← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 87

Sashe 28

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tarin alkawarin salwantar da rayuwarmu da suka yi, haka kuma muna iya guduwa wajen da za'a iya hukunta su, ama muka zabi amincewar dan mu kamanta kyautatawa wanda ke kyautatawa talaka, ta hanyar amincewa ba dan mulkinsa ko arzikinsa ba, zamu mika ki bayan mun gama fada maki cewa duk rintsi gwara a tsire ki da ki aikata abinda suke bukata, watau kashe UMUGHLUK ITIFAL!" Innalilahi wa inna ilaihi rajune, mahaifiyarta na magana ne, barin jikinta na ninkuwa ninkin ba ninkin, wanda ya tsoratar da su baki daya ama kuma ta ki dasa aya sai da ta kai karshen maganarta sannan ta dasa aya tana mai saka idannuwanta cikin na yarta wace girman idannuwanta suka karru , fuskarta har ta dauki ja dan rikicewa, haka kuma numfashinta ya wuce misali a irin gudun da yake yi, watau sama sama kamar zata bar duniya Da kyar ta iya juyo kanta da ya mata nauyi ta kalli mahaifinta, sai kuma ta kalli Innarta wace kukanta ke shiga kunnenta Tabas maganar nan ba wasa bace, tunda a yadda suka sakata a gaba suka yi mata da kukan Innarta kadai zai tabatar mata da ba maganar wasa a lamarin A hankali ta sake duban mahaifinta da ya jimke hannunta da karfi dan ya hannata barin jikin da take yi Idannuwanta na shigewa sunna budewa ta kalle shi , muryarta na rawa ta ce" Abannnnnn, abbannnnnnnah, kunna nufin nice za'a za'a yiwa aure da UMUGHLUK ITIFAL Na baban Garin Agadaz a matsayin wace zata je ta kashe shi?" Mahaifinta ya girgiza kai da sauri ya ce" Ba zaki kashe shi ba Nadirahna, idan kin je ba zaki kashe shi ba domin ke ba azaluma bace, ke ba makashiya bace....." "Abana , to ni ai ya mutun zan fi so Abana....., Abana ku ce min muna iya guduwa a yanzuma, domin ba zan taba iya kasancewa yadda ake so ba, Abana kun san da wanda nake so ko? Kuma kun son bana son rayuwar sarauta ko ta dakika guda ce ko?, Abana ku taimaka min ku ce min zabi gareni, dan zan iya ce maku ya mutun ba zai dameni ba da a kaini gidna sarauta!" Ta fada muryarta a mahaukacin raunane, hawaye na bale mata, haka kuma tana haki tan sakw kure fuskar mahaifinta d ido Hankali tashe mahaifiyarta ta ce" Kina nufin, gwara ki kashe shi da ki je aure gidansa?" A zabure ta zarro ido tana girgiza kanta, muryarta a raunane ta ce" Ba zan kashe shi ba, Innar birni da na kashe gwara a samu gawata, ina fata da na kashe gwara a wayi gari a samu gawata, ama idn ya mutun ni kam babu ruwana, innar birni ku ce min shikenan mu tatara mu koma LABA kun ji? In sha Allah ba zamu kuma dawowa birni bama kun ji inna?" Mahaifiyarta ta ja numfashin samun dan kwonciyar hankali, dan har ga Allah ta tsorata da farko Komawa ta yi ta jingina da jikin gado ta ce" Ki yi hakuri, ki mana biyaya, bana son jan magana ki je dakinki ki yi sallah ki fadawa Allah, idan har alkhairi ne Allah ya tabbatar, in ba alkhairi bane Allah ya kade ta hanyar da kowa zai ji dadin abin , ki tashi kawai ki tafi zamu sake zama gobe in sha Allah " Da mamaki Mahaifinta da Hindu ke kallon Innar birni, amaa ta hade fuska tama daina kallonsu Magana abanta ya so yi ama innar Birni ta bashi barin fuska ta kara hade fuska alamun bata son maganar Hindu ta sake kallon NADIRAH dake cicibawa jikinta gaba daya sai bari yake har kanta ba a daidaice yake ba, sai zabura take yi, kana kallonta zaka gane magana take son yi ama tana tsoron innar Birni Tana idasa mikewa ta juya zata fita sai ji suke dimmmmmmm ta dimu a kasa ba numfashi a tatare da ita A haukace suke rige rigen karasawa inda take Da tsawa mahaifinta ya tare hannun Innar Birni ya ce" Ki barta, kar ki tabata Fadima!, Ki barta haka kar ki idasa kashe min ita!, Dan ni ina sonta, ina son abina!, Ko menene bako yake a rayuwarta, idan kika yi duba da irin kulafurcinta da abin, kuma mun zo mata kai tsaye da abubuwan da a maganar gaskiya sun girmami tunaninta dole mu sasauta, na san idan bamu yi mata da gaske ba, ba zamu iya tankwasata ba, ama kuma komai yanada lokaci, a kan me tashi tsaye zaki fitar mata da komai kuma ki koreta? Ki tuna ke kika sab da rayuwar bauta ba ita ba, Fadimata ki tuna ke kika san irin haka ba ita ba, ita din bata rayu da haka ba, shi yaa bata zama inda muke , dan bata son ganninmu a yadda muke, shi yasa take tafiyarta a wajen da babu hasken lantarki, dan ta fi ganewa ta yi dire direnta a birni hankali kwonce da rikicin cikin gida!, A hankali zata shiga irin rayuwar nan ba tashi