← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 87

Sashe 45

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Asalamu alaikum jama'ata yan uwana masoya yan albarka grup SAJIDA PALACE, ina matukar godiya, ina miko maku fa godiyata, ban amsa maku tarin comment bane dan ban zauna ba, ama zan amsa ku kun san son so ne fisabililah , my zuciya na yin bubuduk idan ina karantaku , kaunarku da kaunata sun riga sun makaleni a kuluna, shi yasa zan wankeku da biyu matab albarka* Da wutar ciki itama ta ce" Aikin da kuke fadin zan aikata kina wani karra maimaitawa ai ni ban taba boyewa ba, gwara ni da ke, kema kin san abinda nake nufi, kuma da kike fadin idan sun isa su gwada tambayarki na yi, ki tabatar min domin dan na mareta Matar nan ta min wani kallo da rabona da na ga irinsa tun a lokacin da na rungumi kanwar Asadeek da tana kukan mutuwar iyayenta, idan kun san wata jaraba kuka hadoni da ita sai ku sanar min na dauki mataki, dan ni babu wanda ya fi karfina!" Tsaki Gimbiya ta ja ta kashe kiran ta wurgar a bayyane ta ce" Shashasha ko ita wa? Idan ta tashi burgarta ta rufe ido ta ringa ihun babu wanda ya isa ya fi karfinta, zaki ga fin karfi ne, domin wannan aiki da za'a aikata tsumi tsumu sai kin samu kanki a ciki, sai na ga ta tsiya, karamar aniya!" Tana maganar ne tana rufa alkyabarta bata tsaya kula kowa ba ta dauki hanyar bangaren mijinta, dan ta tabata da wahala in ya yi sallar asubahima , ta yiwu yana cen yana rizgar barcin asara Tana zuwa ta kwashi wani kayan haushin Sama sama ta ringa jiyo muryarsa yana fadin" Yauwa yar albarka rike da kyau, dan matsa kan kin ji?" Zama ta yi tana ta karkada kafa a falon har wani yangwamamen ihunsa ya karade wajen sannan ta ji shiru Mikewa ta yi ta shige dan ta tabata a irin lokacin shi kuma ya shige bayi dan ya wanke jikinsa Tana shiga ta bi yarinyar da kallo, yarinya karama, sam bata santa a masarautar bama bata taba ganninta ba A rikice yarinyar dake goge jikinta da ya bata mata da wani ruwan jikinsa mai gari gari ta shiga rarumar kayanta jikinta na rawa tana kallon gimbiya da neman fashewa da kuka Bata ce mata komai ba sai da ta gama saka kayan nata sannan ta karasa ta mata wani shaka wanda sai da ya saka yarinyar fitar da idannuwanta waje a rikice tana kallonta A kausashe Gimbiya ta ce" Kin san hukuncin fitar da maganar kin zo dakin nan kin aikata wani abin ko baki sani ba?" A rikice takebada amsr ta sani muryarta na fita da kyar Gimbiya ta saketa ta karasa ta buda kayan mijinta ta dauko kudi ta watso mata sannan ta amshe wayarta ta cire layukanta ta nuna mata hanyar fita A gurguje ta idasa daura nikaf dinta ta fice hankalinta tashe, du gani take yi kamar biyota zata yi ta kasheta, domin a cikin gari sunnanta ya baci iya bacewa Fitowa ya yi yana dan washe baki dan ya gama zubar da tsiyarsa a titi Turus ya yi gannin Gimbiya, sai kuma ya daure fuska yana fadin" Meye?" Gimbiya ta kwashe shi ta watsar tana cire kanta ta ce" Jakadiyar Kasar AGADAZ ta yi kira a kan abinda ya fara fuskantarta, shine nace za'a turo da maganin nan a yi abinda ya dace tunda wuri, dan bana son lamarin wasa, tunda farko na so ace an yi, idan gangancinta ya saka ta aikata abinda za'a gane ta sakamu a matsala kennan" Dakin ya karra bi da kallo, ya kalleta kamar bai san me tace ba ya ce" Ke ima yar mutane?" Goshinta ta dafe da takaici ta ce" Ka san dai da ranshi ba zan yi wasan kashe yar mutane ba ko?, Ta tafiyarta " Kafadu ya dage ya kai zaune yana lalubo wayarsa ya ce" Na sani, abin naki ne wani lokacin kamar baki da imani" Da takaici ya kumeta kasa ce masa ci kanka ta yi, kawai ta yi zurru tana kallonsa har ya gama rage girman idannuwan nasa da kyar ya lalubo number Umma ya buga mata kira Takaici ya saka gimbiya girgiza kai, watu bama zai yarda da maganarta ba sai ya ji ta wancen ko? Bata tashi kallonsa a zabure ba sai da ta ji ya ce" To ke uban wa ya aike ki marin yar Fadimata?, Ku walahi kun cika neman jaraba, su fa basa dukkan ansu, a laluma ya dace ku bita ba da masifa ba, sam baku iya cin ribar duniya ba kunna abu kamar mahaukata, ke baki tambayeta ta gwada maki gaisuwar ba kika dauketa firkyau firkyau kuka tafi?, Tunda kuka kwana ku dukanku har yanzu bai neme ku ba lafiyar ce, ki tashi kawai ki je yadda kika saba kicin da sauransu tunda kece da ikon komai matarsa hoto ce tana labe!, Zan gani zuwa jibi za'a kawo maganin sai ta gani in ta daidaita lokacin ta ga ya dace kawai ta bada masa, ke ko shaka masa ne ta yi a wuce wajen" A