Sashe 16
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mana asiri mu yi kwana biyun nan lafiya mu gama lafiya ba tare da ta zane min ke ta sakamu kuka ba kin ji? Kina gani kamar haushinmu take ji din nan?" Itama kasa kasa ta ce" Innata me zai hanna mu kaura gidan amaryar mu yi bikin a cen har a gama? Na tabata hararan da take na sarkar kafana ne da kuma kitson da aka yarfa min, Innata ban san me yasa Innar birni ke haka ba" Kasa kasa ta amsata da fadin" Wuce mu zauna mu nutsu mu gama lafiya , abinda safiya na yi take zuwa bangaren wancen tabi tabin ta sarki sai kuma wani daren, ke dai kafin nan zuwa safiyar ne zamu kama kanmu" Saman tabarmar suka karasa ita kuwa ta gama damawa sannan ta kalli NADIRAH ta ce" Tashi ki shiga ciki kusan gado ki dauko min mazubi, harda na babanki ki wanke su a cen ki bani" Tashi ta yi, sai kuma innarta ta tashi zata bi bayanta Kallonta Fadime ta yi ta ce" Ina zaki je?" HINDU ta ce" Tayata zan yi , na ji aikin da kamar yawa" Da takaici Fadime ta ce" Zauna malama" Hindu ta kalleta da irin kallon nan na ban fahimta ba Fadime ta sake dagowa ta ce" Ki zauna na ce ko Hindu?, Ke kam Allah ya shirya ki, meye na yawa a wanke yan kwarayan da basu wuce hudu ba? Ki dai ringa tunawa yar taki daki zaki mikata , idan ta je tana aikata wani mugun aikin na kazanta ko lalaci babu abinda zai hanna a zage ku, duba ki ga wani shiga a jikinku daga ke har ita, na rasa me Habu yake yana kallonku kunna tsiyar nan, zauna min!" Hindu ta gyada kai ta je ta zauna tana kallon yayarta Kasa kasa ta ce" Aunty, nawama take yar? Ashirin ne fa zata cika, Allah na tuba dama ai da ni zaki mikamu na ringa mata yan share sharen da dan wanke wanken da dan girkin har ta gane , kuma in sha Allahu in bata gane bama sai na ringa safiya ina yi ina dawowa, Allah na tuba abinda da kokarinta, a wuni fa sai ta je rafi sau biyu kuma ta je dandali rai abinta, dama ita bata cika son wahalar sosai ba, to ganu aikin me nake yi?" "Muhammadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam, ke Hindu ki san annabi ya faku ki gyara halinki, yau ina anfanin mace ba shara, ba guga, ba wanke wanke, bale girki? Ai walahi ba kyau ba ko yar uban wanene sai ta wahala, kika san gidan wa zata je? A cen din zata samu sasauci ko wahala? Ke wani namijin kin san ya fi kishiya masifa, daga ke sai shi a gidan zai zamar maki balaki, bale idan da dangin miji masu jira a yi ? Kunna nan ku a tunaninku kyan da iya shegantakar kadai ke ja ko, kar ki manta talaka kike, yarki talaka take, idan kuka daukarwa kanku wannan hali yaushe garinku zai waye? Kanwata ki ringa tsawatawa Indi, ki ringa nuna mata an ki, ba komai ake nema a samu na, ba kulun take tare da ke ba kin ji?" "Aunty yi kasa kasa kar ta ji ki mana, aunty tsaya ki ji, bari ki ji labari, kun ga yar cen ko? Ni ina ji a jikina in sha Allah sai mun yi alfahari da ita, kuma auntu da kike fadin mu talakawa ne sai me kennan? Mu talakawa ne ama kuma masu rufin asiri a cikin talakawan ma, talaucinmu bai hannamu fara'a ba, bai hannanu bautawa Allah ba, bai hannamu farin ciki ba, bai hannamu hulda da jama'a ba, aunty shegantakar nan kuwa da kike ganni maza da yawa na dauko ta biyu ko ta uku fan ta farkon bata iya shegantaka ba sam...... Allah ma kuwa, ki dai dan bari kawai ki karra Adu'a, ama ko Aminu ne ko? Ni walahi dai dai ya san yadda zai yi da mu duka domin ba zan bari a wulakanta min ya ba!" Ta karashe harda dan buga cinyarta tana kara alamu irin na iya gaskiyarta take fada kennan Salamar Aban NADIRAH ya sakata sake dagowa tana murmushi daga wanke wanken ta ce" Abana ka dawo, dan rike min daya mu kaima inna ta zuba furar nan mu rangada" Yana murmushi harda yi mata sannu ya amshi biyu ya nufo innarta, wace ta saki baki da hanci tana kallonsu Nadirah na bashi labari ya fara kyakyata daria y ajiye kwarayen ya kuma amshi sauran ya ajiye ya juyo ya ce" Shi Aminun?" Nadirah zata yi magana Innarta ta fashe da kuka tana ture furar dake gabanta tana kallonsu gaba dayansu da suka rikice sunna tambayar ba'asin kukan nata Da yatsarta take nuna su ta ce" Yanzu, tsakani da Allah idan muka mace gaba dayanmu fa?, Ko idan wata kadara na tare da ita fa? , Jama'a bakwa gannin sangartar ta yi yawa? Ke Indi dan ubanki je kwaso kayana da na abanki kaf ki wanke su yanzu