← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 87

Sashe 27

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

aka amsata sannan ta shigo da tafiar da ita bata san ta shiga jikinta ba , a tunaninta yadda ta saba ne take yi, sai dai daga Mahaifiyarta, da mahaifinta, da kanwar mahaifiyarta ido suka zuba mata dan abinda ya shiga jikinta abin girmamawa ne su a wajensu Zama ta yi daf da Innarta tana sake kallonsu da son gane abinda yake faruwa, Da sauri HINDU ta mike tana fadin" Bara na je falo na dan dakata, zagayawa zan yi ina ga cikin nawa ke son hautsina min" Innar birni ta dubeta da kaifafun idannuwanta , fuskarta na daukan yannayi na ba wasa take yi ba, kuma ba zata bi abin da taushi ba ta ce" Ki zauna malama, bana son shashanci kin ji?" Mijinta ya sauke ajiyar zuciya kamar shi aka yiwa tsawar ya dan kura mata ido sannan ya maida dubansa kan Y'arsa da gaba daya ta zamto abin kallo a wajensa, kamar ba NADIRAH ba, dama yarinyar akoy ruwa irin na manyan mutane a tatare da ita, ama abin bai kai haka ba, a yanzu kwana uku kacal du kamar ba ita ba, akoy halayanta na da, ama kuma ta wani irin salo take sakinsu a yanzu HINDU zata ta yi ta sada kanta tana sauke ajiyar zuciya, hakan ya sa NADIRAH zubawa mahaifiyarta ido hankalinta na neman tashi Mamanta ta fuskanceta da kyau ta ce " NADIRAH, wannan zama da kika ga mun yi a nan, zamanki ne, mun zauna ne dan mu baki amsoshin tambayoyinki, sannan mun zauna ne dan mu yi magana ta fahimta wace zamu ganewa junna mu kuma dauki abinda zai tunkaromu da kyakyawar fahimta ko ma gudu tare mu tsira tare" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 1 Hpy juma'at A sanyaye NADIRAH ta ce" Inna lafiya? Kamar wani abu ke faruwa?" Innar Birni ta sauke ajiyar zuciya, ta kalli mijinta a tsanake sannan ta sake duban NADIRAH ta ce" Eh wani abu yake shirin faruwa, wanda bamu da tabacin zai kasance din ko aa, idan ya kasance bamu san yaya zai bile ba, abinda muka sani shine abin mai hatsari ne, da kuma muguwar rikicewa, wace bamu isa mu saka ko mu hanna ba, ......Abanta, ko zaka taimaka ka bata tarihin iyayen gidanmu a kanmu? Ka kuma shaida mata alkhairan ZAKIN SARAKAI?" Zamansa ya gyara yana hadiyar yawu mai daci a wuyansa ya fuskanci NADIRAH a sanyaye ya ce" Tarihi ne ginane, tsohon iko ne da yake da tasiri tun a lokacin da ake yin mulkin kama karya, An yi zamani kala daban daban na sarakai masu iko daban daban a NIGAR, an yi zamanin sarkin dake yiwa budurwa cabe a jikin garu har sai ranta ya bar gangar jikinta, magana ne ce ta zamanin da da yanzu, magana ce ta mulki mai matukar daraja da wanda yake na kama karya, ko a shekarar da democradiya ta shigo mana a shekara ta 1960, ta zagaya ta yadu mun rike har bayi sun tashi daga dabobi sun zama masu darajar da har ake basu albashi na bauta, ama bawa sunnansa bawa kuma uban gidansa ya isa da shi a kan komai, saukin abin da muka samu a cikin sarakanmu akoy jajurtatu da duka giga har suka fi iyayensu karfi da tsayawa a kan gaskiyarsu, basa tsoron kowa ciki harda mutuwa, domin sun riga sun san cewa mutuwa da rayuwa hukunci ne na ubangiji, kuma lahira ce dawamamiya....Nadirah shin kina fahimtar abinda nake fada kuwa?" NADIRAH ta sake fuskantarsu, har wata zufa zufa ke neman tarun mata a goshi, dan tsakaninta da wanda ranta ke hannunsa bata san dalilin da ya sa iyayenta sakata a gaba ita NADIRAH suke dauko mata wata magana kamar ta aljannu ba, yo ita me ya shafeta? Ita ba baiwar kowa bace gaskiya, kuma ita kam harkar sarkakiya irin ta sarauta sam bata sonta, magangannunsu kulun a cakule basu da abu a bayane, ita kam ina ta ga hankalin gane maganar Abanta? A hankali ta girgiza kanta ta ce" Abana, gaba daya ni ban san me yasa ake maganar nan bama" "Abinda ake son nuna maki, karfi, da ikon da Sarki yake da shi a kan bawansa, koda an shigo zamani na yancin kai akoy abubuwan da suke da karfi da tasirin da yancin kai ba zai goge ba, bale idan ba haramun bane, Abinda