Sashe 67
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mun dawo, zamu dora in sha Allah *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 4 Da sauri ta juya ta nufi bangarenta dan zuwa ta yi kiran numbarsa, saima ta manta da neman inda Auta ta shiga domin gani take yi wannan rikicin ya fi na neman inda mahaukaciyar y'ar nan take Tunda ta shige ta zauna ta shiga kira a karamar wayarta gaban munafukan bayinta WA'INDA bata boye masu komai Kira ta ringa yi har sau uku ama ba'a daga ba, a dole ta dakatar tana hucin dake fitowa daga cen cikin zuciyarta tana kallon waje daya, domin ta sani ba'a masa kira sama da biyuma , idan ka yi daya biyu bai amsa ba ka bari zai taboka da kansa ne Daya daga cikin bayin ta kara sada kanta tana fadin" Allah ya taimaki sarauniyarmu , sannan uwar UMUGHLUK ITIBEL, Allah ya karawa Gimbiyarmu lafiya da nisan kwana, zamaninki dawamame ne Uwa a wajen zaki, sannan mata daya kwal a wajen ja gaban da muke hari, me yake bata ranku haka ne?" Cike da hura hanci take dubansu, a kausashe ta ce" A tsakaninku ku uku, akoy wace ta yi sake da aikin da na sakata ne a cikin gidan nan?, Ina nufin akoy wace bata cika aikinta yadda ya dace ne?" Kusan a tare suke girgiza kawunnansu cike da gaskata mata yadda suka saba yi mata aiki basu cenza ba! A birkice ta ce" Da mamaki kuwa!, A tarihi a kusa kusan nan ASADEEK bai taba yin fita ba tare da na sani ba!, Rabonsa da irin haka tun yakin sakashi jikina da na yi wanda ni kadai na san irin rayukan da na kawar kafin haka ya samu, dan bama so ya waiga ya ga kowa sai ni kwalin kwal, a yanzu kuma gayacen ya fita ko ina ya nufa?" Wace ke yi mata leken bangaren UMUGHLUK din ce ta dauki magana tana fadin" Allah ya taimakeki, ta yiwu wani abin ya diro masa kai tsaye, irin mai dirowar nan ba tare da an shiryawa hakan ba, domin ni dai a jiya ina bangaren nan dan kuwa su Kamilu suka yi gadi ya barni na shiga da shigarkin nan, kuma ina nan ta fito da sasafe tana hawayen da ta saba na zo na sanar maki har muka sha dariyar abin, daga shi babu abinda ya faru hasalima sai da na tabatar ya hau salaya na yi anfani da ky din wajenki na fice da taimakon Kamilun, bayanshi sai fitowarnan tasa da kika ce mu dawo mu jirayeki zaki je da kanki Bangaren Auta dan wannan ta ce maki bata kwana a bangarenta ba" Umma ta sake yin jimmm, sai kuma ta mike ta nufi dakinta ta rufo ta karasa wajen akwatin da ta boye maganin da aka turo dan NADIRAH ta zuba masa a abinci ta dauko tana jujuyawa, Tunda aka kawo maganin ta so a yi anfani da shi, ama Nadirar ta nuna mata ba yanzu ba, wai ta dakata ta gama abinda take yi, kwata kwata bata san me yasa take sauraron yarinyar ba, abinda ta sani shine har wani shayin yarinyar take yi bata iya hawanta kai tsaye, ko dan tana da bakine? Ko idannuwan nan nara masu lulumshewa dake hadasa mata kasala da jin kamar ta janyota da karfi ta auka mata ne?, Akoy dai wani abu mai karfi a tare da yarinyar, ama kuma ta san ko ba komai yarinyar kamar ta san kanta, dan kuwa a irin yadda ta fara shigewa ASADEEK ta tabata zata gabatar da aikinta a kan tsari, dan hakama zata karra bata lokaci kadan ta gani! Tino NADIRAH da ta yi da yannayinta ya hadasa mata bukatar aikata aikin da ya fi komai dadada mata ruhi, hikimar ubangiji kuwa ya bige mata tunanin dake ranta na neman auta harma ta ba bayinta dama suka rufe su hudu a dakin suka shiga aikata masha'arsu! ( Subahanalah) Wani wiki wiki fa ita ta karaso falon bayan ta bude kofar ta shigo ta ja turus tana kallonsu kamar yadda suke kallonta Auta kam tsam ta yi tana karewa NADIRAH kallo, kasancewar cikin bargo ta yi barci suturarta a jike ya da ba wani bushewa da kayan suka yi ana gannin jikarsu, kai harta irin laushin da gashinta ya yi ya kwonta lambak zaka fahimci wanke kan ta yi, ga hijabin dake hannunta kasancewar milk color ne ana iya gane jikarsa a ido dan kuwa bata saka shi hasalima kunyarsa take ji a ranta ita kam, da shi fa ya rufe abin jama'a! Innarta kuwa kallon tsaf ta kata sai t dauke kai ta ci gaba da jera girkin fa suka yi ita da Auta ba tare da tace da ita ufan ba, domin alamun yan rikicin sun bayana a tare da y'ar tata, idan kuwa ta biye mata ta tabata zata juye mata borin kunya a kanta ne har ta nada