Sashe 68
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
janyo hijab dinta a gefe ta yafa a kafadarta tana amsa salamar Auta Zama auta ta yi tana murmushi ta ce" Sannu aunty, ko na rayaki murzawar?" NADIRAH ta yi dan tsai tana kallonta, sai kuma ta girgiza kai ta mika mata dilkar ta juya tana fadin" Murza min a bayana to Auta, dan Allah kar ki darza da karfi jikina gaba daya ciwo yake yi, na san dan na yi sharar bangaren cen ne........." Auta lebenta kawai ta dantse dan gudun dariya kar ta kubce mata, wani irin farin ciki marar misaltuwa take ji yana taso mata, ashe ashe abinda ya faru kennan? Lalle dole yayanta ya zabura da NADIRAH ta fara ihun jinni a hancinta, dole du abinda ta aikata ya ringa binta da ido kamar ya ga bakuwar halita, dole ta siye gaba daya tunaninsa da motsinsa, ya salam wa zata fadawa wannan abin farin cikin? Bata da wanda zata fadawa, sai dai dan godiya ga ubangiji sai ta yi azumi daga gobe in sha Allah, tana gama shafa mata ta yi gaba tana tatare tataren kayan murje murjen ta shige bayi ta rufo bayan ta ce" Kainama sai na wankeshi sai kaikayi yake min" Ita dai Auta sai da ta ga rufowarta ta sake zamaa tana kyakyata dariyar da a kusa kusan nan bata ga abinda ya sakata yinta ba Mikewa ta yi ta bude window din dakin ta lumshe idannuwanta iska mai dadi na hurota, a hankali ta furta" Hakurin bawa keda wahala, da ace bawa zai jure da addu'a ya yi ta hakuri da tabas zai kai ga ci, Allah ka nuna min ranar da zamu rike dan jariri malakinmu a gidan nan..............." Sai kuma hawaye ya bale mata na tarin kauna da tausayin yayanta, harta Huznah sai da ta bata tausayi, shekara nawa tana tare da shi, shekara nawa tana jurewa tana daukan hakuri? Ashe abin a jikinta ne kuma ta yiwu a kansa ne kadai abin, ta yi sake abu ya riketa tunda yarintarta har shekaru sun fara taruwa a kanta, a yanzu idan abin nan ya bayana yaya zata ji a zuciyarta ne? Ga HUZNAH da baban kishi mai tsananin gaske, HUZNAH bata hada mijinta da kowa ba kuma ta so a rabar mata abinta, danma ta san bata da yadda zata yi ne ta hakura da wannan lamari, to ina ga ta ji baban abin nan? Subahanalah lalle akoy kura a baban daki! A cen kasan zuciyarta kuwa dodonta take kamaltawa, tana tinano irin abinda ke iya faruwa, idan ta tuna magangannun Umma a kan yayanta cewa shi da mace sai dau a lahira in ana badawa, shi da samun Da sai dai in ana haihuwa a lahira? Sai ta ji du duniya babu wanda ya yi asara irin mai hada UBANGIN SAMAI DA KASAI DA WANI ABIN HALITA KO GUNKI!, ya Allah ka karra durmiyar da mu a duniyar musulunci ____________________________________ Tabas, dukkan abinda ya dace a tarbi bako dan karama shi, an gabatar a tsaftace a kuma tsare, sai dai bakon nata tunda ya zauna zama irin na hamshakai bai kalli abubuwan ci da sha din ba kwata kwata, hasalima shi ba danna waya yake yi ba bale tace dannar waya ne, shi kuma ba wani abin yake yi daban ba gayanan dai a zaunen ya dake har wani tsoron sake gaishe shi take yi bayan irin ihun da ta sha da ta karanta sakonsa cewar gayanan zuwa gareta? Wayar dakin ta je ta daga, a dake ta ce" FATIME, KI KAWO WANI ABIN WANNAN BAI MASA BA" tana gamawa ta koma ta zauna ta sake zuba masa ido, Shi kuma ci kanki bai ce mata ba yana ta nazartar girman wautarta kafin ya dirar mata An dauki minti kusan goma a haka sai TV dake hasko yan indiya sunna soyaya, Fatime ce ta yi salama yana dauke da wasu plate plate na kwalba masu nauyi da kyan gaskw, kyansu zai sheda maka kudinsu ta kawo ta ajiye ta juya bakin kofar da baiwa ke tsaye tana amsowa tana ajiyewa a gabansa sannan ta duka muryarta a sanyaye kanta a kasa ta ce" Barka da yamaci uwar gijiyata, wadinne zan kwashe a ciki?" Da zafi zafin gannin jimawar Fatime din BAHIJA ta ce" Dillah tashi daga gabansa karki saka ya shaki karnin dati malama kin matse masa waje kina magana daf da shi kamar kin samu talaka dan uwan............................ Dif ta yi shiru sakamakon kakausan kallo, mai hade da tarin mamakin gannin wannan abin rashin da'a a gaban idannuwansa na wannan yarinyar karama tana wulakantar da matar nan da muryarta kadai ya ji ya fahimci ta girmeta ba tare da ya kalli fuskarta ba A hankali ya dawo da dubansa kan FATIME da kanta ke kasa ta rintse ido tana jin kunnar magangannun BAHIJA yar da ta haifi sama da itama ama dan tana aiki a karkashinsu take neman wulakantata har haka? Sake kallon BAHIJA ya yi, sai kuma ya maido dubansa kanta a hankali ya ce" TASHI KI TAFI" Tunda ya zauna sai yanzu bakinsa ya yi magana, hakan ya sa Bahija sake dubansa kirjinta na dokawa, gashi da ta so zama daf da shi kiyawa ya yi ya nuna mata kujerar dake facing dinsa wai a kiyaye shedan Fatimema a hankali ta dago kanta da idannuwanta jin magana a tausashe an yi mata ta sauke kan fuskar mutumen Fuskar ta yiwa tsai na yan sakwani sai kuma ta dauke da sauri sanadiyar gannin ya wani dan warra dubansa a kanta Kai ta sake sadawa a sanyaye ta ce" Allah ya huci zuciyarka, a huta lafiya" Daga haka ta mike ta juya da niyar tafia, Muryarsa ya sake budewa a hankali ya furta" Dakata " Fatime ta dakata, gabanta na tsintsinkewa ta juyo daga inda take ta duka ta ki yarda ta hada ido da shi sakamakon fuskar dake son yi mata yawo a ido wace ta tabata hade hade ne kawai Sake zuba mata ido ya yi kirjinsa na bugawa da dan karfi, sai kuma ya kawar da kansa da hannunsa ya yi alamun tana iya tafia Har ta bar dakin yana kallon hanyar da ta bi ta fita A hankali ya maido dubansa kan BAHIJA dake kallon abunda yake faruwa zuciyarsa na ta ambaton kamanin da ta ganni a fuskar matar nan Murmushin yake ya yi yana sako kalar serius a hade hade ya ce" Haka dama suke jinnin sarautar?, Basu da tausasawa wa mutun?" BAHIJA ta sauke ajiyar zuciya jin ya fara bata hankalinsa ta ce" Kar ka damu da wannnan, baiwata ce ai" "Dama a masarautarku ba'a daina bautar da bayi kamar a zamanin jahiliya ba? Ko bakwa girmama daraja irin ta dan Adam?" Ya fada a sanyaye, fuskarsa na fitar da murmushi, ama kuma bayanansa na suka Kwarai da tana da hankali da tun a nan ta fara gane wani lamari a tatare da zaki, yana magana a wajen da yake nata ne tamkar nasa hankali kwonce yana neman birkita mata lisafi Sai dai murmushin dake saman fuskarsa ya fi komai dauke mata hankali, dan haka ta ringa mayar masa da sakon murmushin itama tana ji a zuciyarta da ace zai amince ta dawo daf da shi da ya taimaka mata fiye da tunaninsa Cikin rashin ba maganar mahinmanci ta ce" Ita wannan din hasalima bata yi min ba, mun cika fada da ita, duda ta min wani dan kokari ta bada yarta auren da nake fada maka ni aka so yiwa shi, ama kwata kwata ba zata taba birgeni ba, bata da aiki sai son yiwa mutun fada kamar itace Gimbiya, a haka da ka ganta ba tsorona take ji ba, tana wani sasada kai tsaf take iya hada ido da ni ta gagaya min magana, abinda ka ga gimbiyama bata tsira ba bale ni?, Ka manta da batunta dan Allah ka sanar min, wai da gaske tafiyar nan tawa ce ni kadai?" 'YA SALAM......., YA SALAM, YA SALAM..............MMMMMMMM.......' yake ta ayannawa a cikin zuciyarsa, da kyar ya iya hadiyewa duda ya dan san lamarin, ama a yanzu da ya ga mahaifiyarta da kamaninta fa irin relation din dake tsakaninsu sai ya fara tunanin anya da son ranta aka yi kuwa? Dan kurmushi ya yi a saman lebensa ya ce" To ita yarinyar itace ke son auren sarkin ko?, Ke bakya so sam?" Cike da jin maganar wata ba ita ba zata dameta ta dage kafadunta ta watsa hannayenta ta ce" Anya kuwa?, Inaga biyaya ta yiwa iyayenta, inma menene cen ta matse mata ta je ta runguma ni kam bana so bana bukata me zan yi da wani bayan gaka?" Kallonta yake yi, ita kuma zuba take yi hankali kwonce har ta dasa aya tana kallonsa ta ji shiru bai ce komai ba kallonta kawai yake yana mamakin asarar mace har mace da aka yi a wajen nan, tap lalle ya tausayawa wanda zai iya kwasar wannan yar idan ta tsira da duniyar!, Ikon Allah yaya zaki ringa magana kina nuna wata biyaya ta yiwa iyayenta bayan ke kin bijire a gaban namijin da kike ikirarin gashi shi kike so ki aura? Uhum Basarwa ya yi yana kallon gefe a lokacin da ta taso tana fadin" Bara na zuba maka jus din plz, ko shine ka dan sha mana?" Jus din ya dan kalla a lokacin da ta zuba harda su rage tsayi tana sakin murmushi hakoran makarta a waje abinta Hannunsa ya saka ya amsa ya gyara zamansa kadan ya dan surba sannan ya ajiye ya sake dubanta a lokacin da take shirin zaunawa tana murmushin gannin ya sha ya ce" To babu tauye haki? Idanfa tana son wannin itama kuma aka yi mata dole?" Yanzu kam ido ta zuba masa tana son karantar asalin menene damuwarsa da maganar nan ne Fisabililahi? Yaya zai zo bayan ta yi doguwar tsumayin ganninsa bayan lokaci mai tsayin nan har ta cire rai ya zo ya ringa fitinar tumaninta da zancen wace bata da wani daraja? Menene a cikima dan an mata auren dole? Da ya san abinda zata aikatama da ya yi mata wa'azin hakan ga dukkan alamu Girairakinsa ya dage yana dan kausasa kallonsa kadan a kanta, hakan ya bata damar jan numfashi tana sauke nata duban domin wani irin