Sashe 46
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ajiye maganar tana wana manyan idannuwanta zuwa tsarin falon mai masifar kyau da daukan hankali A hankali ta mike tsaye , sannan ta dakata ta juyo tana kallonta ta ce" komin jimawar zaki a dawa, cikin kogo a boye, ba zai hanna kuraye wadaka da kai kawo ba, idan har ba giga ya yi ba, sunnansa na loko , fili kuwa na kuraye ne, Yin girki ba laifi bane a tunanina, idan har ba iya sarafa abin bane ya zamto gagarare a gareki Allah ya karra maki lafiya" Daga haka ta sakar mata malalacin murmushi sannan ta juya ta fice daga falon A rikice HUZNAH ta mike tsaye tana kallon hanyar da NADIRAH ta bi *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 3 A rikice HUZNAH ta mike tana bin hanyar da NADIRAH ta bi ta fita da ido Daidai nan Bayinta suka dawo, ita kuma a lokacin ta shiga kai kawo tana kai yar yatsarta karama ta dantse a bakinta cike da jin radadi da rukuki a zuciyarta A ranta ta shiga ayana magana kamar haka' Kin zo gidan nan ne da nufin takani?, A tunaninki sangartaciyar inna nake wace ke ci ta bar kwano a nan yashe?, Lalle ba zan yarda ki zo gidana ki sameni da mijina ba ki fara kawo min tsare tsare, ni nan ni zan fara yiwa mijina girki kuma zaki samu gayata a yau ba sai gobe ba!' Fuska a hade ta bada umarnin ko me ake yi a je a sanar a baban kicin na bangaren mai martaba zata shigo kicin da kanta A zabure yar rahoton Umma ta dubeta, sai kuma ta sada, a tausashe ta ce" Allah ya taimaki uwar bayin Allah, me ya hada ki da girki? Fatarki ai ba ta shiga kicin bace, sannan Allah ya karra maki lafiya kin manta Maman Ja gaba ce keda wannan alhakin?" Samun kanta ta yi da tsare matar da kallo, idan har tana iya irgawa a gidan nan ai komaima maman Ja gaban ce keda alhakinsa, ciki harda hurumin da ya dace ace nata ne ita matarsa, ya dace ace Umma tana kula ne da abinda ya shafi abincin bayi, ta bar mata na mijinta ita ta kula da shi, ama ya zamto har mutanen da suke bayi a gareta sunna neman yi mata katanga da haka dan ta zubar da hakan ta yi watsi da shi wa wasu? Har ake ce mata fatarta ba ta shiga kicin bace dan aikata aiki mafi hatsari da kaiwa jiki irin na abincin mijinta? A dan kausashen da basu saba ganninta ba ta dubi matar ta ce" Jayaya kike yi da umarnina?" Da sauri ta sada kai, ta sake dukawa tana mai neman afuwa Da umarni ta ce" ki rike magiyarki!, Ki maida hankali kan abinda na saka ki, sannan ki je dakin sako a rubuta takardar gayata cin abinci a falon mai martaba, karfe takwas na dare, a turawa SARAUNIYA BAHIJA!" Daga haka dakinta ta wuce dayar ta bi bayanta da sauri dan fitar mata da dukkan abinda take bukata Ita kuma a lokacin tana fitowa sai da ta dokawa Umma waya ta sanar mata cewa wai HUZNAH ce zata zo Kicin na bangaren Sultan, A lokacin kuwa Umma bata jima da baro bangaren ba tunda aka sheda NADIRAH ta dawo bangarenta, ta zo tana son jin dalilin da ya sa Nadirar har ta fito ta je wani wajen ba da izininta ba Innar Nadirah kam, uffan bataa ce ba, har Umma ta gama maganarta, hakama NADIRAH kallonta kawai take yi har ta ajiye maganarta, a nan ne ta samu kiran nan wanda ya kusan sumar da ita Da tuhuma ta dubi NADIRAH ta ce" Shekara tara kennan yarinyar cen na masarautar nan, bata taba cewa zata shiga ta yi masa girki ba sai yau da kika je bangarenta? Me kika ce mata?" Da dan kosawa Nadirah dake bale dan kunnen kunnanta ta dubi Umma Lalle matar ta gama samun waje ne gaba da baya, ya zama wajibi kuwa ta bita a hankali har ta durmiyata a cikin ramin da ta haka da kanta Kai ta girgiza tanaiwa idannuwanta wani irin warrrr sannan ta dan yatsine fuskarta ta ce" Kin san menene burina?, Burina na gama abinda ya kawo ni gidan nan, na smau yancina, burina na aikata aikin da ake so na aikata na kama gabana, domin a waje inada rayuwata wace nake matukar son na ga na cika, ni nan da kika ganni burina na yi kudi na gagara, ai ba laifi bane ba kuma haramun bane yar kauye ta yi buri da mafarki ko? Ina iya ranste maki a kan kudi komai sai na aikata, wani yardar tawama dan na tabata za'a bani wani dan abin ko yayane na je na ja jari, ba kowa rayuwa take tafiyarwa ba a cikin daula kin fahimta? Ki yi hakuri zaki ji maganata wata iri kamar na raina ki, aa ba raini bane, kin daga hannu kin mareni ido da ido, ba'a yi min haka, ki sani da ba dan na san jakarki da