← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 87

Sashe 23

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yana jira" Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye ya amsata, yana kallo har suka tafi sannan ya koma yana kallon Fadime dake tsaye ta rungume hannayenta a gaban kirjinta A sanyaye ta ce" Ana nufin, a tafi da ita bangarensa ya ganta?" Kai ya gyada ya zauna a nan yana kallonta Murmushi ya yi ya girgiza kansa ya ce" Anya na yi maku adalci kuwa? Anya ni din uba ne na gari kuwa?, Anya da na zauna a nan ina aikin nan na maku adalci kuwa? Sai nake jin dama dako na je na yi na ciyar da ku, sai nake jin dama buka na samu ko a ina ne na saka ku, na kasance tare da ku, anya ni din nan uba na gari ne kuwa?" A hankali Fadime ta karaso ta tsuguna tana kallonsa, ta ce" Kai uba na gari ne Abanta, kuma kai miji na gari ne....., Ai inaga da saukima, ko menene inaga an dan rangwonta mana fa, domin da wani karnin ne mu din za'a fara batarwa, kashewa ko badawa a duniyar mahaukata, sannan a dauki y'ar a sakata a mugun aikin!, Abanta ina cike da tsoro, ni bana tsoron sanar mata domin ni nan zan sanar mata, abinda nake tsoro shine kar su rinjayeta, yarinya ce!, Ama in sha Allah, Allah zai kama mana, ni na yi imanin adu'armu ba zata taba faduwa kasa ba, in sha Allah zamu yi ta rakata da Adu'a, ko menene zai zo da sauki, bi'izinillah ba zata aikata abinda suke so ba, .....ka kwontar da hankalinka, a yanzu ka samu ka je da itan, idan kun dawo zan fita da ita, domin bana son abinda zai janyo mana saka ido, zan fuskanceta na fada mata gaskiya, mu da muka rike Allah? In sha Allah shi zai kama mana, shi zai daidaita mana, shi zai kare mana yarmu, kar ka sake sage min gwuiwa bayan na dangana Abanta" Ajiyar zuciya ya sauke ya gyada kansa ya ce" A saka mata hijabi da nikaf mu tafi" Ciki Innar birni ta koma ta zakulo lafcecen hijab dinta da nikaf dinta ta ba Nadirah fuska a hafe ta ce" Ke saka maza ki tarda babanki ku je nan ku dawo" Sakawar ta yi ta fice suka tafi Sunna tafia innar birni ta zauna ta fuskanci Hindu, a ttausashe ta ce" HINDU, ina so mu yi magana dan Allah, ta fahimta, ina so ki bani duka kaf hankalinki kin ji?" HINDU ta zauna daga ninke kayan da auntyn tata ta barbazo tana kallonta Fadime ta ce" HINDU, ina so ne ki fuskanci abin nan da fuskar da ya dace, ina so ki gane cewa a tafiyar nan rikicinta ya fi jin dadinta yawa, kuma ki sani ba za'a taba yinta da ke ba domin uwa ce ke, jinnina ce ke, Gimbiya ba zata taba yarda ki je ba, dan tana iya gannin zaki hannata aiwatar da abinda suka yi niya ne" HINDU ta kalleta , alamu na hankalinta ya fara tashi da maganar karara ya bayana a tatare da ita Muryarta a sanyaye ta ce" Ita daya? Ita daya za'a kai babar masarautar da sha yanzu biya yanzu idan aka kamaka da wani laifin? Ita kadai za'a mika wajen da take da kishiya? Yayya kishiyar take? Ita kadai za'a kai wajen da wasu zasunna zuwa sunna azalzalata aikata sabo? Idan fa suka cin mata?, Yaya zamu yi?" Fadime ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Shi ya da da farko na so mu gudu, ama abinda kika fada din nan ki sani ya yi tasiri a zuciyata, na tabata dalilin wannan har makotanki sai sun shiga uku ba ke ladai ba, da a yi wannan gwara mu zuba ido mu rungumi Adu'a mu barawa Allah zabi,Hindu tabas abin nan ko uwar mata sai wace ta ginnu a kan kafafuwanta zata iya, sai dai kuma yarinyarki tanada adu'o'in neman kariya daga dukkan fitina, haka kuma tarbiyara da muka bbata ba ta kwadayi ko ta alfahari bace, sai mu dangana mu sake dukufa mu ringa fadawa Allah, na tabata wata rana idan da rai zata yi nasara, idan kuwa kadarar NADIRAH ce haka ina fatan kafin su cin mata ta yi kisa ita nata ran ya bar gangar jikinta........." Fadime ta karashe tana lumshe idannuwanta hawaye naa digowa daga ramin idannuwan nata Itama HINDU, a hankali kuka ya zo mata, kuka mai rauni, mai matukar zafi, domin a da kwata kwata bata hango lamarin nan a haka ba, a yanzu da akai mata irin wannan karatun sai ta ji hankalinta gaba daya ya tashi tana neman ficewa daga hayacinta, tabas ba zasu taba yarda ta bi y'arta ba, a yanzun sai take ji dama basu zo birni ba, da zuwa ta yi ta ba innar Aminu hakuri aka yi auren nan, innalilahi wa inna ilaihi rajune, tabas abin na nemen rikitata, sai dai yayarta ta yi ta tausarta da nuna mata cewa basu da makamin da ya zarce Adu'a, ana karni na yanci