haka suka yi salama, gombiya na yi masa wani irin mugun kallon da ya sakashi rafka tagumi ya ce" Wani lokacin sai na ga kinai min kallon nan kamar zaki kasheni ki huta walahi" A ranta ta ayyana ' Dama inada wannan damar, da ina mai tabatar maka ba zaka kara minti daya ba' A bayane kuma ta ce" Kai kake bani mamaki, ina tsoron idan Allah ya tashi kamaka ka tube zirr ka bi Fadime da gudu, Allah shi kyauta" tana gama fada ta juya ta kama hanyar ficewa, shi kuma ya daga murya yana fadin" Ba amen ba bilahilazi, yar bakin ciki ni da ita ai yar daka ce ba yar hanya ba, sai dai ki mutu!" ( Wannan shine huldarsu, fahimtarsu, cin kansu, Allah ka sa mu dace) _____________________________________ Da yamacin ranar ta samu iso zuwa bangaren HUZNAH, ziyarar da UMMA bata ji ba kwata kwata, sai bayan isarta labari ya je mata daga bakin masu kai mata tsegumi, watau daidaikun mabiya bayanta Tarba ce ta salu ta gani ta fada, tarbar da ta bata mamaki, haka ta zuba ido tana bin yadfa suke gabatar da huldarsu zuciyarta cike da mamakinsu baki dayansu Bayan sun gaisa, su biyu ne a saman kujerun, sai bayin dake duke a kasa kowace kanta a kas , ba'a basu damar fita ba, dole zasu zauna ko me zai faru ya faru a gaban idannuwansu da kuma kunnayensu NADIRAH dake zaune, tauna kalmar da aka ce ta zo ta bada ta hakuri da abinda ya faru jiya take yi a harshenta, sai dai sam ta rasa ta yaya zata fara, domin a aunawarta bata ga menene girman laifinta ba, hasalima bambancinta da su shine bayar da hakuri a lokacin da ba'a aikata laifin komai ba Bayin nan kwaya hudu take kallo, kalmar dake saman harshenta ta samu fitowa a hankali ta furta" Ku bamu waje " Sai dai bayin da aka ce nata ne kadai ta ga sun mike sun fice bayan sun yi mata fatan a yi hira lafiya A nutse ta dora shemamun idannuwanta saman biyun da suka rage, wa'inda daya ce hasalin baiwar HUZNAR, dayar sunnanta dai ne baiwarta ama dukkan motsinta tana kaishi ne gaban UMMA Kallon da take yi masu, da hanna kanta dura masu ashariya gannin jam'u ta yi furucinta ama biyu basu basu wajen ba ya sakata muimui da baki tana karra kausasa dubanta a kansu Da yan yatsunta, ta masu alamun su fice, wanda hakan ya ba NADIRAH mamaki ainun, watau an nuna mata ga yadda ake sarautar ko? Sai dai kashhh, bata san ko a tsuman ranta ba domin ba wannan ne a gabanta ba Sunna fita ta dago dubanta ta dora saman Huznah Matar dai ta girmwga gaskiya, dan a yadda ta kiyasta zata kai shekaru talatin haka, ko da doriya, ama gatan wata zullu abinta ba'a cewa komai Akoy fa kyau dan kyau sai baranci....ta ayana a zuciyarta Kai tsaye, ta ce" Me yasa, a matsayinki na wace ta isa ta saka, ko ta hanna, kike zaune bakya shiga kicin ki girkawa mijinki abinci, ko baki iya ba?" Da sauri HUZNAH ta dago da idannuwanta, duba ta sauke a fuskar NADIRAH, wace take yiwa kallon BAHIJA, Sai ta ji kamar zaginta yarinyar ke son yi, ko tana so ta nuna mata cewa ita bakuwar jiya tsal har ta kai wajen da zata iya nuna mata son mijinta? Ko tana so ta nuna mata bata iya girki bane?, Sai ta samu kanta da tsare NADIRAH da ido, sakon da aka kawo mata an ce mata ne zata zo gaisheta, da bayar da hakuri, ama a zuwanta ko gaisuwar ce mata ta yi sannu fa da hutawa tanai mata wani kallo kamar ka tile kayan wankin nan, a tunaninta ko dan girmarta da ta yi ai ya dace ta girmamata ko?, Ko dan da ake cewa kishiya kishiya ce zata yi kishi da ita?, Ko nuna mata zata yi kusa ta fi kusa ne?, Ko kuwa tana so ta nuna mata ita yar sarauta ce?, To ai itama yar sarautar ce, idan bata da labari bara ta sanar mata A nutsenta ta ce" Mahaifina, shima sarautar ba cira ya yi ba ALLAH ya dattar da ke da tsufa a bisa girman darajarki BAHIJA" NADIRAH ta dan yi tsuru, gaba daya bata gane ina ta dosa ba, to ana zancen girki me ya kawo maganar mahaifi? Allah ta tuba itama nata uban ai sarkin ne, na dogarai,kowani sarki kuwa ai sarki ne a fadarsa wa bilahilazi! Baki ta tabe, ta ari yaren nutsuwar, domin ta kula idan ba halayar da Allah baya so ka dan aro ba ba zasu fahimceka ba, watau girman kai, ta yafa , a nutse ta ce" Allah ya huci zuciyarki....." Ta ajiye zancen tana tabe baki da tunanin me aka yiwa zuciyartama? Ta sake fuskantarta ta ce" Ban zo gidanki, fadarki, duniyarki, balbalin mijinki, dan na koya maki tafiyar da dukkan abinda ya dace ace naki ne......., Ki gane ban kuma fada dan na hadasa husuma bane... .., kawai gani na yi shi sarki mijin sarauniya ne, ba mijin makaraban gidan sarauta ba"
Chapter 45 · 0% Book details