← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 87

Sashe 55

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai ku fa hawayeni *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 3 Asalamu alaikum, oh , ku yi hakuri kun ji? Kira ne message ne , ku yi hakuri, ina cikin uzuri mai girman gaske ne, bana din yanke maku ko yi maku shirme, in sha Allah zaku jini a kai a kai da zarar hankalina ya kwonta, ga daya ba yawa Lebensa ya dantse yana mikewa ya ce" Ham bara ka gani!" Da murmushi Sheikh ya raka shi da kallo har ya bacewa ganninsa, sai kuma.ya maido dubansa kan matarsa da kanta ke kasa baiwar Allah Murmushi ya yi ya ce" Madam ya tafi fa dago kan mana?" Kai ta girgiza kasa kasa ta ce" SHEIK bashida rawani fa, ba zan dago ba ka rufa min asiri" Yar dariya ya yi yana kada kai bai sakata dagowar dole ba, domun ya san yadda mutan garinsa ke girmama shi, kuma dai buzu da nadi aka sanshi gaskiya Da isa ya bude ya shige dakin, sai kuma ya tsaya yana kallonta, jalabiyar da ta ce ba zata saka bace ta saka, ruwan milk Jalabiyar ta amshi kalar fatar jikinta, gashinta dake jike kuwa ya yi wani lufluf a gaban fuskarta Dan cire idannuwansa ya yi yana kallon bed din, yanna nan yadda yake, ya sake kallonta a hankali ya ce" Bafa inda zaki je!" A da ta ki kallonsa ne, a yanzu sak ta dago tana kallonsa, ido cikin ido Kai ta gyada ta taka a hankali ta bude wajen kayansa ta dauko jan hirami dake cikin ledarsa ta bude ledar ta yafa a saman kanta tana gunguni kasa kasa ta ce" Sai ka hannani tafiya!" Kai tsaye ta tunkaro shi, ko nace ta tunkaro hanyar fita, idannuwanta tar cikin nasa, duda tafiyarta dake murgudewa , da azabar da take ji bai hannata dantse lebenta tana masa hararar da ita kadai ta san me take rayawa a ranta, abubuwan kuwa sunna da karfin da a gaskiya ba zata ji tsoronsa ba, jama'a Aminu fa ya sa ta ci amana, Aminunta me zata cewa duniya? Me zata cewa Aminu? Innalilahi wa inna ilaihi rajune Sai da ta zo daf da shi, face da shi, tsayuwar da ta zamto tamkar zata shige jikinsa, ta dago kanta ta sake zuba masa ido kamar yadda yake kallonta da mamakinta, walahi yana matukar mamakin halayanta, ya rasa a wani bigiri zai ajiye yarinyar nan, tunda Allah ya haliceshi bai taba dora magana aka ce da shi aa ba, yana iya cewa wani abin SHEIK kan dawowa ya zauna ya yi ta rarashinsa sannan ya ce da shi idan da hali da kaza ya dace a yi maimakun kaza, to fa ta haka yake samunsa, bayanshi ko Sheikh da yake amini na kud da kud da mahaifinsa baya yi masa haye, ama wannan yar itace ta masa tsaye kikam Shi UMUGHLUK ITIBEL kan sai ta yi abinda ya ce ba za'a yi ba? Idannuwansa ya lumsje, a lokacin da ya ji kamar gumi ke tarin masa a kofofofin hanci da habarsa A hankali ya dan goge saman karan hancinsa sannan ya kauce kadan ya jingina da garun yana kallon ikon Allah Ai kuwa kai ta saka tana dan dafewa a hankali sannan tana rike rigar, domin rigar ta yi mata bululum kamar ta zurma buhu, fadin da tsayin duka ta mata yawa, hiramin kuwa iya saman gashinta kawai ya rufe bai rufe sauran gashin ba Kai jama'a, yau yake koyan darasi, yau gashi ga fitsara gannin idannuwanshi, yace ba inda zata je ta je din, la ha ila ha ilalahu muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam Kai ya gyada yana daga kafarsa a hankali yana biye da ita, dududu da hannayensa fa sai ya dunkuleta walahi, a kasa take sosai tsayinma da takeda bata kawo ko saman kirjinsa ba, ama take masa kallon cikin ido A wajen saukar na karshe ta yi tsaye tana kallon wajen, domin wajen da dan tsayi gadkiya, idan ta sauko a haka sosai zata fi da jin azaba, kai in bandama kokari irin nata walahi kai sake ba zata iya wannan aiki ba, ama da yake tana da kokari gata ta sauko Daga tsayen da yake a daf da ita ya rage muryarsa sosai ya ce" Ama ai kin san bin miji aka ce a adinance ko ba wai na ringa binki ba ko?" Baki ta tabe tana karra dantse bakinta, mutumen nan ya ki ya gane, ya ki gane idan ta bude bakinta komai na iya fitowa, ya ki ya gane tana rufe bakin ne dan kar dan mutuncin da take tunanin tana da shi a idannuwansa su zube Gannin tana ta son ta duka irin zata zauna din nan sai ta sauka ya saka shi sake gyada kansa yana kifta ido ya zagaya ya mika mata hannunsa mai girma da fadin nan irin na maza da idannuwansa ya mata alamar ta zo Kadadarta ta noke tana hanna kanta fashewa da kuka Ido ya sake zuba mata, a sanyaye ya