Sashe 35
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
hanya" Tana fita ta daga wayar wa'inda ke tsare da hanyar saboda REBEL ( watau yan fashi da makami) ta tabatar an watsa mutane ta ko'ina da bindigogi dauke da alburusai, domin gari ya dauka ya yi aure, idan akoy masoyansa a daji, akoy makiyansa masu farautar rayuwarsa a bayane! Ke kuma aboue ko? *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 2 Tana tafia NADIRAH ta dago, muryarta a cen ciki ta ce" Innata, idan kika bi ni Aban kauye fa?" HINDU ta lumsje idannuwanta sannan ta yi murmushi, a sanyaye ta ce" Ba zasu kwace mana komai ba Indina, zan raka ki har dakinki sannan na dawo in sha Allah, ki min alfarma ki kwontar da hankalinki kin ji?" Kai ta gyada tana jin sanyi sanyi a ranta, sannan ta karra jimke yar karamar wayar da Abanta ya bata cewar akoy layinsu a ciki, yanzu haka Innarta ta daukota daga ma'adanarta ne dan su yi magana da iyayen nata, sun gama maganarma ama ta kasa mayarwa, da kyar ta ba Innarta ta mayar ta boye sannan suka mike dan gabatar da sallah Bayan an gama sallar azahar aka shiga fitar da kayan da aka ce nata nw, kayan da su ba'ama nuna masu ba Lalle an fitar da kaya masu yawan gaske sannan aka fitar da ita Gimbiya ke rike da ita, irin rikon nan na tana jikinta sosai sannan tana ta shafa kanta tana afkin nuni da rarashi take yi har suka karaso gaban wuleliyar motar da za'a sakata suka shigar da ita sannan suka yi salama aka dauki hanya, domin tafia ce zasu yi a hankali wace zasu dauki lokaci koda sun shiga garin da wuri ba zasu isa gidan da wuri ba sai sawaye sun dauke, dan ba'a zuwa da matar sarki ido na gani A hankali suke tafe, cikin motocinsu, motocin sojawa sun zagaye su, tafiya wace idan sun doso ake dakatar da masu zuwa sai sun wuce har suka dauki babar hanyar da zata kai su AGADAZ A hankali Umma ta dan karkata kusa da kunnen NADIRAH ta ce" Kuka kike yi?" NADIRAH ta dan yi tsam, kafin ta girgiza kanta a hankali" UMMA ta yi murmushi ta ce" Kina iya kwontawa a cinyana, ko a kafada ki huta kafin mu isa BABAN birni, domin zan so ki bude ido ki ga Baban birni, ko kin taba shigowa?" NADIRAH ta sake girgiza kanta tana dan gyara zamanta Umma ta sake yin murmushi ta ce" Garin Agadaz, gari ne dake dauke da al'adu, da kuma yannayin ginni irin na kasa, Mazan garin sunna da kudi , boyayun kudi, mahaukatan kudi, domin wasunsu manya ne na kasa, wasu kuma manyan da suka aikata fashi da makami a da ne, wasun ma'aikatan gwamnati ne, wasu masu cin gashin kansu ne, muna cakule da larabawa, da kuma wasu daidaikun yaren........, Gari ne mai daraja, mai girma, mai dauke da mata buzaye da larabawa masu ji da kansu harma da daidaikun wasu yaren, a Agadaz muna girmama Uban kowa, Shi UMUGHLUK ITIBEL yana zuciyoyin samari da yan mata, datawa da tsofafi.............., Zan iya ce maki kin yi dace kin kuma taka sa'ar da duban yan mata ke hari....kin kafa tarihi koda a yanzu kika mutu" NADIRAH ta dan dago da idannuwanta ta dan saci kallon Umma, still bata furta mata koda A ba Umma ta dora da fadin" Abinda ya sa ba'a cika gini irin na bulo da bulo ba sai gidan wa'inda suka gagara, saboda sahara, yankin kasa da kuma tsohon gurbi na Volcan, idan zaka dora ginnin da ba kasa ba ko zana, tabas sai ka girgiza da aljihunka, sai dai idan ka tara hakan ba wani matsala bane kuma sai ka zuba cefa ka zuba ginni, Mijinki ya yi ginnin da harta dakin shn shayinsa Bulo ne.............., Ya tara fa, ke kam kin yi dace" NADIRAH ta tabe bakinta a ranta tana ayanna' hakane' Umma ta ce" Zaki sha mamakin darajar da zaki samu, duda ba ainahin ke din bace, ama ke dinma kece, tun daga wajen gari matasa na cen da manyan motoci sun yi niya sai sun yi wasan dauko Amarya duda shi angon ba kece a gabansa ba, ya fita da mahaulaciyar kanwarsa da kuma matarsa shakatawa......, Wannanma ai kamar cin amana ne ko?" Wani murmushi ne ya kwacewa NADIRAH, a ranta ta ayana' An zo wajen, dama na fadawa Innata kina warin munafukai, da ace ita din ce ta yiwu hakan ya mata ciwo, sai dai kashhhhh ko a kwalar rigata' Umma ta karra rage muryarta ta ce" kin san manyan ginni na matan gidan hudu ne, daya matarsa na ciki, daya sai ya saka kanwarsa, kema a dayan kike na kusa da na kanwar tasa, na san dayan kuwa rushe shi zai yi dan da wahala wata macen ta shigo a matsayin matarsa ko?" Lalle A yau a yanzu NADIRAH sai ta rainawa matar nan wayo, kuma ta tabata wannan mata tana fama da jahilci mai tsananin gaske, wanda ba zai iya