← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 87

Sashe 87

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

bace ya saki jiki ya yi ta tafka lamuransa sai a cikin bulala ukun nan daya ta riske shi sai kuma a dawo ana dana sani ko a rikice a bar dabi'u na alkhairi a koma kwashe kwashe watau *RASHIN LAFIYA, TSUFA, MUTUWA*, wa'inda basa yiwa kowa uzuri ko su baka dana ka sake gwada wani tashin daban da wanda ka yi..................................." Ya ajiye maganar yana jan numfashi, dan ya zame masa jiki idan dai ya yi doguwar magana irin haka yakan ji ya gaji ne tikis kamar wanda ya yi wani aiki , sai yana yi yana ajiyewa ko zai iya karasa yawan maganar A hankali ya sake budar bakinsa ya ce" Tabas mun bata yarda, ta ci amana, a lamarinta yanzu abu daya ne ke cikin duhu a zuciyata shine rasuwar mahaifiyata, me ya hadasa kumburin cikin ANNA kai tsaye? Harta a likafaninta cikinta a tashe yake sosai wanda na jima a cikin tunanin nan, da kuma bakin jinnin da ya fita ta hancinta..............Shin matar nan ta kai wajen da ta kashe min uwata Auta?" Dummmm gaban Auta ya yanke ya fadi, zuciyarta ta shiga yi mata zafi domin tunano kamawar da ta yiwa Umma da irin rikicewar da ta yi kafin kuma ta ga ta sauke ajiyar zuciya a lokacin da ta ji jan numfashin Mai dakin Mai martaba na karshe, jan numfashi da ya yi wani irin tsayi ya fita bai kuma dawowa ba, kukansa a kunnenta da irin ajiyar zuciyar da ta ga UMMA ta sauke alamu na kwonciyar hankali ya wadata fuskarta, ama kuma sai ta kamata ta kaita dakinta ta rufo ta fada mata mamanta ta mutu , bayan tana cikin kukan wai mahaifinta ya rasu.............ta barota a ciki, ita daya kwal da ranta , ta yi kuka har nunfashi ya yiwa kofar hancinta kadan ta summe, wanda sai a washe gari aka ringa nemanta hankalin ASADEEK din a tashe kamar zai summa dan tashin hankali da kyar aka ganota a dakin nata summe....... A harhade ta sanar masa komai , dukkan abinda ta sani, irin abinda ta gani a fuskar UMMAN har rufewar da akai mata Umma ce ta rufeta a daki Ya jima idannuwansa lumshe, gaba daya ji yake yi me kuma ya rage masa na jin dadi a duniyar nan? Gaba daya ji yake yi sarauta bata yi masa rana ba , ji yake yi da ace su ba kowa bane da ba'a rabe su dan a cutar da su ba, saima yake ta kokonton anya zai iya sake yarda wani ya masa shigar da Umma ta yi masa a zuciya ta cutar? Wani tarin takaici gefe daya kuma yake mintsininsa, wannan maganar idan har haka ce dole zai ji ciwo a zuciyarsa mai tsanani, domin ya so ne ta rayu a cikin gidan kaso ta yadda zata yi doguwar rayuwa tana kallon abinda zai yi ta nukurkusarta, idan kuwa harda maganar kisa a ciki ai dole za'a kasheta itama, sai dai kashetan nan walahi walahi ba zai aikata da wuri ba, bi'izinillah sai ta yi rayuwar gidan kaso koda ta shekara biyu ne tare da fargabar yau ko gobe, da rikicin tunanin kwonciyar kabari da irin abinda ta aikata, sai ya sakata daki mafi muni da duhu ta yadda zata ringa auna a duniyar kennan ina ga lahira da nauyi irin nata? Sai ya wakilta malamai irin masu zafin wa'azin nan sun ringa zuwa du safiya ta Allah sun yi wa'azi a kan mutuwa da girman laifin wanda ya cutar da bawan Allah da irin azabar dake cikin wuta, uwa uba hanyoyin da za'a tarar kafin a kai tsayuwar hisabin, bi izinillah sai ya bata damar dandanar ukubarta daidai misali, ta yadda zata zamo mahaukaciya ta gasken gaske ba wai ta karya da hade haden magani ba, sannan zai zartar mata da hukuncinta ta hanyar bawa du mai iya ganni damar zuwa dan hakan ya zamo babar bulala wa mai rabon dacewa da shiriya tun kafin lokaci ya kure masa Daga hakanan kuma ya kasa furta komai sai idannuwansa da yake kawarwa baya so Auta ta kalla du irin yadda take son kallon dan kamalta abin a zuciyarta ta san yana cikin wani hali mai wutar fasara, "ABAH" Auta ta fada a sanyaye tana kallonsa Da kyar ya iya daga idannuwan nasa yana kallonta Auta ta lumshe idannuwanta cike da jin tausayinsa a zuciyarta, ita ta fi tausaya masa fiye da nata, dan shi ya zame masa dole ya dauka ya kuma shanye, ya dauki damuwarsa ya kuma dauki ta talakawansa Murmushi ta dora a saman lebenta, a hankali ta ce" Abahna, Aunty NADIRAH....... Au, Momy NADIRAH fa tana da ciki, Abahna zamu samu baby muma ABAHNA....." Ta karashe tana kallon yannayinsa a lokacin da ya zarro manyan idannuwansa yana kallonta, kamarma bai yarda ba, kamar kuma abu ya shigo maka kai tsaye, dama burinta kennan abin ya shigo masa kai tsaye , cikin tarin duhun da yake gani haske ya ratso alfarmar annabi da Alkur'ani............. Muryarsa a cen ciki ya iya sake budar bakinsa da kyar yana kallonta idannuwansa a wajen nan ya ce" Me kika ce?" Auta ta sake maimaitawa, yanzun har yar dariya take yi tana share hawayenta hadi da jan hanci Jikinsa ba karfi , ama kuma yannayinsa na cenza salo ya dan rangwabar da kansa aa sanyaye ya ce" kuma tsokanar da zaki yi min kennan Auta?............" Daria Auta ta saka mai dan sauti kadan, ta ce" Hello people, morning all Times New Roman mes New Roman !%),.:;>?]} $([{ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office eadd320200214feda1d7efc26510d338
Chapter 87 · 0% Book details