furta" BAHIJAHHH" "NI BA BA.................." Sai kuma ta yi dif da maganar , irin bara ta mantar da shi din nan sai ta yarda ta miko masa hannun A hankali ya janyoto jikinsa ya cicibota ya daukota gaba daya ya karaso falon da ita Kasa kasa ya ce" A bangarenta za'a dubata" SHEIK da kansa ke kasa shima ya saki murmushi yana sake sada kansa Kara cijewa ya yi yana dan sake tarota, hannunta na wuyansa kanta na kife a kirjinsa, jikinta kuwa zafi ne da shi sosai har huci yake bayarwa, A hankali ya nufi hanyar dake iya sadashi da bangaren nata yana tafe a nutse har ya kawo daf da kofarta Hannunsa ya saka zai bude hanyar ta shiga ta nan din ya ji dumi a gefen kuncinsa a hankaki tana fadin" Ka rufa min asiri ka ajiyeni a nan, kar innata tace na zama yar a zuba ido duniya ta bi da tofi" Dakatawa ya yi, Innarta? Mahaifiyarta? Ko me? Ya Allah, bai taba jin son sannin abu a rayuwarsa irin a kan yarinyar nan ba, yana ji kamar ya bude din ya shige din A hankali ya sauketa a kan kofar da ya san tata ce, domin kofofin hudu ne reras da ake dauka a karasa nasa falon Yana tsaye ta bude ta shiga ta rufo , a hankali ya karra kunnensa ko zai ji wani abu? Ama shiru bai ji komai ba dan haka ya juya jiki ba karfi ya koma falo NADIRAH na shigowa sai da ta cuje dan kwallin ta yar a nan sannan ta gyara tsayuwarta da kyar ta takarkare da karfin da ya rage mata ta fasa ihun da ya saka innarta dake zaune da redio a kafe a kunne tana jin labarin hantsi leka gidan kowa tana dariya da gyada kai ta kafa dauri da sabuwar atampa, domin tunda garin Allah ya waye ta tsinci sarki bai samu sallar asubahi ba ta kada kai ta karra zuba ido yar bata dawo ba ta haye ta tsala wanka ta rangada sabuwar atampa ta kafa dauri, ta tabata alkhairi zata ji da yardar ubangiji! Redion ta wancakalar gefe da sauri ta sauke daurin ta mike tana nufar hanyar da ta ji kukan yar tana salalami da fadin" Wayo ni ta Habu yar nan ina kika kwana?" NADIRAH dake kuka bilhaki a zaune dandabar hannaye kawai take watsawa tana cije lebe da furta" Hummmm, Humm" ta bi innarta da ido muryarta a kurya ta ce" Innata wanka kika yi?" Da sauri Hindu ta girgiza kai ta ce" Wane mutun, ina ni ina wanka, rasa yaya zan na saka atampar nan yanzu nake cewa na je wajen Wancen matar na nemi alfarmar ta rakani wajen Aban bayin Allah na fadi cewa kin bata, innaliwa shigana bayi ya fi a irga yar nsn, tashi mana" ta karashe tana lelen kafafuwan Indi NADIRAH ta sake barkewa da kuka tana kawar da kai ta ce" Ki daina ce masa Aba, walahi bai haifeki ba, ba aban innar birni bane, ba kuma na Aban birni bane?" Wayo dadi, wayo duniya da abin dadi take, da kyar innar Indi ta iya juyar da kanta gefe ta ringa sakin murmushi, yo jama'a in dai Indi ta ga fuskar UMUGHLUK ITIBEL ta yiwu komai ya faru, yanzu baban burinta ta mike tsaye ta dan taka, ta tabata komai kankantar halitar namiji idan ya ziyarci budurwa sai ya nuna, ah to, dan haka burinta ta ga aiki a bayane Da harare ta ce" Ke ba zaki daina yiwa Aban marayu rashin kunya ba ko?, Taso min mana wai daga zaunen nan, yaya aka yi kika biyoma ta nan, ko wancen matar ta rako ki? Kukan me kike yi? Wai wannan rigar ta waye, kuma yaya aka yi ta zo jikinki?" Kukan da take yi ne dif ya dauke, ta zubawa Innarta ido Yanzu Fisabililahi ina ruwan innarta da son sannin yadda aka yi rigar nan ta zo jikinta? Gaba daya sai take gannin kamar Innarta na yi mata wani kallo daban, irin na ta lalace din nan? Kai innalilahi wa inna ilaihi rajune _________________________________ Matarsa ya raka har kofar da ASADEEK ya kwatanta masa sannan ya dawo ya zauna yana ta murmushin da ya gaza barin lebensa Asadeek dake zaune yana dan shan tea din da aka kawo cikin breakfast ya dube shi ya ce" Sai watsa hakora kake yi SHEIK" SHEIK ya yi yar dariya yana gyara zamansa ya ce" Kai kuma dariyar tawa ce take damunka?" Dan shiru ya yi, sai kuma ya yi murmushi shima yana girgiza kai kasa kasa yace" Ban taba haduwa da tsageran da nake jin zan yiwa biyaya ba sai a kan yarinyar cen, cewa fa na yi ba inda zaki, ko irin tace min in barta dan Allah ta tafin nan, kai tsaye ta tunkaro hanyata idona cikin nata, gaba daya bata da kunya SHEIK" Dariya kam yanzu Sheikh ke yi tsakaninsa da Allah, shi dai a haife ya haifi ASADEEK, girma ne ya dame shi kai tsaye bawan Allah, hakan ya saka shi aron halaya irin na manya gaba da baya, ga halin
Chapter 55 · 0% Book details