Sashe 29
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nawa tana cewa zasu gudu idan aka hanna masu junna? Dan ubansa ba kudin aurensa aka kai ba? Me yace mata? Ciwon yatsa yake yi yana gindin babarsa!, Kuma ya dace ne ka ce da ita mamanta ta yarda, kai ka yarda haihuwarta aka yi dole ta yi biyaya, idan har NADIRAH ta kai wajen da zata bijire luma ba sai mu janye mu zuba mata ido ba, Yaya bana cikin wannan tafiyar, lalle abin ya zo wani iri, an mata wani kwana kwana bayan ya dace ne mu fuskanceta, ni da take wajena nakan fada mata abu kai tsaye ne, sannan na nuna mata a adini ba haramun bane ko haramun ne, koda ta yi kuka zata dawo ta yi hakuri! Bata fa kai wajen da ba zamu iya tankwasata ba yaya, haba dan Allah!" Ta karashe babu ko digon hawaye a cikin idannuwanta sannan ta juya wajen NADIRAH da ta yi dif kamar ba ita ke rizgar Kuka ba ta fuslanceta ido cikin ido ta ce".NADIRAH tsaya ki ji, maganar da aka fada maki gaskiya ce, bamu yi labe labe da kame kame ba dan muna jin tsoronki, mun yi ne dan muna gudun tashin hankalinki da rikicewarki, ba bacin ranki ba!, Idan mu namu tashin hankalin ba komau bane a wajenki ki bijire ki fice ki tafi ga kofa nan, NADIRAH kar ki amince dan an ce za'a batar da mu, kar ki ce zaki amince dan farin cikinmu, domin hakan na iya sakawa a cin maki da wuri, ke hakan na iya sakawa a wayi gari ki amshi gubar da zaki kashe Sarkinmu!, Ki shiga uku a duniya sannan ki je kiyama ki hadu da ubangiji, NADIRAH ke baiwa ce ba kowa ba, le yarmu ce, mu kuma bayi!, Ba maganar kina sonshi ake ba, ba maganar kin tsane shi ake yi ba, magana ce ta damar da Allah ya baki ake yi, wace kina iya cenzata da izinin ubangiji!, Nadirah gaskiyar mahaifiyarki ke ba jaririya bace, ba kuma dai na maki dogon tarihi ba, ke ba kurma bace a wajen dandali, a cikin kauye, a wajen sarakan kauyenmu, a bakin samari da yan mata masu shiga birni kina jin wanene UMUGHLUK ITIFAL!, shi din Uba ne, kuma kimarsa ta fi kargi laban bakina!, Yanada daraja, dan mutunci ne, mai kishinki ne ke talaka, kina iya zaunawa ki yi nazari idan zaki zauna mu tatauna ta yadda zamu ci karfin makiyan UBAN GIDANMU mu tatauna, ba dan maganar soyaya ba, bamu kawota kusa ba!, Ki yi dan ceto ne, ki yi domin Allah, idan komai ya lafa ta yiwu yana iya sawake maki cikin ruwan sanyi , idan har Allah ya bamu nasara yana iya yi maki abinda kike buri, a yanzu kam bara muke, kuma Umarni muke baki, dan ki kasance mai biyaya a garemu ba a garesu ba!, Ta yadda zamu buga wasan biri da ayaba!, Babu makiyinki a nan, kar ki kuma manta abinda nake fada maki *BA KOMAI DA KAKE SO KAKE SAMU BA, BA'A TSANANTA KIYAYA KO SOYAYA, ADU'A ITACE MAKAMIN MUMUNI!*" Daga haka HINDU ta juya tana ficewa a dakin tamkar zata tashi sama ta nufi nata dakin ta bude ta shige a hankali itama ta silale ta saki kukan da ta rike da dukkan karfinta a gaban y'arta, kwarai da gaskiyar yayarta, basuda isashen lokacin da zasu tsaya wasa da NADIRAH, idan suka ce zasu tsaya har ta bada amanarta ta laluba da rarashi da nuna kauna da meye meye meye ko? Sunna ji sunna gani wankin hula zai kaisu dare, itace a kauye, ama ga dukkan alamu ta fi yaya sannin rikicin wasu marikitan!, Shi a tunaninsa zasu je lai tsaye su ga mutumen da shekaran jiya da kansa yace sai a jima ana son ganninsa ba'a samu ba su kai masa wannan magana mai kama da tatsuniya kai tsaye dan shine aljanin sannin abu da hawa kan abu ya yarda ya hukunta bafansa? Idanfa yana tare da wanda koda za'a gile kansa ba zai taba yarda da cewa yana iya masa karya ba ya daurewa bafan nasa? Idan a wajen yin binciken Bafansa ya juyar da komai ya hau kansu fa? Shikenan sun zama mararsa ilimi dan basu je boko suka nitsa ba ko? Lalle zasu nuna masu islamiya itace tushen komai, a cen ake koyar da komai, su kuwa yayan malamai ne ba iya Alkur'ani suka karanta ba, da izinin Allah zasu kai ga ci! Itafa dama a duka kaf rikicin tafiyar y'arta take ji, tunda ta ji yanzun ko? Zasu ci karfinta in sha Allah! Irin zaman da ta yi a saman gadon bayan fitar innarta dole ta baka tausayi Kamanin fuskarta kana kallo zaka gane a wani hali take Fuskarta ta yi jajajir haka idannuwanta sun yi jajajir A zaunen da take ji take yi tamkar duniyarta ce ta zo karshe a yau Tana kawo magangannun nan ne sala sala tana bajewa da irin yaren da zata gane Da ace iya innar birni ce abin ya tsaya da ta tabata da sauki, domin dama innar birni ba fai fushi ba Sai dai magangannun innarta sun sakata a halin ita ba mutuwa ba, ita