nauyi ba da sai na maida maki goman wanda kika yi min!" NADIRAH ta ajiye maganar, da wani yannayi da ya saka innarta dagowa tana kallonta, domin tamkar wata rikakiyar yar daba ko irin rikakun yan barikin nan Ita da kanta Ummar shan jinnin jikinta ta yi, a lokacin abu daya ke ranta shine bata kyauta ba da har ta kai hannunta fuskar NADIRAH, ashe yarinyar tanada mafarki nata na kanta, gaskiya ne mai yawo a cikin mafarkin kudi ko mulki baya tsoron kowa, baya tsoron komai, a mutu ko a yi rai du ba shi bane a gabansa in dai yana irgen ta ina kudi zasu shigo Lalle ta yarda yarinyar na iya aikata masu aikinsu, ama duda haka bata ga dalilin da zai saka ta je bangaren HUZNAH ba, har maganar nan ta fito fili haka ba gaskiya Umma ta dan dubi Inna, sai kuma ta sake kallon NADIRAH, ta dan rage gautsin Muryarta ta ce" Kema kin san marin nan dan raina a sama ne, ni na mareki ama ni na ji a zuciyata" Ta idasa tana mai dora hannunta daidai zuciyar tata A dole NADIRAH ta kalli innarta, da sauri kuma ta kalli Umma Umma ta ce" Ama kawai ki yi hakuri, ba za'a kuma ba, yanzu ki fada min me kuka tatauna da wancen ne?" Tabe baki NADIRAH ta yi, sai kuma ta cirw kanta ta ce" idan ta hanyar da nake tunanin za'a bani aikina a gidan nan ne na yi sharar fage, dan ya zamto an samu abinda ake so ba da labe labe ba, dan kuwa in ban samu hanyar yi masa girki ba, hakan ba zai tana samuwa da sauki ba, ina fata kina gane yarena" Wani irin farin ciki ne ya ratsa Umma Har ta rasa me zata ce a irin wannan lokacin Kiran dake ta shigowa ya sakata mikewa ta masu alamun sai ta dawo ta fice domin a cen kicin din ne ale ta kiranta, Kai tsaye ta je, tana jin ba'asin kiran ga mamakin HUZNAH sai Ummar ta bata damar dafawar hankali Kwonce, duda dan abin da ta saba sakawa a irin abincin auta yai ba zata saka ba kennan? Ama zata yi hakuri har gobe Girkin NADIRAH A dakin NADIRAH Umma na fita Innart ta dubeta, da duba irin na karra son gane gaskiyar lamari Sai kuma ta sauke numfashi ta ce" haka nake so, ina matukar son idan kina magana ya zamto tana sauraronki, dan karfin muryarki ya fi nata zafi?, Haka kuma ina fatan Allah ya nuna min ranar da zan rama marin nan, walahi ko ana ruwan mazuru da zaho sai na zabga mata mari in sha Allah, Kwartuwar bamz da wofi, wai zuciya, ina ta ga zuciya wancen?" NADIRAH ta yi murmushi ta zauna tana tunanin idan har hakarta ta cimma ruwa, matarsa zata amshi girkinsa, hakan na nufin za'a rage wata jarabar, idan kuma an kawo maganin da za'a zuba masa a abinci hakan na nufin ita za'a ba ta zuba, ba Umma bace zata zuba abincin ita kuma a bata ta kai masa!, Ko ba komai Abam su Inna za'a dan karra kwanakin shiruftaka bawan Allah!............... Kusan sallar magarib takarda ta sameta ta gayata cin abinci, wanda a kusa kusan nan Umma ta fada masu da wahala ta sake samun zuwa falon UMUGHLUK ITIBEL sai idan ya huce Murmushi kawai ta yi ta ajiye abin tana sake karantar girman girmama abu irin na gidan sarauta, zo ki ci tuwo ne aka buga a computer? Watau tvn nasara? Allah shi kyauta Da dare ya yi sai da larfe takwas din ta kusa ta shige wanka, a nutse ta fito ta bude tarin kayan dake sakata nishadi idan tana kallonsu ta zaro wata doguwar riga irin ta kantin nan ta zaman cikin dakin nan mai laushi mai ruwan fatar kare ta ajiye, sannan ta dauko pant shima fari kal shi kuwa ta ajiye Bangaren alkyaba ta bude ta zuba masu ido A hankali ta dora hannunta ta ringa shafasu tana kare masu kallo A kalla zasu kai talatin ko fi a irgenta,haka kuma kowace da irin yannayinta, watau da tsarinta da kyanta da komai Ajiyar zuciya ta sake saukewa a hankali ta janyo wata mai ruwan gashin mage, laushinta da dukan da ta yiwa kirjinta ya dakata daukota domin tana kallonta sai da ta ji ta sace zuciyarta, haka kuma tana daukota a hannunta ta ji wani laushinta sai da ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya A hankali ta karasa wajen abin turaren wuta ta dauki abin kyastawar ta ciro ta kyasta daya ta dora ta dan dakata ya kama sosai har ya fara zama toka toka kadan , sannan ta je ta ciro turaran wutar na kaya ta zuba ta loda kayan Wajen madubi ta karasa ta tsaya cike da tunanin me ya dace ta yi? A hankali ta zauna tana dan dora hannunta sama ta shiga tuna maganarta da matar dake koya mata yannayi da lamura irin na sarauta A hankali ta maimaita kalmar da