← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 87

Sashe 62

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bed din ya zauna yana sake kafe waje daya da ido Ba wannan aikin ya kawota ba, shi nama ya dace ya barawa wani nasa?????????? Gefen mataunansa ya dan cije, hakan ya sa kashin gefen fuska dake boye bayana adan ya nuna alamun abinda ke cikin zuciyarsa Ya barawa wani namansa?, Ba wannan bane ya kawota?, Anya zai iya hakura har sai an nuna masa abunda ke wasa da hankalinsa kuwa? A hankali ya sake lumshe idannuwansa, yana ji a cen kasan zuciyarsa anya zai iya ja da wannan rikicin kuwa? Bai san rikici irin na cen cikin zuciya ba, wanda ya sani na fili ne, a bayane, wanda zai ja tunga ya daka da kaffarsa a suma, ba irin wannan ba wanda yake daidai da boyayoyina da makaho Safarsa ya cire ya dora kafafuwansa ya sake harde hannayensa yana jin jikinsa na ta neman rikice masa 'Ama me yasa zata yi min haka?, Na yi mata wani laifi ne? Bata san girman hakina dake kanta bane?, Ko bata gane a kanta na san lamarin bane? Ya dace ta zamto mai tausayi da jin kai a gareni, domin nima ai mutun ne, ko laifi na yi mata ya dace mu zauna mu yi bayani ko?' yake ta ayana a sanyaye cikin zuciyarsa, jikinsa kuwa banda sake rikicewa babu abinda yake yi, a yanzu bai san me zai yi tunani a kai ba, shi dai ba zai ce bai san so ba, domin matarsa uwar gidansa soyaya da yarda ke rike da mu''amalarsu, da babu so da tausayi da jin kai da sun raba hannu a yadda suka kasance mararsa anfani ma junna, haka kuma shi ya san cewa tsakaninsa da wannan yarinyar babu maganar so , yana dai tunanin abinda ya sa yake matukar jin kamar numfashinsa zai tsinke idan yace zai zauna ya zurfafa a tunanin son gane wacece ita?, Me ta zo nema rayuwarsa?, Tana daya daga cikin masu neman gannin bayansa? Idan har haka ne to shi yaya zai yi da rayuwarsa? Zai iya fadin yana ji a zuciyarsa sai dai su kashe junna shi da ita, yana jin a ransa cewa a kanta yana iya tafka aikin da za'a ga rashin wayonsa, gata yarinya karama duda bai san shekarunta ba, gata yannayin wajen da suka fito ba iri daya ba domin a bayane yake ita din ba jinnin sarauta bace, kai lamarinta na hadasa masa ciwon kai mai tsananin gaske............... Da farko a zabure ta fito da gudu gudu ta nufo matatakalar saukowar tana waigen bayanta gabanta na faduwa tana Adu'ar Allah ya shiga tsakanin na gari da mugu, watau ita da wannan bawan Allah Tana hango matarsa zaune da kanwarsa ta ja ta tsaya tana sauke numfashi wani na korar wani tana daidaita kanta da tunanin abinda ya dace ta aikatawa matarsa dan ta karra dorata a kan layin mijinta cikin dabara ba a bayane ba Tafiyarta ta daidaita tana kin kallon jinnin dake gaban rigarta a ranta tana ayyana cewa' In sha Allah, na kusa gamawa, in sha Allah na kusa, ba zan tsaya sai sun banu damar sanar maka wacece ni ba , zan kwatanta maka ta yaren da na fi iyawa, zan kuma ganar da kai a aikace idan ya so sai ka kashemu dan mun shigo maka rayuwa!' "Ana hutawa?" Ta fada a hankali a lokacin da ya rage mata matatakala biyu ta idasa saukowa bayan ta dafe hannunta a jiki ta yi wani iri da fuskarta irin yannayin nan na raini A tare suka zuba mata ido sunna kallonta, irin kallon nan na karewa mutun kallo, bama kamar Bahija da sai da ta ji gabanta ya tsinke ya fadi da karfin balaki ta zubawa NADIRAH ido NADIRAH ta dan tabe baki tana jan hanci ta kalli sama, sannan ta sake kallonsu ta idasa saukowa ta karaso fallon tana kallonsu kasa kasa ta ce" Ama ai dai ba sai an ce maku ku tafi ba ko? Fisabililahi mace da mijinta a ranakun amarci a ringa sakata a gaba ana mata ido ido kamar an kama kwartuwa?, Ni kam wannan lamari nakunyana daure min kaina, ta yaya za'a ce du dare na Allah a ranar da take taku ko ba taku ba sai kun zo kwayakwayanku da kwarkwatarku kun sakan miji a gaba kunna ci yana ci an hanna ni yar soyyayar da abina?, Sam wannan tsari baya birgeni, kuma na dakatar da shi!" Ta idasa tana hade girar sama da ta kasa tana duban HUZNAH da ta wara idannuwanta da suka sha kwali mai kyau tana yiwa bakuwar jarabar da ta risketa fashin baki dan ta gane irin jarabar da zata kasheta ne ko ta jigatatata? Yau ita Huznah wata mace mai daura zani zata koyawa zama da mijinta ko cenza tsarin mijinta? Muryarta a hade ta sake dubanta da kyau, kafin ta mike tsaye tana dubanta ta ce" Ina gannin baki gane abinda kika tarar ba ko? Wama sunnanki? ....." Ta isada tana kallonta da kyau, sai kuma ta tabe bakinta ta ce" Ba wannan ba, sunnankinma ba shine a gabana ba, ina so na