Sashe 48
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fara hasala ta yi maganar Kafin HUZNAH ta sauke harufanta Umma ta dauki nata itama a dan hasale ta ce" A kan wani dalili zaki saka yarinya ta sha madara bayan tuwo nace ta ci ta sha maganinta ne?" Idannuwansa ya rintse, hayaniyar ta farra hawa kansa, jira yake ya ji ta yi magana a haukacen da ta saba, sai ya ji shiru Hakan ya saka shi dago dubansa ya shiga binsu da kallo su dukansu Su amsa suke jira daga gareta Ita kuma ta dauki madarar da aka mata magana a kanta dan bakin rashin ji ta kai baki ta lumshe ido tana shanye masa madararsa, madararsa fa, shi fa, shi ASADEEK jama'a Rasulullah (S.A.W) NADIRAH kuwa a ranta ayanawa take yi' ku bari na sha na dawo hayacina, sai mu baje idan hali ya kama, ai ba'a gwa da gwa da yinwa kawuna uwa dutsin jifan shedan!' Tashin hankali, ita bata san me ake nufi ba hala? Mun shigesu *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 3 Sai da ta gama shanye madarar nan, ta lumshe ido tana jin yadda take ratsa mata kirjinta, watau sanyi ne da ita madarar, tana matukar son madara mai sanyi ama innarta sai tace aa in dai zata sha ga mai dumi kawai ta sha Idannuwanta ta bude hankali kwonce ta sake mika hannu ta dauko dan tsinken sakace hakori kamar wace ta ci naman kazi ta dan bude bakinta kadan ta tsatsaka sai kuma ta yi wani tsut tsut da bakin nata sannan ta barshi a ciki tana dan wasa da shi a bakinta A wajen nan Auta ta fi kowa jin kamar zata kurma ihu, domin tun kallon na mutun biyu ne har ya dawo na mutun uku sunna kallonta, amsa suke jira ama NADIRAH ta gama ta yi shiru abinta da bakinta Umma, ji take yi, wani irin ashariya, irin na maguzawa, irin na mutanen kafurci na mata yawo a harshenta, so take ta yiwa yarinyar nan abinda bata taba tunanin ana iya yiwa mutun a duniya ba, sai dai wanzuwar UMUGHLUK a wajen ya sakata kasa barkata hakan Ajiyar zuciya NADIRAH ta sauke ta kalli HUZNAH dake kallonta ta daina cin komai Murmushi ta yi mata ta ce" Aunty, ba'a taba madararsa ne? Ko nice ban zama ta gida ba?"........... Sai kuma ta kalli Umma ta ce" Umma, magani ai idan an sha madarama ana iya sha ko? Bata ra'ayin cin tuwon idan aka takurata sai ta samu matsala ai inaga ko?" "Ba maganar kasancewarki yar gida ko yar wajen gida bane, babu mai taba madararsa, yaya zaki taba baki tambaya ba kanki tsaye"...... HUZNAH ta fada tana dake fuskantar Nadirah Ko ajiye maganar bata idasa ba Umma ta ce" Bama wannan ba, maganar cin abincin Auta, shanta, komai nata nice a gidan nan, babu macen da zata shigo ta shiga ciki domin nice mamanta, kin gane? Kuma rashin lafiyarta dole ta ringa cin abinci a kai a kai " HUZNAH ta sake cafewa, dan bata ga a kan me Umma zata hannata fadin nata damuwar itama ba, a birkice ta ce" Aa Umma, ai dolene nima na fada mata ta gane cewa madararsa, abu ne mai matukar mahinmancin da shi kadai ke shan abinsa, ko ke bakya tabawa, haka nima, ta zo ta dauka ba izini ba komai ta sha ta ba Auta?, Ai ba haka ake yi ba, ba wai maganar tana matarsa ko yar uwarsa bane, a gidana ta sameni dole zata bi takun tafiyata!" NADIRAH ta sake waro ido wata shegiyar dariya na tukota, a hankali ta kai hannunta wajen bakinta ta furta" Toh fah" domin abin ya bata mamaki ainun, bale da kamar hayaniya da yar cacar baki ke neman kaurewa a tsakaninsu, hakan ya sa da sauri auta ta shanye madararta tana sake kallonsu itama NADIRAH ta kalli wannan, ta kalli wannan mamakinta ya ki barinta, gaba daya sai ta samu kanta da raina masu ajawali walahi Kamar daga sama, muryarta a tausashe ba a kausashe ba ta ce" Ku dan dakata ku huta mana, abin nan dai tunda ba sabon Allah bane ya dace ku saurara hakanan gaskiya, na gama fadin amsar kawai a wuce wajen mana, karawama zan yi!" Sai da Umma ta ji zata kifu a sama, da karfi ta ce" Lah ha ila ha ilalahu......." Kara talabe haba ya yi a bayane, kasa kasa sosai ya tare da fadin" Muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wa salam" Umma ta nunata da yatsa ta ce" Babu abinda zaki karra a nan, yaushema kuka shigo da zaki nemi fin yan gida?, Dokata babu mai taka min domun ba zaki taba fina sonta ba, yarinyar dake fama da ciwon hauka ne zaki saka ta kwonta da dan ruwan madara a cikinta da magani?"