yanzu ba sai gobe ba, kuma Innarta walahi sai dai ki kauro nan mu zauna tare ama yar cen ko? Yar cen? Sai na bata kyakyawan horon da ba zaki ganeta ba, ! Balen abin nan na kafarki kar na tashi na karya ki, kin shigo birni wata fasara za'a maki dalilinsa?, Abanta abanta yanzu ka riko mata mazubin nan da kanka? Ka riko mata??????" Tap wollah yau gaba daya in fada maku rubutun ya ringa min gwalo dan kar na barku shiru ne na samo wannan *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 1 Sorry ba edditing Gaba dayansu rasa ina zasu sakka kansu suka yi, ya zamto sai neman gwaruwa suke ciki harda NADIRAH A rikice NADIRAH ta yi ciki ta haska fitilar Abanta ta shiga ciro kayan , duda a hade suke a kule sai da ta fitar da su kaf ta kawo ta ajiye ta je wajen manyan robobin wankin ta dauko ta ajiyesu sannan ta shiga hada ruwan wankin Innarta idannuwanta ne suka cika da kwallah, a hankali ta muke ta shigewarta ciki dan ta dan yau mijin yayar tata ba zai kwana a nan ba, dama idan sun zo yakan yi tafiyarsa wajen mazan gidan ya yi kwonciyarsa, Da ido FADIME ta rakata sannan ta sake maido dubbanta wajen mijinta tana jan hanci ta ce" Yanzu haka kuka zata shiga ta yi dan an saka Yarta wanki ko?" Murmushi ya yi yana sake gyara zamansa yana kallonta ya ce" Wai menene?, Na tabata kukan nan ba haka kawai zaki kwashe shi ba, meye aka maki yau? Me yake damunki?, Duba ki gani yarinyarki ta tsorata ji yadda take wankin jikinta na rawa?, Kin sani sarai wa kuka haifa Dimana, kuma kin san wankin dare ba kyau, me zai hanna ki mata uzuri ta kule kayan cen ta kwonta kusa da mamanta da sasafe in sha Allah ta tashi ta yi wankin?, Kin ji Fadimana?" Ajiyar zuciya ta sauke, domin kukan da ta yi sai ta ji sanyi sanyi a ranta, a hankali ta saci kallon y'ar tata, sai kuma ta dauke kanta kasa kasa ta ce" To ka ce mata ta bari, ni dai ba zan mata magana ba , dan kar ta raina ni" Sai da ya sauke ajiyar zuciya, domin a gaskiya da bata yarda ba bai san ba ko zia iya hakura NADIRAH ta yi wankin nan da daren nan, basuda wuta a bangaren nasu da sai ta yi idan da hasken fitila, kuma fa rikicin Fadime ne, ya tabata akoy abinda ya daga mata hankali , domin har ga Allah yarinyar fa ba laifi tana da kokarin aiki walahi, A sanyaye ya umarci NADIRAH kan ta ajiye ta je wajen mamanta ta kwonta dare ya yi Kai ta gyada ta daure kayan ta ajiye su da ci masu alwashin sai dai a tashi a ga ta gamasu, ita abinma ya rikitata me ya saka mamanta kuka? Sumui sumui ta zo wucewa Innarta ta saka ta dauki furarsu ta kaima innarta su sha Dauka ta yi harda su godiya ta shige ciki Mahaifinta ya yi murmushi ya dake kallon iyalinsa Kamar yadda ya kware wajen yi mata nasiha ya ce" Me yake damunki?" Ido ta zuba masa na dan kankannin lokaci, sai kuma ta girgiza kanta a hankali tana jinginar fa bayanta a jikin garu a sanyaye ta ce" Ba komai Abanta" Sake kafeta ya yi da ido, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Kin san ta yiwu gobe ace da ke za'a je baban birni ko?" Kai ta gyada a hankali tana kallonsa Ya ce" Kina son zuwa ne?" Kallonsa ta yi da yannayi irin na son gane da gadke yake da tambayar nan?, Sai kuma ta yi murmushi a hankali ta ce" Inada zabi ne Abanta?" Kai ya sada yana dan murza yan yatsunsa, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce " Ina iya samun hanyar da zan hanna a je da ke" Murmushi ta yi ta girgiza kai, a sanyaye ta ce" Zan iya, idan har hakan ya tabbata in sha Allah" Idannuwansa ya lumshe sosai yana jin abu mai girma a ransa a kan iyalinsa, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya dauki kasonsa na furar yan murmushi ya ce" Ko dan rakiya ba za'a yi min ba Madame?" Itama murmushin ta yi ta mike ta dauki hijabinta ta ce" Mu je na taka maka mijin Fadime........" Raka shi ta yi sosai sunna hira sannan ya tsaya yana hangenta har ta shige bangarensu kafin ya ja ya rufe masu ya tafi Tana dawowa ta tarar da HINDU zaune saman tabarmar kabar kanta ko dan kwali babu ta nade kafafuwanta tana kallon waje daya Dan murmushi ta yi ta karaso ta zauna a daf da ita tana fadin" Kamar wace kika kulaceni daga fadin gaskiya?" HINDU ta dawo da dubanta kan yayarta, kallonta take yi har sai da ta mata alamu na kallon fa? Sannan ta girgiza kanta tana dankwashi a kanta ya bata kas kas kas ta ce" Gaba daya