daya ba, so kike ta gujeki? So kike ta kulaceki? So kike abinfa muke so ta kiyaye dan kauna ta aikata dan kiyaya? Haba dan Allah, dan muna talakawa ba mahaukata muke ba Fadimata, sai da muka yarda cewa mun amince, idan baki amince ba a yanzuma ina iya fitar da mu, da mu saketa a birkice gwara mu gudu tare!, A kan me zaki ringa irin haka? Kin hanna innarta ta bita ta yadda ta saba binta, kin ce ba zata saurara ba, bayan na tabata da ita din ce ta mata hirar sai dai su sha koke kokensu zata dawo ta rarasheta!, Haba Zahrah da wane kike so na ji? Ke Hindu daukarta mu je dakinta, ke kuma kar na ga kafarki a nan!" Rai bace suka tafi suka barta a nan tana tsugune, a hankali ta silale ta hade kanta da gwuiwarta ta fashe da kuka tana kai hannunta daidai kirjinta ta jimke da karfi , muryarta cen ciki ta ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 1 Ba edditing Muryarta cen ciki ta ce" Allah, kaine gatan bawa, mai kudi da talaka, sarki da bawa, Allah ga yarinyata nan, ka tankwasa min ita cikin ruwan sanyi, Allah kai ka fi kowa sannin irin halin da nake ciki, wannan daula da tunanin zamantowarta matar mutun mai daraja baya dadani da kasa, na fi tsoro da zulumi a cen kasan zuciyata, bana iya ci, bana iya sha , bana iya rintsawa, dan na san wacece yata, na kuma san zata kasance ne a filin da babu wargi, ya Ubangi ka mayar da bakin abu fari a tafiyar NADIRAH"............... (Amen innar birni) A saman gadon dakinta Hindu ta shinfideta, jikinta na rawa a amshi ruwan da Abanta ya miko ta gumtsa a bakinta ta fesawa NADIRAH fesawar farko a fuskarta Sai dai bata farka ba, hakan ya saka mahaifinta a rikice ya ce" Hindu ko ki dauketa mu tafi asibiti?, Hindu ta ki farkawa?" Kai ta girgiza da sauri ta sake gumtsa da karfi ta fesa mata, wannan karron kam ta farka a rikice, sannan tana nan rarume rarume Da sauri HINDU ta rukunkumeta a jikinta tana bubuga mata bayanta tana ambaton sunnanta da sanar mata cewa itace a tare da ita kar ta tayar da hankalinta Murya a raunane, cikin yaren kuka mai tsuma zuciya ta ce" Innata, innata mu yi tafiyarmu, innata mu tafi, innata bana sonsa, bana kaunarsa, kuma bana son maganar a sakani kashe mutun, innata mu yi tafiyarmu wajen Aminuna, mu tafi innata" Hankalin Abanta tashe ya ce" HINDU, tunda tace bata so ni kam na hakura, ki kimtsata zan fita na sama mana hanya, na hakura ba maganar yi mata tunda bata so, tayar da ita ki shiryata mu tafi!" NADIRAH ta dago da sauri tana riko hannun mahaifinta tana gyada kai harda alamun fara murmushi ta ce" Abana, toh, toh Abana, mu tafi, ba sai an wani shiryani ba, mu je Abana, mu je!" "Mu je ina?" HINDU ta fada da dan karfi sannan a kausashe tana kallonsu Aban NADIRAH ya dubeta ya ce" Mu tafi ko'inama, ko ina mu je mana HINDU?" HINDU ta girgiza kai da mamaki ta sake saka hannayenta ta zaunar da NADIRAH da take kokarin mikewa ama jikinta ba karfi A kausashe ta fuskanci Aban NADIRAH ta ce" Ai kuwa yaya idan ta haka ne zaka iya yin wani abu gwara ka je kawai dakinka ka sasanta da matar cen da ka baro, domin zan iya rantse maka da Allah soyayar da kake yiwa yarinyar nan bata kama farcen wace take yi mata ba!, Itafa ta haifeta, du kusancinka da ita ba kai ka yi dawainiya da cikinta ba, ba kai ke gagara barcin dare idan tana wutsil wutsil ba, ba kai ke yawo, rana, zafi, ruwa, sanyi da ita a bayanka ba, yaya du wahalar soyaya da zaka nuna nake fada maka ragagiya ce a kan wace take yiwa y'ar nan!, Kuma ta fi kowa sannin wacece yarinyar nan!, Wai bama wannan ba, kana nufin zaka je ka rike makogwaron masu tsaron kofar cen, idan Allah ya baka Sa'a a kansu ta yiwu ka kashe su ka kwashe mu ka nufi wajen UMUGHLUK ITIFAL da mu ko ka je wani kauyen da a kankanin lokaci za'a kwasomu a dawo da mu nan?, Yaya kana tunanin du yar tsamar da suke tsakanin su idan ya tsaya a gaban dansa maganarka zata yi tasiri ne bayan bakada huja bayananiya wace zata saka a dubeka? Sunna aiki da ilimi ne, ka san wani laifi za'a lankaya maka kai da mu baki daya? An kar da dubu a kan laifin da ba nasu ba, ko kana musu?, Kai da zaka tayamu yaki a kan haka? Kai da zaka sheda mata Aminu fa karya ce a cikin gaskiyarta, zuma ce mai dacin balaki? Yaron da mahaifiyarda ta saka mata karan tsana ina take tunanin zasu je? Aminu ba zai taba biyota ba dan za'a masa aure da wata dan iyayensa na gaba da ita, itama ta sani, idan sun a shirmen soyayarsu uwarsa na tsaye a tsakiya, itama ta sani, sau
Chapter 28 · 0% Book details