......... Tunda ta furta kalmar nan, sai ASADEEK da HUZNAH suka zuba mata ido, kalmar haukan da ta ambata kai tsaye ba wani dan sakaya ya saka su zuba mata ido su biyun, Auta kuwa sai ta samu kanta da sada kai bata ce komai ba NADIRAH ta zuba mata ido itama, kallon da take yi mata ya dan ankarar da ita cewa a yau ta so barin bacin ranta fitowa, uwa uba itace har da yin hayaniya a saman kansa bayan basa yi masa haka, hasalima abinda ya sa ta ci galabar sace zuciyarsa dan ta kasance mai tausasawa a gabansa, sam bata wasa da yarda da yin hayaniya a gabansa, shi yasa baya taba daukan maganar Auta dan ita da koke koke, da hauka haula take son ganar da shi, har kwanan gobe, shi yasa a kulun yake yi mata kallon da Umma ke nusar da shi cikin hikima Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke ta dauki tissu mai girma ta shiga goge fuskarta, sannan ta koma ta zauna Kanta ta sada, ta rage muryarya sosai, kasa kasa ta ce" Allah ya huci zuciyarka, na nemi zurmawa dan bana son na ga wata fitina ta billo a cikin gidanka, mu barka da rigingimun cikin gari da na wajen gari mana? Ama sai abu ya nemi bilowa, ina son dakushewa ne dan kar Bahija ta yi aiki da isa da takamar ita yar uwarka ce ta kawo mana cenji a zamantakewarmu, ba zan lamunci haka ba, idan har na bata maka ka yafe min, na tuba ba zan kuma yin hayaniya a gabanka ba" Ta idasa tana karra sada kanta sosai, wanda hakan ya saka Auta kafeshi da ido tana ta yin magana da idannuwanta ama baya gane komai, sai kwalar da ta cika mata ido da ya iya gani kawai A hankali ya gyadawa Umma kai, hakan ya sakata sake sadawa ta furta" A tashi lafiya" Daga haka ta fice ta bar falon tamkar zata tashi sama ta kuma nufi bangaren NADIRAH Shiru ne ya karra biyowa baya, na yan dakiku Cike da darajawa, da girmamawa HUZNAH da bata taba kamanta irin haka a rayuwarta a gabansa ba ta sada kanta itama tana share yar kwalar da ta tarun mata a gurbin idannuwanta Ta rasa me yasa, ko kallon yarinyar ta yi sai ta ji wani katoton kaho ya tsaye mata a kirji, uwa uba irin abinda yarinyar ke nunawa , yayama za'a yi ta zo jiya jiyan nan ta nuna zata koya mata zama da mijinta? Yaya za'a yi ta zo jiya jiya ta zauna a kujerar da ta fi kusa da mijinta sannan ta dauki madarar UMUGHLUK ITIBEL ta sha har ta yi kyauta? Da kyar ta iya hanna kanta yin kuka, muryarta a raunane ainun ta karra sada kanta ta ce" Allah ya huci zuciyarka, Allah ya karra maka lafiya, na bari abinda nake gannin duhu a gareni neman rufe min ido, lamari ne na halitacen abinda ban isa da shi ba a zuciyata, in sha Allah zan kiyaye gaba,.....zan je bangarena na yi shafa'i da wuturi, Allah ya tashemu lafiya" Kallon abar sonsa yake yi, kallon matarsa mai laushi da nutsuwa yake yi, sosai ya yi mamakin gannin ashe ta iya fada?, Sosai ya yi mamakin gannin an hasalata da wuri haka, yana kallonta ta mike da idannuwanta da take tare hawaye ta sake rufa alkyabarta sosai ta juya ta bi ta dayar hanyar nan domin ba zata bi ta kofar shigowa ba bayi su fahimci halin da take ciki Tana tafia wajen ya rage su uku kacal NADIRAH ta yi wuki wuki ta kalli wannan kujerar ta kalli wancen, watau kujerun Umma da HUZNAH, sai ta ji kamar wajen yanzu yana neman yi mata yawa, dazu kuwa da abokan hamaya wajen har kadan ya so yi mata, dan so ta yi a yi ta yin rikicin har safe "Kin san daraja da girman uwa kuwa?" Ta tsinci wata murya, mai cike da kamala, da nutsuwa, uwa uba da kaifi a zuciya ta daki kunnenta A hankali ta juyo ta kafe fuskarsa mai dauke da rawani ido, a yanzu ta karra yarda da taken gadonta da ake yiwa maza, watau buzu babu rawani gwara babu wando ( ), in ba wannan ba, menene ta kangama rawanin a cikin dakinsa, falonsa, tare da iyalinsa? To shi yana cire rawanin nan kuwa? Sai kuma ta samu kanta da sake dora dubanta a wajen da shara sharan rawanin ya fi yawa, sam fuskarsa ba yaba yaba irin ta tsufa, to ama me yasa ake ce masa Aba? "Ita uwa, itace halita mafi daraja a duniya, ita wannan da kika yiwa rashin kunya tamkar uwa take a wajenmu, kin san darajar uwa kuwa?" Ya sake ambata a tausashen da ya sakata lumshe idannuwanta ta mayar da jikinta ta jinginar jikin kujerar sannan ta sake bude zaburarun idannuwanta ta zuba a fuskarsa A rants take ayana magana kamar haka' Sannin darajar uwa, ya sakani fadawa a bakin kura, sannin darajarta ya sakani tarban aradu da kai, sannin darajarta ya sakani juya baya na baro wanda nake so dan zuwa na rayu da bakin rayuwata, sannin darajarta ya sakani zama tamkar gimbiya bayan ni ba kowa bace face mutun dan Adam, ka sani da ban san darajar uwa ba, da yanzu wata maganar ake yi ba taka ba!' Auta