Sashe 57
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
taa gyada kanta kasa kasa ta ce" Ama dan Allah idan an kawo maganin a yi dabara kar innata ta gane" Murmushi kawai LUBNA ta yi , sai kuma ta dauki hijabinta da nikaf dinta ta mayar tana gyara kayanta ta ce" Barana na koma da kaina na amso na kawo maki" Itama ta ji dadin haka , dan haka ta kilacewa LUBNA kayanta a cen cikin adaka ta juyo tana tafiya a hankali sai ga Innarta ta sake faduwa hannunta dauke da kwano yana tururi , watau hanji ne aka rababaka ya samu dahuwa mai daraja yana ta kanshi da tururi Direwa ta yi a gabanta tana fadim" Yi maza rarabakeshi da zafi zafinsa zai fi warware maki yan hanji, yauwana bayin cen akoy irin bahon bayina na wanka ko? Ko sai na dauko katuwar roba?" Naman ta dauka, domin yinwa take ji sosai , saima da ta ganshi ta ji yinwar ta sake sheda kanta ta janyo ta yi bismillah ta fara motsa shi tana kallon miyar da tunanin dama ace ta samu nono ne, da ta morw walahi, ama abin nan idan ka ci ai nauyi zai maka a cikinka sosai Innarta kuwa bata tsaya kulata ba ta shige tana dudubawa Jim kadan ta fito tana kama haba ta ce" Ke bayinki ta fi tawa girma ko me yasa?" Nadirah ta dage kafada tana raunar hanta tana kallon Innarta Wucewa Hindu ta yi ta fice a dakin ya koma kicin dan ruwan zafi ta dora tana gadin ruwan tana dariyar Auntunta, wai daga sanar mata abu sai kawai ta katse kira ta labe , gaba dayama ta ki yarda su yi maganar wai kunya, yo ita yau ai shagali nata walahi, abu ya fara kankama sunna shawara da matar SHEIK? Uhum, Ruwan na fara tafarfasa ta juye a katon bokici ta kinkima ta koma dakin ta wuce ta yi tsaye tana ta tunanin yadda zata tara ruwa a abin nan kamar yadda matar SHEIK tace Kai kawai fitowa ta yi ta koma ta dauko katuwar roba ta kai bayin ta zube ruwan ta sirka shi, ama fa da zafinsa walahi sannan ta fito ta yi tsaye kan yar cewar ta taso maza ta je ta shiga ruwa ta tara mata A wannanma sai da aka yi da gaske, sai da HINDU ta dage sannan Indi ta tafi, haka kuma wajen shiga ruwan da kyar ta iya zama domin ya mata zafi kuma Innarta tace walahi tana sauraronta idan ta karra ruwa zata shigo ta zaunar da ita Ziciyarta na mata suya, tana cike da tsoron shikenan, kennan Innarta ta sani? A haka ta yi ta gama ta fito da jalabiyar tasa tana kallon rigar da Innarta ta ajiye mata ta dha turare Hanci kawai take ja ta saka rigar ta haye saman gadon jikinta da zafi zafi tana sauke ajiyar zuciya Bata jima ba Matar Sheikh ta dawo da maganin innarta kuwa na biye da ita a baya dauke da jarka irin katuwar nan yelow tana murmushi ta ce" Ga nono Indi an turo maki " Ido NADIRAH ta zubawa nonon, innarta ta ajiye ta fita dan dauko abin zubawa A hankali Nadirah ta ce" Waye ya bada wannan nonon?" Lubna dake balo mata maganin ta ce" Daga bangaren UMUGHLUK ITIBEL ne aka kawo" Baki ta tabe bata ce komai ba, ita kuma ta bata na hadiyar ta sha da kyar sannan ta bara mata na shafawar ta tafi ta shafa da kanta tana sake jin kamar duniyar tai mata zafi ita kam, kamar duniyar gaba daya zata kifun mata ne haka take ji Dawowar innarta ya sakata barkewa da kuka , tana jin barci na fuzgarta ama ta riga ta faka garin rigima tana kallon Innarta dake zama tana sallalami da tambayar meye kuma ta ce" Inna, walahu ba zan iya karasa aikin nan ba, ba zan iya ba, gida nake so, innata gida nake s............ *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* '4 Da sauri innarta ta zauna tana ajiye abinda yake hannunta tana furta" Subahanalah subahanalah subahanalah, Indi gida kuma? Mun gama abinda ya kawo mu ne?" NADIRAH ta kwontar da kanta saman cinyar innarta tana wani hakin kukan tana fadin" Ba sai mun gama ba, dan girman Allah ki mayar da ni gida Innata, ba sai mun gama komai ba, kawai Allah zai kare shi, mu bamu isa mu yi masa kariyar komai ba!" Cikin sigar rarashi innarta ta saake tausasa muryarta ta ce" Ama, me ya yi zafi haka da baa wuta ba?, Kyan alkawari fa cikawa, me yasa mun taso mun zo har mun gano wani abu a zamansa da mutanensa zamu zubar mu tafi? Ai hakan ba daidai bane a tunanina, bamu yiwa kanmu adalci ba bale shi mu yi masa, haba kema Indi, me yake damunki ne wani lokacin sai ki rikice kamar ba ke ba?" NADIRAH ta lumshe idannuwanta domun kanta har sara mata yake yi, muryarta a cinkushe, barcin nan na fuzgarta sosai ta ce" Ban zo gidan nan dan wannan ba, Innata ban zo dan na lasance kazar cikin daki ba, kyan alatun dake zagaye da gidan nan