← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 87

Sashe 38

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

saka shi zumudin karbarta a yau" Tana gama fadi ta fice da sauri itama tana fatan Allah ya sa kar ta biyota Umma kuwa kwarai ta shaka , hakan ya sakata yin kasakai da mamaki, Kai ta gyada tana cije lebe a ranta ta ayana' *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 2 A ranta ta ayana' Yaro man kaza, lalle ina sake da lamarinki, ama ke na zan tabaki da kaina ba, radadin kishi da abinfa zai samu Mijinki zai saka ki dabawa kanki wula da kanki ki kashe kanki, domin kima na san kina masa so irin mai tsananin nan, wannan kam ba algus a ciki, hakan zai kaiki ga halaka wawuya!' Ficewa ta yi ta nufi Bangaren NADIRAH Tana shiha wani kanshin turaren ne ya sake dakar mata hanci, Ita fa mamaki take yi na NADIRAH da innarta, irin yadda suke ba tsafta da kanshi mahinmanci sai ido ya gani, Da safe da ta shigo da sasafe Nadirar ta tardo yana guga, sai da ta tsorata walahi, domin a lokacin kowa na iya shigowa, idan aka tardota tana guga me kennan?, Da kyar ta iya hannata, haka dazu da za'ai mata kwaliyar tarbansa da kyar ta amince domin cewa ta yi bata son hoda da da shafe shafen nan na fusla, a bar mata fuskarta naturel, sai da suka yi mata a taro a taro sannan ta amince, an dauki lokaci ana kwaliyar, hala suturar da aka ciro mata abin sai wanda ya gani, du a burin Umma ta jefi tsuntsu biyu da jifa daya ne, watau ta sakawa ASADEEK yarinyar a rai farat daya, sannan ta kayar da gaban HUZNAH, bayan ta yiwa NADIRAH hudubar du jaraba kar ta yarda ta kwana a bangarensa, bata san tana fada NADIRAH na ayanna nata abubuwa a zuciyarta bane , kala daban daban wa'inda da kunnuwanta zasu jiyo mata da tana iya summa dan firgita da tsorata Karasowa ta yi falon tana yiwa bayin dake zaune a dan takure alamun su tafi, Da sauri suka karra dukawa suka yiwa NADIRAH da inna salama suka tafi zulatansu cike da mamakin hira fa Take yi masu su bayi? Zaunawa Umma ta yi tana karra cika fuska rai a bace ta ce" Ba zai samu ganninki yau ba, yana tare da gajiya ne sai ya huta wai" Wata irin boyayiyar ajiyar zuciya ta farin ciki NADIRAH ta sauke A bayane kuwa ta talwakwabe fuska ta irin mugun hade fuskar nan bata ce komai ba Umma ta sake yatsina fuska ta ce" Ama ya yiwa kansa asara, na tabata da ya yi arba da ke a yau da sai ya mance wanene shi, du takamarsa da mulki da kyau kuwa" Da mamaki HINDU ta kalleta, sai dai bata ce komai ba ta cira kanta a ranta tana ayana' Toh Fah' A fili kuwa ta ce" Ai ba zamu gajiya ba in sha Allah, mu da muke so? Dole mu jure har mu kai ga ci" Ua ta yi murmushi ta kalli HINDU, a ranta ta ayana' shi yasa nake jin ba zan bari ki tafi ba, dan na kula kece ky din bude kwakwaluwar yarinyar nan, dan alamunta tanada ra'ayinta, ama kamar kin isa da ita' A fili kuwa ta mike tana sake sakarwa da NADIRAH murmushi ta ce" Ki huta lafiya, da safe in sh Allah za'a kuma zo a shirya ki, dan kin san kishiyarki na kusa, ko dan ta saka maki ido tana iya shigowa, duda ke ya dace ki fara zuwa ki gaisheta ama ba zaki je ba, kwa hade a cen fadar uban gidanku ku goga, kin fi karfinta walahi, sai da safe idan na samu damar kaiki zan zo ko na turo yam mata" HINDU ce kawai ta iya amsawa, NADIRAH ta cika, iya cika, a zuciyarta kuwa fadi take yi' Aikin banza, idam an samu damar a kaini?, Hehehe an fada masa cewa na yi ina son zuwa na gaishe shi ne? Wai takamarsa kyau, wani kyan mutumen da ya haifi su Innar birni da innata? Sunna ce masa Baba?, Ai sai fatiha kawai koda an yi kyan a da, a yanzu an tsufa kuma sai hakuri, oh ta yiwu matarsa fa kishinshi take yi, itama ko yarinyar ce ko tsohuwa ce? Allah dai ya tsareni da cusa kai ki ta Aminu!' Tana Fita Hindu ta rafka tagumi, sai kuma ta saki hannunta ta ce" Allah, Allah mun tuba Allah, kana zamanka sai shedan ya ringa sako maka tunani kala kala, kim ga kawai sai ta ringa min ka.da kwartaye matar nan" NADIRAH ta kalleta a zabure tana rufe baki ta ce " Astagfrulah Inna mamansa ce fa aka ce, ni mamakin da nake mamansa wace ta haife shi ko kanwar mamansa?" "Ke hadimarsa ce, ni da Sarki ya samo min labari sala sala, baki ga jiya har dare muka raba muna tataunawa ba? Kina ji ita wannan a da baiwa ce, irin bauta ta da suka yi wace ba'a biyansuma, kuma da kika ganta a nan kina ji irin aminiyar nan ta kuryar daka mahaifiyarsa