa ta yi tana fadin" Zan koma bangarena kafin ya gama sallah na koma na bashi hakuri" Inna ta gyada kai tana kallonta har ta bacewa ganninta Tagumi ta rafka tana sake kiran sunnan yarta da fadin gwara ta bude kofar nan su fuskanci junna , ita kuma ta yi shiru ta ki fitowar, domin a muryar Innarta tana gane bata sauko ba, idan ta sauko sa yi maganar Bayan sallar isha'i da kyar Umma ta samu komawaa domin baki ya yi a irin lokacin, sai dai tama zuwa ta sha mamakin gannin Auta har yanzu bata tashi ba Zama ta yi ta shiga gabatar masa da lamarin ta fuskar rarashi da ban baki, ta karashe da fadin sakon sam na daga wajen sarauniya ya fito ba, wata kula kula ce, in sha Allah tana kan bincike dan ba zata yarda a fara kawo wargi a gaban danta ba Murmushi ya yi yana basar da maganar, sannan yana karra gannin girman Umma a zuciyarsa, domin irin yadda take tsaye a kan lamarinsu ko iyayensa sai hakan, shi fa tausayinta yake ji baiwar Allah, ya tabata yakinta na ta kawo yarinyar cen gabaansa ba komai bame sai dan ta samu yan jikoki abinta, baban mafarkin Ummansu ta ga yan magadan sa, bata san shi bama zai kwatanta wani abu da yarinyar ba bale har ya dauki wani nauyim zuciyar, kai shi koda ya warke gaskiya da wahala ya tara zuri'a da yarinyar, dan sam bai ga tarbiya a tare da ita ba, irin yadda ta nuna din nan a saudiya ta bashi mamaki, bai taba tunanin akoy irin haka a hausa ba, abu kamar rainon arne? Sai da intacen bawansa ya daka mata tsawa fa a lokacin da ta ga dakinsa ido rufe ta nemi kutsawa da neman fado masa a jiki, bata san ba gidan ta samu ba, yanzu da wani lalatacen ne shikenan ta fado gidan sauki zai murjeta son ransa a bagas, ita a tunaninta soyaya ce sai ya bace mata batttt, kai shi yauma zai kunna wayarsa da ya bata layin, dama bai kunna bane saboda so yake ya huta sosai saboda abokan kasuwanci, layinsa ne sanane wa yan kasuwa kadai, Umma ta yi murmushi tana kallon Auta ta ce" Babyna kin yi sallah kuwa?" Auta ta dago a dan tsorace, dama tunda ta ga Ummar hankalinta ya kasa kwonciya ta tabata sai ta mata fadan ba ta hannata jimawa wajen Aba ba Da sauri ta gyada kanta, sai kuma ta bude bakinta dake dan rawa ta ce" Dama harda ce zan yiwa Abah, shine, shine na jima" Umma ta yi gagawar tareta dan karma ya saka wani abu a ransa ta ce" Aa ai karatu ba komai Auta, dama bana so kina jimawar ana ta hira kuma ki je baki samu isasshen barci ba , hakan na taba lafiyarki, idan kin gama yanzun tashi mu tafi na gyara maki komai ki sha maganinki ki kwonta" Auta ta budi baki har tana dan hardewa ta ce" Ummah, ban gama ba, dama so nake na yin, kuma na sha maganin a gaban Aba yanzu ko Aba?" Daga rubuce rubucen da yake ya dan dago ya gyada kansa, sai kuma a takaice ya ce" Zan rakata idan ta yi Umma" Dan zuba masa ido ta yi ta ga hankalinsa ya dauku a abinda yake rubutawa Wani irin harara ta watsawa Auta sannan ta yi kwafa ta mike ta yi masu sai da safe harda jadada a yiwa Auta addu'a fa idan zata kwonta Bayan tafiyar Umma Auta ta jima tana kallon waje daya fuskarta na nuna alamun she is sad Sai kuma ta sake tino maganar dazu Ita abin ne ya sakata dariya ba dan komai ba sai tino maganar mahaifinsu da in dai yan tsokanarsa suka motsa ya kama adabar mhaifiyarsu da maganar kennan, a kan rikicin da suka sha tsakaninsa da ita dan aurwn hadi ne su a lokacin, kuma ita mahaifiyar tasu itace Auta, ya zamto tsaf take cewa ba zata je gaishe shi ba gaskiya ta gaji, shi kuma a lokacin eh lalle an bashi mata ne, ama farat daya ya ji du duniya ta masa iya yi, haka yake sabo babar rigarsa shi ya je ya gaishetan, ko ba komai ai halal ne, to mahaifin nasu ke anfani da haka ya yi ta tsokanar mahaifiyarsu ita kuma tana sinne kai tana dariya, summa sunna shaan dariya da mamakin wai du girman sarauta irin ta mahaifinsu dama zai iya aikata haka? Zai iya tashi da kansa ya tarda iyalinsa? Kwarai so wani abin ne mai girma Kara sakin murmushi mai