kai ne, ama kuma karni na mai kudi shine sarki, bale sarkin da kansa a kan bafadensa? An yi wanda ya fi wannan zafima. An dauki kusan awa daya da tafiyarsu sai gasu sun dawo, dawowar da suka yi a cikin mota mai sirri, watau mai bakin gilashi, da direba daya kwal su biyu a baya Bai masu dogon bayani ba, ya taya su kwasar dukkan abinda yake na anfanin gagawa a garesu sannan suka bi shi bisa umarninsa suka shiga motar nan direba ya ja su, Tafia ta dan lokaci kankanin da bai fi minti talatin ba suka karaso wani gida mai babar kofa da tsari irin na masu hannu da shuni , suka shige bayan ya sauka ya bude masu sannan suka yadda zango a sabon gidan babu mai yiwa dan uwansa magana sunna jiran abinda zai biyo baya, domin ko NADIRAH da ta tambayi innarta cewa nan kuma ina ne? Yaushe zasu tafi wajen bikin? Amsar da ta bata shine ta yi shiru bata son hayaniya yau, hakan ya bata mamaki ya kuma daure mata kai, innarta bata son hayaniya? Lalle akoy abinda yake faruwa, sai dai zata zuba masu ido ta ga koma menene A gidan sarki kuwa da gadara ya yi kiran Gimbiya, a lokacin matarsa amarya ce ke tare da shi tana zuba masa abinci, a dole ta fita dan zai yi sirri da Gimbiya, zuciyarta cike da daci Gimbiya na zuwa ta zauna saman kujera fuskarta a cinkushe, yau tunda safen nan da ta dauki mari take bangarenta kamar zata kone dan bacin rai, Dolema ta rikita rayuwar FADIME, ta tabata ta amshi mari daga mijinta ne dan ta mari FADIME ba dan wani laifin daban ba, mari a matsayinta? A gaban bafadensa?, Lalle lalle idan komai ya lafa sai ta yi dalilin da Fadime ta dawo yi mata bauta dan ta wanka mata ninkin ba ninkin din marin da mijinta ya yi mata! Jus din da ya kai bakinsa ya ajiye bayan ya shanye ya gyara zamansa yana fuskantarta ya ce" Elle est tres belle, mais sauvage, l'a tu remarqu ?" ( Tanada mugun kyau, sai dai batada wayewa, kin kula da haka?) "Wayewa, abu ne mai saukin koyo, duda jahila ce zai dan bada wahala sosai gashi waje a kure, rayuwar sarauta ce mai wahalar dauka Aban Bahija!" Gimbiya ta fada a tausashe tana sako sunnan Bahija dan ta ga reaction dinsa, domin rabonta da ta sako magana irin haka an jima Juyowa ya yi daga kunna TVn da ya yi ya dubeta ya ce " Ba jahila bace, saukarta biyu in ji ita" Baki ta tabe tana dubansa ta ce" Islamiyar kadai ta je, bata da boko" Kafadunsa ya dage ya ce" Sai a gargadeta da budar baki da yin magana ko a gabansa ne, dan kar hakan ya haifar da matsala, an kai su gidan BAHIJA na yi magana da Lauyana cewa ya mayar sunnan mahaifiyarta a saman takardar" Da mamaki ta zuba masa ido, a hankali ta ce" Gidan BAHIJA?" Kallonta ya yi a kausashe ya cire idannuwansa da kansa ya mata alamun kwarai haka yake nufi Zuciyarta sai da ta yi wani irin tsale ta daki kirjinta dan buguwa da faduwar gaba, sai dia bata yi magana da karfi ba dan ta kula ya fita hawa sama yanzu A tausashenta ta ce" Ama gidan Bahija fa ka ce Aban Bahija?, Gidan da ka kashe makudan kudi million na gugar million la ginna shi?, Gidan da ka yi masa hawa hawa hawa ka zuba gazon ka yi masa ginnin a zo a gani kace na Bahija ne saboda ita daya ce mace cikin yayanka itace abin tausayi, sauran su nemi nasu maza suke shine zaka saka sunnan wata a sama?" A kausashe ya ce" A da ba, a da da nake tunanin na isa da ita, a yanzu gaskiya kowa ya yi ta kansa kawai tunda har ni zata duba ta yiwa rashin kunya!" "Aban Bahija, ka kiyaye, kar son zuciyarka ya fi karfinka wannan karron, domin ka san abu ne da ba zai taba yiwuwa ba, kar girma ya fadi a kan abinda bai kai darajar haka ba!" Ta fad a dan kausashen itama, domin abin ya fara bata tsoro, gidan Bahijarta? Gidan da take takama da shi a cikin kishiyoyi? Bama a lokacin da ake kan ginninsa basu isa su hadu da ko daya ba sai ta yankawa mutun magana, bale a yanzu da aka gama? Da gadara gadara take dauko maganar gidajen sarki tace kaf ciki gida uku ne ya fi na Bahijarta? Lalle akoy tashin duniya a garin nan! Zamansa ya gyara da shauki irin na yan duniya ya ce" Kina tunanin da abinda kike tunani ne gidan nan zan malaka mata?" Kai ta juyar ta sake kallonsa ta ce" To nima shi na gani, me zai hanna ka saka sunnan Uban yarinyar idan ya so idan aka daura aka tafi da yarinyar sai ka maido sunnan Bahija a sama?" Habarsa ya kama da mamaki ya ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 1 Jinjina da ban girma zuwa a gareku masoya, Allah ya
Chapter 23 · 0% Book details