barinta tunanin fari ko baki ba, sai dai ta aikata abu kanta sake, tabas tana da ayar tambaya a kan matar nan, magangannunta sunna saba kamaninta, sai dai ba zata yi gagawa ba, dan bata san wacece ita a masarautar da wajen baban nasu ba sam, Sun ja tafiyar iya ja, har sai da duhun magariga ya fara shigowa sannan suka saki tafiyar suka yi mai sauri suka karasa ana gama sallah A hankali NADIRAH ta samu kanta da dan ba idannuwanta damar kallon hayaniyar da take ji A hankali ta fara kallon yadda innarta ke washe baki tana daga hannu Wani murmushi ne ya kwace mata dan tsakanin Innarta da Allah take daga hannayenta bibiyu tana gaishe da masu gaisheta Da sauri ta damu kanta da karra wara ido tana kallon tarin jere na motoci da dawakai majiya karfi, da manyan babura sun tsara abin gefe da gefe sunna gabatar da wasan a tsare Karra zubawa abin ido ta yi tana jin wani irin yamyamyam a jikinta, domin wasa ne na kwararun wa'inda suka iya sarafa mota, ko babur, uwa uba DAWAKAn da suka sha ado , ga wata mahaukaciyar busa da manyan makadan kwararu masu gadon abin a jinninsu sunna aiko da busa da kida irin na sarauta sunna karra rike gangar kamar zasu tada wajen Tabas abin ya kayatar da ita, a hankali kunnenta ya tsinkayo mata muryar Umma tna fadin" Murna suke yi, farin ciki suke yi, burinsu suke gannin har ya cika, Uban gidansu mai tausayin talakawa ya karra aure, ta yiwu a yanzu su samu magaji mai halin datako, sunna farin ciki ne dan burinsu a wayi gari matar UMUGHLUK ITIBEL ta dauki ciki, uwa uba ta haife masu , a yanzu kyauta zaki gabatar masu ta wani abun dake jikinki, ko menene, kina iya basu zoben nan, ba kudinsa zasu auna ba, darajarsa da ya fito daga wajenki zasu duba, idan mun karasa Fada an fito da ke zaki yi kyautar" Janye idannuwanta ta yi daga kanta, yanzuma bata ce mata komai ba, hakan ya sa Umma karra kallonta, ikon Allah take ta kallo, bata taba gannin yar bayi da saurin daukan abin sarauta a jinni ba irin na yarinyar nan! Get din gaba daya aka wangale motar dake dauke da ita kadai ta hau baban hanyar su kuwa du suka layu ana ta buda irin ta bugaje ana yi mata oyoyo Umma ta fara fitowa bayan ta sanar da Innar Kauye cewa ta dakata har a mikata dakinta sai ta shiga, idan ta shiga kar ta zauna a saman kujera ta zauna a kasa har a gama gaishe su a watse Ita dai NADIRAH tana zaune ta ji Umma ta kamota, a kasan zuciyarta ta rinha addu'ar da Innar birni ta koya mata cewa ta shiga da ita du inda za'a sakata A hankali ta dan dakata da Adu'ar ta zubawa hannunta dake cikin na umma ido sakamakon jin da ta yi tana dan murza mata hannu A hankali ta janye hannunta tana mayar da shi kirjinta sannan ta ringa bin sawun Ummar wace ke ta son karra lalubo hannunta A kofar tamfatsetsen falonta Aka ja aka tsaya da ita Da wata irin isa da kuma iy sarafa harshe Umma ke yi masu godiya, ta gabatar da NADIRAH a matsayin yar sarkin Tanut sannan mata a wajen Sarkinsu Sosai wajen ya karra daukan budar farin ciki A hankali ta juyo wajen NADIRAH kasa kasa ta ce" Ki kwatanta kyautarki wa jarumin matasan garin nan baki daya dan ya isar da sakon wa matasa" Dan tsai ts sake yi, a hankali ta sake yin yadda zata hangi taron mutanen nan, har jikinta wani irin rawa yake yi idan ta ga wai taronta ne, a gaskiya ta haka ta yarda ko yayane yanada masoya shi baban nasu, domin ba'a yiwa talaka dole, koda an sayi wasu a cikin talakawa wasu ba zasu sayu ba, wandinnan jama'ar kuwa da du fadin masarautar nan ta ki daukansu ta tabata sa kai ne, yan gani a kasheni ne a kan sarkinsu A hankali ta kai hannunta wuyanta ta bale tafkekiyar sarkar nan ta zinari, ta cire awarwarayen zinarin gaba daya tana murmushi ta fitar da farin hannunta wanda shi an ganshi sanadiyar hasken wajen na fitilu ta mikowa UMMA wace ta yi mutuwar tsaye ta kasa karba har sai da ta budi baki kasa kasa sosai ta ce" Kadan ne, Allah ya sa zasu ji dadin karamawata, na gode" Wani irkn abu ya sara a gefen kan UMMA, maganarta jakadiyar UMUGHLUK ITIBEL ta ji, nan take ta daga murya ta rangada buda tana sheda kalaman uwar gijiyarta, A dole Umma ta amshi sakon, tana ji tana gani ta mikawa Hakadiyar sarki sannan ta juya ta budewa NADIRAH kofa tana kallonta har ta gama murmushin tana jin kamar ta cire alkyabar nan ta kwaso shokiiii ta juyo ta shiga falon da take kyautata zaton na sarkin ne ko? Domin tana shiga ta tiles din dake malale ta fara tunanin nan din dakin mai gidan ne gaba daya Rufewar kofar da muryar Umma kamar cikin fada