← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 87

Sashe 12

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aminu ya balle jama'a mun shiga uku, Nadirah mata saman kanki ga inna nan tafe Cmmnt, sabon posting *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 0 Raf Nadirah ta yi da hannunsa a lokacin da ya sake nufar aljihunsa ta tsayar da rawar tana kallonsa ta ce" Kai Aminu kudin nan fa? Ko kijmashin ka fara?" Sai a lokacin Aminu ya tino a cikin wani kudi ne yake baje kolinsa Idannuwa ya zarro ya kalli makadi, makadi ya kalle shi Gabansa sai da ya karra kwonci kwonci ya rufto, sai dai lokaci daya ya ji wani karfi ya zo masa a lokacin da amininsa Adamu ya dafa kafadarsa ya ce" Kai daya kake tal gaya na Indirah ikon Allah, kai ja mata ja mai dogon hanci kaine zaka haifowa dan mai gari mata gaba gaba kauyen LABA tafin hannunka mutumena, dole ka yi jarumin gwarzon kauyen LABA kai daya gaya, ko jaka dari ka zuba a rawar nan ta yi elhajina, idan baka daka da karfi ba watarana a gaban idannuwanka za'a cireta, nake fada maka Indirah ba karamar kadarah bace tanadinta mayar da kudi gida ne" Daria ya yi yana gyada kansa ya kalleta ya ce" Saki aljihun mana Indin Aminu?" Nadirah ta girgiza kanta ta ce" Wasa kake Aminu, kudin wa ka samu kake bararwa haka? Kardai na shago ne kake yiwa barin mahaukaciyar nan?" Kamata Yar dubu ta yi ta jata tana fadin" ke zo mu tafi, mu je mu je ga cen su hansatu sun kaure da fadan karin da Aminu ya yi, wai Hansatu ce take fadin a da fa Aminu ita ya so? Mu za'a kawowa bidi'a? Sun ha Aminu ya yi kudi za'a fara kawo masa hari ko? Aminu na INDIRAHn Yar dubu ne ba wata shegiya walahi!" Sakinsa ta yi tana kunce dan kwalinta ta ci damara ta ce" Ta samu , mu je, yo a kan Aminu in dan ni a kwana ana tseren rai a garin nan, sai gobe masoyi....." Daga nan wajen fadan nan suka je aka casu da su, Yar dubu kam ta jigata, ita kuwa ta sha dukewa domin ba zata yarda a lalata mata fuska ba gaskiya, da kyar suka raba kansu da kansu suka raka kuma tare ana tafe ana zaurance da yade yaden magana har kowace ta karasa gidansu ta shige *Safiya maraicen kura in ji yan magana* Bankadowar kofar gidansu ya sakata sakin tulun da ta nada gamo ta dora a kanta dan ta je ta dibowa Innarta ruwa a rafi Butar da HINDU ke kuskurar baki ta ajiye tana tafa hannayenta ta ce" Zan ga annabi idan na yi hali na gari, yanzu Indirar inna ba zaki daina kashe min tulu ba? Kin san tulun nan mu uku muka yi jayaya a kansa dan yanada saurin sanyaya ruwa? Kin fashe shi Indirah saura wancen na babanki shima ki dan dauko ki maka a kasa sai mu huta!" NADIRAH ta hadiyi yawu tana dake kasa kunne tana jiyo muryar innar Aminu a kofar gidansu Dam dam ta karaso ta rage murya ta ce" INNATA kamar muryar Inna Aminu fa, bakya ji tana fadin idan bai shigo ba zata muka masa faskare?" Kaffafuwanta ta janyo da kyau ta yi zaman yan makaranta tana kallon NADIRAH da sin karrin bayani, me kuma zai kawo innar Aminunta a karro na biyu gidan nan? Mema ta aikata to? "Allah jikanmu!" Innar aminu ta fada a takaice ta daka hannunta ta tankado keyar Aminu ya yi taga taga ya dake dukawa kansa a kasa , kana kallon gefen fuskarsa ka san ya maru bawan Allah Ido Hindu ta zarro ta zabura ta mike tana fadin" Ke bani hijabi ashe siriki ne da asusuba ko hantsi bai fito ba da Innarsa, Allah ya sa alkhairin da ya saba zuwar mana da sanyin safiya ne ya zo mana yauma" Rai bace innar Aminu ta ce" Zaki fadi haka, zaki fada haka uwar yan cin amana da cin zali, to bara ki ji Hindu ni nan innar Aminu a kan wannan mai ido ya na mayun sai na tsine masa albarka, ace na bi kasuwani, na sha zafin rana, na yi dakan fura na samo kudina na dashe ya je ya zubawa wannan la'ananiyar? Ni kuwa ai aure da Aminuna da wannan y'a sai dai idan kasa ta birni idona, kai dan Ubanka ka amso min sauran cenjin a wajenta ko sai na jibga maka faskaran nan ka summe kowama ya huta?....." Ta karashe da tartsatsin ihun da ya saka Aminu sake sinne kai NADIRAH hankalinta ya sake tashi, ta karaso ta duka tana kallon Innarta da ta ja tana kallon ikon Allah, a rikice ta ce" Inna kar ki tsine mana kin ji? Nawa ne kudin sai na saka Abana ya bani na kawo maki idan ya dawo daga birni, sababima zai bamu, ama inna ku daina shiga soyayarmu ni da Aminuna dan Allah, ni bai bani ko taro ba ki tambayeshi, ki daina dukansa