ce, domin baiwa ce da ta zama kamar yar uwa, ita ta raine shi, da kanwarsa shi yasa suke ce mata Umma, ba wata mahaifiyarsa, ke yanzu mahaifiyarsa zata neme shi da mugun nufi? Ki duba fa kalamanta, ni abinda nake son ganewa daya me tak da matar nan, shin asiri akai mata ko nuna mata aka yi idan bata yi ba za'a kasheta ko wani nata sosai? In ba wannan ba gaba daya matar nan gaskiya ko shedan dan makarantarta ne, Indi wai bata maki kama da lwartaye?" HINDU ta karashe tana karta kama haba da zarro ido Da sauri Indi ta mike tana cire alkyabar nan ta kuma warware gashinta ta cuje dan kwalin ta ce" Wa bilahilazi ki yi bakinki ya fita innata a kashe mu kafin mu yi ceton bale na komawa Aminun, Astagfrulahi ina ita ina kwartanci jama'a tsofai tsofai da ita, Umansu ce fa, ai ba zata fara ba Innata, bara na wanke abin nan kaikayi yake min a fuska bama na gani da kyau na zo mu yi carafken nan, jiya a tara na fadi ba manta ba" Da ido innarta ta rakata, sai kuma ta sauko kasa tana cire daurin da aka kafa mata itama ta rafka tagumi a bayane ta ce" Oh ni ta Habu na shiga uku yar nan tana tune da shegen nan wuya uwa marikin lema?, In sha Allahu Indi ba ke ba Aminu, yau dai da gani ga UMUGHLUK ITIBEL?, Kai jama'a da babu abinda zai hannani fashewa da kuka, yo ni ai Adu'a nake yi kar na fada masa su waye mu mu shiga uku, Je ki dawo mu yi carafken ko na manta wannan tunani na matar nan kamar kwartuwa, dan nima ji nake yi kamar na yi sabo walahi, mace baba haka ina ita ina irin aikin nan?, Kawai itama tana magana ne tana lumshe lumshe ga wasu idannuwa kamar maya sai ta kureka da kallo, in ba wannan ba ai.na za'a yi mata wannan tunani ba sam, sai kuma wasu magangannu dai irin na yan iska, ama in sha Allahu inaga ba zata kasance kwartuwa ba sam, ai ko dan gudun kar danta ya karta zata kiyaye ai ba kyau kwartanci ".............( Allah dai ya taro ki Hindu madam) __________________________________ Washe gari haka aka tashi da baki, kamar koda yaushe, sai dai na yau manya manyan baki ne dan yi masa barka da sabon aurensa, Haka ya wuni amsar bakin har yama ta yi ya kowa ciki dan samun dan hutu kafin lokacin sallar magariba ta yi A irin lokacin ne kuma ya sake samun wani lamarin na matan uku dake rayuwarsa, wani zaman, da wani shirin daban, domin da gaske Umma ta dage sai matar da aka daura masa ta zo ta gaishe shi, hakan ya sa ta ki zuwa kawota danma kar su dawo su tardo ya shige barci, sai kawai ta tura Baiwa cewar maza a rakota , idan ta fito jakadiya ta yi jagora a rakota Sosai HUZNAH ta karra kimtsa zamanta, Auta kuwa ta bude litafinta tana nuna masa cewa zata bashi hardar wata Adu'a da ya koya mata a kauye Baiwar ta samu shiga falon domin sakon UMUGHLUK ITIBEL ne Tana shiga NADIRAH ta fito daga kicin, hannayenta sanye da safar hannu, kugunta daure da abin girki, girki suke yi ita da innarta, fuskarta da kwaliyar da akai mata, ama ta cire tufafin ta mayar ta ninke , gashinta a baje yake a bayanta, girki suke gwadawa ire iren WA'INDA masu gyaran nan suka koya mata Har kasa Baiwar ta duka, kanta a kasa, domun ta tabata matar nan ko wacece ta jikin sarauniyarsu ce Kanta a kasa ta gaisheta NADIRAH ta amsa tana sake gyara daurin abin girkinta a kugunta Baiwar ta sake sada kanta ta ce" Allah ya taimakeki, sako ne wajen sarauniyarmu, daga Umma uwar bayi, aka ce ta fito mu mata jagora baban Falo, a irin wannan lokacin UMUGHLUK ITIBEL na nan zai amshi gaisuwarta" NADIRAH ta yi tsai tana ta kallonta, a hankali ta fahimci me sakon yake nufi, watau ana nufin ta je ta gaishe da shi babansun? Baki ta yatsine tana dan waigawa dan bata so Innarta ta ji, domin a wannan lokacin da take jin zumudin su fitar da gashin cen ta dangwali romonsa ta zira a bakinta babu abinda zai sakata wanka ko cenza kaya da zuwa shirmen gaisuwa, wai inama ruwansu da sai ta gaishe shi ne? Su shafa mata lafiya, ko haka ake yiwa matan safakan ne? Dole sai an san ka je wajen miji? Shi yasa a sarauta bata ga komai ba sai tsabar wauta da rashin sakewa Hankali kwonce NADIRAH ta ce" Idan kin je ki ce, na ce yanzu ina kicin, sai dai wani jikon" A zabure baiwar ta dago, ba da gangan ba ta yiwa Nadirah kallon tsaf, a rashin gane me NADIRAH ke nufi ta ce" Sakon na sarauniyarmu ne ranki ya dade, sannan sakon daga UMUGHLUK ITIBEL ya fito, domin idan UMMA tace, shi yace" NADIRAH ta saki
Chapter 38 · 0% Book details