baya cikin tsarin abinda ke iya sakani ni NADIRAH na ji zan iya zubar da komai da na gina na farin cikin rayuwata a nan ba!, Innata bana jin zan iya rayuwa a wajen dake zagaye da munafukai mafi soyuwa a zukatan masoyansu ba, hasalima irin haka ya saka nake guduwata wajenku, domin ban.........ban..........innata Aminnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnunnnnnnnnnnnnnnannnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnnn ........" Sadakawar muryarta, daukewar muyarta, da sakuwar jikinta da fitar numfashinta tamkar na dan jariri ya saka innarta lumshe idannuwanta tana sauke ajiyar zuciya da dauke hannunta daga saman kirjinta a hankali tana dan karra kallon Fuskar NADIRAH A hankali ta shafa gefen fuskar nata sannan ta mike kadan ta gyara mata kwonciya ta luluba mata abin rufa ta fice jiki babu karfi ta koma baban falo Tana zuwa falo ta tarar da Umma zaune tana amsa waya kafarta daya kan daya cike da gadarar nan Har ga Allah sai da ta ji gabanta ya yanke ya fadi, jiki babu karfi ta zauna saman kujera ta samu kanta da zubawa Ummar ido tanna kallonta, kallon nan mai kama da kana karantar mutun, kana son gane wanene shi a fasarar badininsa, irin girman waye shi ne a duniyar da ka ajiyeshi Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tana cire dubanta ta dora a kasa Tunda take, bata taba jin tsoro tsoro, firgici firgici, na wannan lamari ba irin na Yau Aminu? A yanzu da wannan gagarumin abu mai daraja ya wanzu, wanda yake abin a wuni yau ana sukuwa da dawakai a cikin fadar nan dan murna da farin ciki, abindaa take cikin tunanin shin yaya wannan bawan Allah yake cikin farin ciki aa yau? Dama tunda ta ji an fadi maganar nan ta cewa Yayarta walahi ita ta tabata lamari ne na sihiri, ita fa ba zata yarda bama ta tura yarinyarta gidaan sarauta babu tsari, mamakin da take yi, mahaifan HUZNAH a labarin da suke tsinta daidaiku ance shi sarki ya auri yar sarakai ne, yaya aka yi suka miko yarinya gidan sarautha baabu tsari? Rayuwar nan da ta zama abinda ta zama yau ko gidan wani dan karamin mai kudi ne ai ks nemi taimako a wajen bayin Allah wa'inda suka riki ayar Allah kan a karra baka daga hasken addu'a tsari dan yaron ya je ya zauna da nutsuwar zuciya, ba wai ta malake miji ko yin yadda aka so da miji ba, aa wannan fa karya ne, ita babu ruwantama da wannan, lamarin karyar?, Shirme ne gaba da baya bata cikin wannan tafiyar gaskiya, ama a yi gyara, a iya girki, a san tsafta, a iya girki, aa iya kisar gyaran aure da iya yiwa namiji hira, uwa uba talabarsa a fagen da daga ke sai shi ki sakashi ihun jariraima watau wannan na kuryar makogwaro mai kama da kukan tinkinyar nan du abu ne da ta rika da karfi take kuma gannin komai hali irin na namiji da ake kadawa ba zata saki wannan ba domin darajarta ce ta ya mace, namiji kuwa ya kada iya shegen mana, ai kowa da irin rawar da Allah ya bashi ikon takawa, in ba dan tsoron kar a mutu walakiri ya mumuke bawa a cikin duhu ba yan rabiya bama ai da ta bi bayan habu, yanna kada gangar tana ana bakace, Firgigit ta dago jin muryar Umma na fadin" Hajia lafia kuwa?" A hankali ta ce " lafiya kalau, na gaa kina waya ne" Umma ta sake zuba mata ido ta ce" Aa gani na yi ina ta magana shiru kamarma baki san ina yi ba?"" Inna ta kade maganar tana yin dan murmushi da daukar kafarta daya ta dora saman daya tana ji a ranta inama idan ta rufe wannan abar da duka za'a gane yarenta? Umma ta sake fadin" Cewa na yi, da nace ba zan ringa yawan shigowa ba, dan na fahimci hakan da nake yi yana hadasa mana rashin jituwa, to ama sai na ga yau gaba daya du irin tsayuwar nan da muka yi a kofar mai baban fada bata leko ba, bayan HUZNAH na tsaye tunda safe sai da wancen munafukin ya sanar mana lafiya kalau muka watse, kin san gidan nan ko me kake yi a ido kake, ana binka ne da kallo ana fahimtar me kake yi, ta haka kake shiga ran bayi idan suka ga mu'amalarka da uban gidanka, ta haka manyan barori ke baka daraja har su ji du duniya kaine uwarsu, mu da muke so mu siye kowa ai ba zamu yi wasa da irin damar nan ba, koda nace zan fita a harkar matse mata waje dan na ga yana neman hadasa mana rashin jituwa, ama dole na ringa lekowa idan ta kama dole, domin na ringa sanar mata manyan sirika irin na sarauta wa'inda bakon gidan nan ba zai taba sani ba" A hankali Inna ta dauke dubanta tana sake tausasa dubanta a kanta ta ce" Hakane, ama sai na ji har kamar hankalina zai tashi da jin wai zaki ja baya dan dan abu