nata duka a banza a wofi, Kai ta juya wajen agogon dakin ta kalla, a zabure ta dake juyowa tana auna irin awanin da ta dauka a cen kennan? Ita da tace a bar kofa a bude ba inda zata? Kai innalilahi wannan wani irin tarin abin kunya ne haka ke yi mata tarere a cikin jama'a? Da yannayin bigicewa tana ta taro kafadar rigar da ba faduwa yake yi ba ta ce" Ina kwana Innata" Innarta ta sake tsareta da ido sai kuma ta dauke kai ta ce" Lafiya, je ki yi wanka ki zo mu ci abinci" Fuskart ta takwakwaba nan da nan sai ga hawaye yana harhada kansa murya na gargada ta ce" Wanka kuma Innata? Me yasa zan yi wanka ni kuma Allah na tuba?, Babu abunda ya hadani da wanka Innata..........." Ta karashe tana sakin hawayen harda jan hanci fuska kuwa ta yi mata jajajir tana kallon innar tata Hindu ta ajiye kwanon dake hannunta tana tafa hannu ta ce" Indi idan baki yi aniya da saurin kukan nan ba ina mai tabattar maki idan na kama kifa maki mari ko Habu ba zai amsheki ba bale Aban birni, da kaniya kin yi wanka da safe ne? Yau ga ya yanzu kuma wankan ne zai zama rigima? Wuce malama maza ki je ki yi wanka na sabulu tas ki yi kwaliya ki fito mu debi girkin nan idan kuma kika jima a ciki in bamu cinye kazar ba ki ce min ba Hindun habu ba!" Ido ta kikifta harda su sauke ajiyar zuciya jin wankan ashe na sabulu innarta ke nufin ta yi Dakinta ta wuce tana harhada tafia dan har ga Allah ba fa rasss take ba, burinta ta yi wankan nan ta dawo ta sanarwa innarta abinda zai summar da ita, danma kar ta fada yanzu ne innar tace sai sun koma wajensa a haka a ringa mata gani gani? Auta dake tsaye idannuwanta a kan tafiyar NADIRAH suka sauka har ta shige dakinta tana cicin magani irin karma a wani kawo mata maganar da ba ita ba ta rufo a kan idannuwanta A hankali ta dora dubanta a kan Inna dake ta dawainiya da kwanuka sai sake goge su take yi tana dan wake wakenta kasa kasa sosai hankali Kwonce A hankali ta kai zaune saman kujera tana ta fama da tunaninta, har fada take yiwa kanta cewa me kuma ya hadara da irin wannan banzan tunanin? Ai ba huruminta bane sam, sai dai kuma katutun da abinda ta dan ba mai yiwuwa bane ya yi mata a kirjinta ya sakata sada kai ta yi wani iri Inna dake miko mata ruwan Adu'a ta ga bata amsa ba ta ce" Ke kuwa tunanin me kike haka da yarintarki da komai harda wani motsare lebe kamar kina rike da duniyar nan?" A hankali ta Kalli inna, zuwa yanzu ta gama gane Inna da yannayinta, shi yasa take biye da ita kamar jelar kare A sanyaye ta sake kallon hanyar da NADIRAH ta bi muryarta a dan sarke kadan ta yi dan murmushi ta ce" Ko me ya jima auntyna a kafa ne?" Inna ta juyo ta kalleta, sai kuma ta dauke kai ta ci gaba da hade hadenta a cikin nonon rakumin nan ta miko mata sabuwar tatsa ta ce" Dan kafa kai ki shanye wannan ki bani" Auta ta amsa tana kallon yadda nonon ya cenza kalla , tana kallon nonon ta ce" Inna menene a ciki?" Inna ta tabe baki ta ce" Haka fa, ku kam aikin da kuka fi kwarewa a shi kennan, tambaye tambaye baku iya nema ba, sai a riskaku ku ringa yada kai kamar kadagaren da ya sha jifa, Allah na tuba sarauta ko ta makada ana jifa ana shige da fice bale masarautar AGADAZ?, Gashinan ita wancen ai abin inaga a jikinta ne ko? Tunda ai labari dai kasa kasa ana jinsa sai hakuri, ki kafa kai ki shanye ki bani malama maza kuma ki shige ruwan cen da na tara ki yi wankam na zo na maki turare du kin zama wata sangayayiya kina tafe kamar baki da laka a jikinki, ni ba zan yarda da wannan iya shegen ba, ku zagine ku amshi gyara da nemam tsari ba iya kwaliyar da takun kasaitar ba kina raye makashinki a tare da ke, kuma abinda kike tunanin a kan Indi da aban datawa hakane , wai ni za'a yiwa magana a rufe jama'a? Ku dai Allah ya shirye ku baki dayan ku!" ....... Sababi Inna ta ci gaba da yi har ta shige Kicin ta shiga hasa wutar da zata yi masu turare turarenta da tace Habu ta tuta ya amso mata ta bar Auta kamar ta summa a tsaye Da sauri ta kafa kai ta shanye madarar sannan ta nufi dakin NADIRAH *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 5 Nadirah na zaune tana mulka kurkum a jikinta mai hade da madarar gari dan shiga wankan mai gaba daya domin sai da ta kunce kitson da innarta ta mata dan ta wanke kan gaba dayansa ta dago tana