ba rayuwa ba A irin zaman da ta yi Allah ne kadai ya san halin da take ciki Mahaifinta ya sake zama a gefenta, muryarsa a tausashe sosai ya fuskanceta ya ce" Nadirahna, ki yi hakuri, ki yi hakuri kin ji? Ki yi hakuri sannan ki fadawa Allah, abin nan fa kila wa kala ne, ba lalle bane ya tabata, idan muka fadawa Allah shine zai yi mana zabi, sannan kar ki saka maganar Aminu a ranki, Aminu namiji ne kamar duban sauran maza na duniya, a kanki ba zai kashe kansa ba ko ua bijirewa iyayensa, ki dauka hakan ne alkhairinki, domin koda innarki bata da gaskiya a wani wajen tanada a wani, mahaifiyarsa bata sonki NADIRAH, nima ba zan taba bashi yata ba, domin koda yar Allah bani ce ke ina son abina, kema yar gata ce, kuma ki sani idan auren nan ya tabata ba yana nufin zaki dawama a gidan sarautar bane, na san bakya ra'ayin rayuwar sarauta, idan har Allah ya bayanar da gaskiya Nadirahna zai gode mana sannan ya salameki salim alim kin ji? Ki kwontar da hankalinki dan Allah ki fuskanci abinda yake gabanki, domin yaki ne mai girman gaske, a fada mai tsaurin gaske kin ji?" Bata iya bashi amsa ba, ama irin yadda take kallonsa ya san tana jinsa, vai bar dakinta ba sai da ya shinfida mata darduma da carbi da alkur'ani sannan ya tafi ya daura alwallah shima ya fito falo da dardumarda ya fuskanci gabas, domin ya san a yau ba zai iya rintsawa ba ko yaya ya so rintsawar A bangaren NADIRAH kuwa, a lokacin da ta fuskanci kowa ya fitta daga dakin nan an barta daga ita sai halinta tamkar wace ta rasu aka kawo kabari ta karra saukowa kasa gaba dayanta daga saman gadon tana kallon kasa ta ringa auna komai dala dala, tun daga bayanan mahaufinta,na mahaifiyarta, na innarta, irin gidan da suke ciki, komai da komai sai ta samu kanta tamkar mai hauka sabon kamu Salayar da mahaifinta ya shinfida mata ba itace a gabanta ba a irin wannan lokacin da ta nutse cikin kogin tunanin shin ta mike ta dadaura wani abu ta shake kanta ta bar duniyar kowama ya huta ko ta mike ta dira ta tagar nan ta gudu idan safiya ta yi a nemeta a rasa? Ta jima tana kan wannan shawarwari biyu, wa'inda suka karrawaa kukanta karfi ta yadda tta ci kukan da bata taba irinsa a duniya ba, irin kukan nan da zaka iya fasaltashi da kana yi kana fatan dama mutuwa ka yi da irin wannan ranar? Irin kukan nan da shedan ke karra masa siga har ka ringa jijiga kana gannin ka zo duniya a banza ne, kukan kana yinsa ne kana auna rayuwarka tun daga lokacin da ka malaki hankalin kanka kana auna me ka yi da tsauri haka ta sameka,? Kuka ne kana yi kana tunanin aanya mutanen dake zagaye da kai sunna kaunarka kuwa? Irin kukan nan ne wasu kkan kashe kan nasu, wasu kuwa su fada a mugun hannun da zai basu shawarar guduwa............ Tun tana jin murya r kanta har ta dawo tamkar madiriritsi ya danneta tana ihu babu mai jinta A hankali yinwa ta fara dawo da ita a doron duniya Tun da sauran sawaye yinwar ta ringa kwakularta Karfin Adu'ar iyayenta ne? Allah ne ya yi ita din ba zata kashe kan nata ba? Ita dai yinwar nan ta sakata bude ido ta yi tsuru tana jin tashin hankali kamar ana rarakarta A hankali ta shiga auna yaya mutuwar kennan? Uwa uba idan ta je a wannan halin yaya zasu kare da walakiri kennan? Wai shinfidar kennan A hankali ta shiga tunanin iyaye A duka kaf abinda suka roka a wannan tashin na farko wanda shine na farko a tarihin rayuwarta cikin duban wanda suka yi mata Yau ko a shegiya suka haifeta sun mata adalci da basu bi da cikin ta magudadar ruwa ba Uwa uba suka jure shirme nata da sakalci A hankali ta gangaro kan wace bata yiwa laifi Idannuwanta ta rintse da zafin gaske da ta tuna kalaman innarta A hankali ta kawo maganar a namijin kansa Haannayenta ta watsa tana tunanin wai a cikin wanda suke kira sarkinsu, da wanda take keta rantsuwar tana iya guduwa a kansa wane ya cencenci bijirewa iyayenta a kansa? Namiji dai sunnansa, zungundumin katon da ba miji yake a wajenta ba bale tace mijinta ne ai maganarsa na kan ta iyayenta Kennan yaya sunnantama? Zungureriyar yar iska marar rabo? Aminu baa ciwon yatsa yake yi ba, Aminu angwoncewa zai yi? Shi kuwa dayan azalumin za'a kai masa ni shima! A gaskiya a cikin biyu bata ga daya da zata bijirewa iyayenta saboda shi ba Manyan azalumen ya dace ta yi yaki da su, Ita marar gata ko? Iyayenta bayi? Abinda ya fi sakata tsanar rayuwar gidan tun tana yarinya idan mahaifiyarta ta tafi sai dare ya ratsa take dawowa, idan ba fitsari ta tashi yi tsakiyar dare ba bata ganninta, idan aka yi wasa sai a yi kwana