fahimtar da ke cewa da kika samu mijina yanada igiyar wata mattar a wuyansa, haka kuma in me kike takama da shi nima ina takama da shi, So ki iya bakinki da take takenki, ki kama kanki ki daina zubarwa mijina mutunci kina abubuwa kamar wata wace bata san NOBLESSE ba!, Kina saka sutura kamar zaki je gada kina fitowa ba alkyaba ba, na kasa fahimta menene a cikin kwakwaluwarki mai zafi dake juyata haka ba, abinda na sani shine babu macen da zata shigo gidana ta lalata min farin cikina da zamna da mijina, babu macen da zata nemi hautsina min lisafina!, Maganar soyaya kuma da kike yi kece bakuwarta, ina tunanin abinda wasu matan suka ci a kan soyaya ke ba zaki taba jurewa ba!, Ban iya fitina ba, ban iya rikici marar anfani ba, kar ki koya min dan Allah domin a kan mijina kadai nake zamtowa wawa har na daga muryata!" Ta karashe ranta na sake amsar gayatar NADIRA, wace ke kallonta hankali kwonce tana dan murmushin nan mai karra tafarfasa zuciya A hankali NADIRAH ta kalli Auta da ta mike fuskarta na nuna hankalinta na neman tashi sanadiyar abinda take ganni wanda ba zata so ace yana faruwa a cikin gidansu ba, bata san dalilin da ya sa take ji a cen kasan zuciyarta bata so haka ta fara faruwa da su sam, ba dan tana shiri da HUZNAH ba, ba kuma dan sun shaku da NADIRAH ba Murmushi ta yi ta dauke dubanta ta maida kan HUZNAH, a hankali ta ce" Kina ji, maganar Alkyab da wani wai shi nozlasssss ko me? Ke ta gano!, Yanzu Kina tunanin dan ina bakuwa a gidan nan na zamto bakuwa a duniyarki da ta mijinki?, Ai mace ko yau ta shigo gidan miji ta tardo mata uku ta zamto ta hudu sunnanta mata a cikin gidan kuma za'a kirayeshi mijinsu ba nata ita kadai ba, ko a rikicin kishinki a kan mijin naki kin manta wannan ne?, Mace kuwa, wace ke gidan mijinta, kina so ki ce min idan zata yi tsari na tsakaninta da mijinta sai ta nemi shawarar uwar gidansa dan tana wa?, Abinda yake farin ciki a wajenki ni shirme nake kallonsa, ko mace maki hauka nake kallonsa! Ki yi hakuri ba zaginki nake yi ba ko raina ki, gaskiyar abinda nake so a kiyaye min na fada da babar murya, daga yau bana so na kuma gannin kafar mace uwa ko kishiya ko kanwa a lokaci irin wannan idan kwanana ne a bangaren mijina!, Sunnan hakan sannin ciwon kai da iya kula da Namiji, kin ga idan kunna zaune na mika kafa na lalubo ta ASADEEK ai an yi abin kunya ko?, Gashi da sauki cafka....ke kin sani!, Bana son yin rashin kunya shi yasa na fi gane na yi bayani a saukake dan ku fahinta, saurana kwana uku mu dawo raba kwanaki, hakan na nufin gobe kina da damar gannin mijinki cikin wuni, da zarar dare ya yi a bar ASADEEK ya dan zaga ko zai iya wartar linzamin doki da karfinsa!" Subahanalah, Hasbunnalahu wani'imal wakil, wannan wani irin tashin hankali ne, jikin HUZNAH har rawa yake yi tana kallon NADIRAH Hannunta ta saka ta ja NADIRAH da karfintta ta mayar da ita gefe sannan ta shiga Haurawa sama har tana hade bibiyu tsabar hankalinta ya tashi, idannuwanta sun rufe, kai ba'a yi ba, ba za'a yi ba yar da zata zo ta wulakantata, zata je ta same shi a yita ta kare, ita ta san waye uban gidanta ba zai taba bari wata halita ta wulakantata ba a doron kasa ba tare da ya kare yancinta ba! Idannuwanta a bude kasa kasa ta ce" Toh fah, bara na gudu wajen Inna kar a ci zalina" Gana juyowa suka yi ido hudu da Auta, wace ke tsaye tana kallon ta, kallo irin na tsoro da mamaki Idannuwa ta fan kifta sannan ta zagaye a hankali ta nemi hanyar tafiyarta tana ta neman hijabinta fa idannuwanta "Auntu BAHIJA" Auta ta fada a sanyaye tana sake dubanta Turus ta yi da son tafiyar, tana ji a ranta wani abu na tabaa zuciyarta sakamakon muryar Auta da ta ji na rawa A hankali ta juyo tana kallonta, Auta kuwa ta sake kura mata idannuwanta da suka cika da kwallah a hankali ta ce" Aunty Bahija, har nima na daina zuwa wajen Abahna?, Aunty idan ban zo ba a cen take bani abincin cike da kayan maye, dan Allah kar ki hannani zuwa wajensa kin ji?" Wani irin duka zuciyarta ta yi, a hankali ta ji zuciyarta ta wani irin mugun karyewa ta shiga bin hawayen dake zuba a saman fuskar Auta da kallo Bata taba jin zuciyarta naa neman sakata a uku ba irin na yau da ta ji kamar zata fashe da kuka sanadiyar damuwar yarinyar dake bakuwa a duniyarta Kanta ta cire, idannuwanta suka sauka a kan hijabinta Da dan sauri ta karasa ta dauka zata saka ta sake kallin jinnin gaban rigarta, hakan ya sa ta zagaya baya wajen kujeru ta raage tsayinta sosai ta cire rigar sannan ta saka hijabinta ta dago a hankali tana satar
Chapter 62 · 0% Book details