sauti ta yi, wanda ya saka yayanta dagowa da dan sauri ya tsura mata ido ya na dan kallonta da byron dake hannunsa Dariya ta yi har sai da jerarun hakoranta suka bayana sannan ta mike ta koma dan kusa da shi kadan da hannunta ta shiga nunawa ta ce" Abah, kana tune da labarin Papah da Anna?, Papah yace a gaban dogarai da fadawa nake saba babar riga na kai gaisuwa dan idan ta kiya tsaf zata ce ai itama mutun ce kulun kulun sai dai ita ta wani zo ta gaisheni?" Rawanin da bai sauke ba ya samu kansa da yi masa kasa sosai har habarsa ta bayana, Dariyar da kanwarsa ke yi da tsohon tarihin da ta tuno ya daka shi jin kamar numfashi ya masa kadan dan farin ciki A hankali ya saki lalausan murmushi, domun ya gane da me take hada zancen, sai kuma ya dan karra kure fuskarta da ido kasa kasa ya ce" Auta, ita fa ai ba irin na su Aba bane ba fa" Auta ta dafe habarta ta ce " Abah, sakon naan daga wifey dinka ne, Allah ma ko" Ido ya zarro da mamaki ya ce" Noh,kar ki rantse Auta" Auta ta sake sakin yar dariyar da ta saka Yayanta lumshe idannuwansa yana mai godiya ga Allah, uwa uba ya shiga tunnanin kennan akoy sauran dariya irin haka a tare da ita?, Ya Allah kennan tana da sauran tarihi a zuciyarta da kwakwaluwarta? Kennan kanwarsa bata shige cikin duhu gaba dayanta ba da sauranta? Auta ta kara dubansa ta ce" Abah, ka bada dama a kawota gobe sai mu gani ka ji? Please Abahna ni ina soma na ganta plz" Idannuwansa ya kankance, sai kuma ya gyada kai yana murmushi ya ce" Me yasa kika damu haka Auta bayan baki santa bama?" Ya yi tambayar ne dan ya gane idan har ba kanwarsa na neman shakuwa da abar da yake da takaitacen zama da ita a zuciyarsa Auta ta yi murmushi ta ce" Abah, ina son mutun mai karfin zuciya, mai courage, in dai daga ita sakon nan ya fito nima ina saka ran wata rana na yi karfin zuciyarta, Abah Kaine UMUGHLUK ITIBEL sunnan da talaka ya baka , kuma sarakai suka amsa, ba kai ka sakawa kanka dan isa da fin karfi ba, du wanda ya aiko maka da sakon nan, ko ita, ko ba ita ba i swear ina son ganninsa Abahna" Murmushi ya yi shima, sosai mamakinta na neman hanna shi yin abinda yake yi, Idan har zai tuna rabonsa da gannin haka daga Auta gaskiya an jima, irin mugun jimawar nan, murmushinta kansa sai a jima bata yi ba, bale dariya? Kai ko hira ake yi sai ka ga kamar bata san me ake cewa ba, ashe tana iya doguwar magana har haka hankali Kwonce?, Shima sai ya samu kansa da son yi mata abinda take so din, dan haka cikin nutsuwa ya ce" Ohk ohk, zaki gani yarinya da ba ita ta bada sakon nan ba, zaki gani, ama ba gobe ba, gobe da jibi inada zama a fadamai tsanani, inada Shari'a masu tsaurin gaske da rikici a ciki, in sha Allah ranar asabar alhamis sai mi zauna one 12 mu ci abinci tare?" Da farin ciki Auta ta amsa har ta karra bashi wani mamakin ta ce" zaka cire Rawaninka?" Da mamaki ya dubeta ya ce " *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 2 Da mamaki ya dubeta ya ce" Me ya kawo maganar cire rawani kuma?" Auta ta shagwabe fuska ta ce" Please Abah, idan ka yi haka zan ji dadi sosai fa?" Murmushi ya yi ya mike yana fadin" Oya maza miko ki yi hardar na raka ki dare na yi fa" Ajiyar zuciya ta sauke ta dauko ta mika masa sannan ta gabatar masa da hardar shi kuwa yana sauraronta har ta gama Yana murmushi ya nuna mata hanyar da zasu bi ya rakatan sannan suka dauki hanya Har suka karasa kowane na tunani a zuciyarsa Shi yana mai karra godewa Allah da tunanin ai idan hakaa ta ci gaba da samuwa tsaf zai mayar da ita wajen mijinta, sauki ya samu Masha Allah, dama a gaban Umma ta yi hirar nan a sake, da Umma ta ji dadi aa ranta Auta kuwa sunna tafe tana tunani kamar haka' shikenan kai ba zaka bude fuska ba sai kaa yarda da mutun? Na ga ai itama matarka ce, maganar yarda kuma ai ya kare ko?, Abah ban santa ba, hasalima ian tsoron iyayenta domin nice kat cewa summa da wani saka hannunsu a lamarinka,
Chapter 40 · 0% Book details