kin ga fa ya yi uwa igiyar leko a ruwa" Ai kuwa innarsa ta sake kifa masa mari tana hankade NADIRAH da gangan domin dama damar nan take nema A zabure innar NADIRAH ta karaso ta saka hannunta ta hankade Innar Aminu sannan ta shaki kwalarta ta daga hannu zata rufta mata mari ihun NADIRAH da Aminu ya sakata dakatawa Da ihu NADIRAH tana dira ta ce" Innata aa aa maman Aminu ce" Shima a haukace ya ce" Inna kar ki yi mari ta hannani aurenta na bi duniya kar ki yi" Lebenta ta dantse ta daki kwalar innar tasa ta shige uwar dakanta Cen kasan gadonta na karaga ta lalubo asusun mijinta ta zauna ta fasashi ta shiga irga kudin dake ciki Biyu ta raba ta fito da shi ta mikawa Innar Aminu tana kallonta ta ce" Asabe, ki ji tsoron Allah, ki ji tsoron Allah asabe, ki sanni Allah ya yi hanni da zurfafa soyaya ko kiyaya, sannan ya ce idan zaka yi soyaya ka yi dominsa, haka idan zaka ki bawansa ka ki shi dominsa, kar ki kasance mutun mai fitina da rashin son zaman lafiya, ki sani nima uwa ce, kuma yarnan da gatanta, ba shegiya bace, ba maya bace, ba barauniya bace, ba yar iska bace, dan rashin son gaskiya danki fa ya yi likin nan ba wuka ta saka masa a wuya ya yi ba, a duniya menene maza basa yiwa mata?, Na karashe maki magana ni nan na hanneta amsar sisin Aminu, ko rake bai taba siya mata ba, bata amsa , bata so , nace ta bari idan ita din matar aminu ce a gidansa ya ciyar da ita, bana neman kai da yarinyar nan, ban kasa rike abina ba, ki sani du abinda kike yi da amsu ziga ki ba masoyanki bane, domin baki tsaya a kan huja kakarfa ba sai wata bankadafiyar hujarki marr ma'ana, kin dage dan yarinyar nan ta cika kyau ko me? Shin ita ta halici kanta, idan zaki iya ki iya da danki ki hannashi shiga sabgarta, ni kuma na rantse da girman Allah daga lokacin da Aminu ya nuna baya ra'ayin indi ta fita a harkarsa kennan dan ki bar ganninta haka na isa da ita!, Sannan ke kin san daraja kike ci, kina min takakiya ki ci min mutunci har gidana ni ta sarkin makada ko?, Ba damuwa, idan har kika kaini bango nice zan tarda ke!, Ke kin san wacece ni, ina daga kafa dan na ga yara sun dage, aure kuwa ba'a yi masa haka, to bari ki ji na gama maki magana idan Indi matar Aminu ce kina raye ko kina cikin asa za'a yi a gama kina kallon yan dugwui dugwui a gabanki, idan kuwa ba matarsa bace du tsiya sai dai kowa ya yi hakuri, dan Allah kina abu kamar jahila, ki fice a gidan nan in ba haka ba, in ban cuje maki dan kwali na danna kanki a cikin ta murhun cen ba ni bace HINDU bace!" Gannin yadda Hindu ta farra hawa sama tana zarro mata ido tana neman dungure mata kai ya saka ta sake tatara kudaden da take jinsu da yawan gaske kamar sun fi natanma yawa ta karasa inda suke tsugune ta damki hannunsa ta ce" Tashi mu je, yau yau yau zan ga ubanka mu tsayar da magana daya fa yarinyar gidan rabe, yarinya na sonka kana janta a kas, tashi mu je" Kamar jansa take, a kan kaffafuwansa yake tafiya ama kuma kamar jansa take ya bita suka fice a gidan Hindu dake tsaye kallon NADIRAH take yi tana jira ta ga ta zabura ta bi su, sai ta ga ta share hawayenta ta mike ta dawo kusanta ta tsaya tana kallonta, sai kuma ta fada jikinta ta saki kuka mai tsuma zuciya tana cusa kanta cikin kirjinta Idannuwanta ta lumshe itama hawayen nata suka samu digowa daga gurbin idannuwanta, ta dagota tana kallonta ta ce" Kulan ya tafi ne ko? Kukan abinda mamansa tace kike yi ko? Yi hakuri yar albarkana kin ji? Yi hakuri ki daina kukan nan, na sha fada maki ki barsu du abinsu abinda Allah ya hukunta fa zamu gani a rayuwarmu kin ji?" NADIRAH ta ja hanci tana fadin" Ni yanzu na fara tsoron matar nan, ginnin da yake yi dakina da nata a hade suke, idan har ya gama ya tabata a gidanta zamu zauna makotaka, anya zata barni na rayu a gidan mijina? Imnata ko kaini zaki yi a bibila min fuskata na zama mai munin da take so? Ita in ba abinta ba ai nima ba wani kyan ne da ni ba tunda banida tsayi ko Innata , kuma na ji ana cewa mace idan ba tsayi batada wani kyau ko Inna?, Dan Allah ki kaini a bilen fuskata" Janta ta yi suka karasa wajen zamansu domin rana bata fito ba bale su je kasan shuka suka zauna A sanyaye ta ce" Kin san na tabata wata rana Innar Aminu sai ta kaunace ki, Allah zai saka mata kaunarki tunda batada dalilin tsanarki, kuma ba za'a maki bile bile a fuska ba, babu kyau fa
Chapter 12 · 0% Book details