ake son sake nuna maki shine sarauta da kike dauka makiyiyarki itace gatanki, domin Allah ya yi umarni da mu yiwa shuwagabaninmu biyaya, sannan a zamaninmu na yanzu munna cikin zamani da ya kasu kalla biyu ne , a cikin tafiyarmu munna tare da rikitaciyar tafia wace ta hada adalin da yake adali a garemu da kuma adalin da yake adali a gare shi!, NADIRAH kin fahimci maganata?" Innar birni ta fada a kausashe, hakan ya saka Nadirah jin numfashinta na mata kadan a hancinta, a hankali ta dan ja gindinta da niyar matsawa kusa da innarta, sai dai bata idasa aikata hakan ba ta ga innar birni ta matso daf da ita ya kasance sun sakata a tsakiya A hankali ta kamo hannunta ta rike da kyau a cikin nata tana kallonta ta ce" A lokacin da mahaifiyata take raye,an yi rikicin da ya hadu fa shari irin na bayi, aka dora a kanta cewa lamari na zina ya shafeta, shi UMUGHLUK yana zartar da hukunci ne bisa hukuncin musulunci, an kaita an garkame har an saka ranar jefeta, ashe shi din ba wanda ke aiki da gadara bane, yana bincike ta kasa, mun gama fawalawa Allah komai mun kauracewa kowa aka wayi gari da sanyin safiya aka fitar da rakardar wanketa tas faga sharin nan, tun daga lokacin nake kallonsa da kallo mai girma a idannuwana, cikinmu irinmu mun fi a irga dake dauke da daraja mai girma tasa a kirjinsa, wadda bamu taba haduwa gamu gashi ba, ama kuma a kulun muna binsa da addu'a" "Inna me yake faruwa?" NADIRAH ta fada muryarta na mugun gargada tana kallon mahaifiyarta Innar birni ta ja numfashi ta ce" Abinda yake faruwa shine, kadara ce zata biyo ta kanki, ta yiwu fara ce ko baka, koma wacece ita kike iya dauka muguwa ko mai sauki ta yannayin fahimtarki, abinda yake faruwa shine hukuncin rayuwa dake zuwarwa bawa ne ya riskeki, watau babu bawan dake rayuwa d asalin yadda yake so, kowa da irin takun salon kadararsa, ko wanene!, Ba komai bawa ke nema ya samu ba, mun yarda da wannan, hakane ya kasance a kanki NADIRAH............" Yanzu kam har jikinta ya fara rawa, haka kuma sun fara bata tsoro, haba, gaske take jin wannan shorye shiryen da ake yi mata baya birgeta, kennan da lauje cikin nadi? A hankali HINDU ta ce" Aunty, dan Allah kar ki rikitata, ba a haka zata fahimci maganarki ba, Kim ga Indi dubeni nan kin ji?" Hindu ta fada tana juyo da NADIRAH, domin gani take yi wannan salo da auntynta ta dauka sam ba zai kaisu da ci ba, ba Nadairah kadai ba itam dake sauraronta jikinta rawa yake yi bale NADIRAH A tausashe ta kama hannunta tana kallonta ta ce" Kin sani cewa, wani lokacin abinda bawa ya nacewa a so ba shine alkhairinsa ba, da yawama soyayar ake kamar za'a cinye junna har a yiwa iyaye tabara, da zarar an shige gidan kuma a dawo kiyayar junna, tunda ba'a nemi zabin Allah ba ko?" NADIRAH ta ce" Innata, Aminu ya rasu ne?" Kai ta girgiza ta ce" Da ransa Indi" NADIRAH ta kalli abanta da innar birni ta ce" To menene? Ku fada min menene kun ji? Me yake faruwa ne? Kalli Innar birni kamar wace ke kuka ko?" HINDU ta karra hadiye nata kukan itama a hankali ta ce" Abinda yake faruwa shine, sun so bada yarsu aure wa UMUGHLUK ITIFAL dan ta je ta isar da bukatarsu na kawar da shi a doron duniya, sai ta kiya , kasancewar tanada damar hakan a wajensu, sai abin ya juye zuwa................" "Hindu" Aban NADIRAH ya fada a hankali yana katseta HINDU ta saki hannayen Nadirah ta sad kanta hawayenta suka bale A hankali ta juya wajen Abanta tana kallonsa Mahaifinta ya yi dan murmushi ya ce" kina ji?, Na amince da haka, innar birni ta amince da haka, dan baban abinda ya fi janmu amincewa da hakan shine tunaninmu zamu iya kare wani abun ta damar da Allah ya bamu, Gaskiyarsa da kare yancin talakawa ya siya masa makiya, barima ki ji NADIRAH, ina iya guduwa da ku, domin masu tsaron kofar cen su biyu babu abinda suka isa su yi, na tabata idan na shiga masarautar da ku na sanar masa abinda yake faruwa zai iya daukan mataki, sai dai tsorona shine , shin sunne kadai mafarautansa ko maciji zan kashe ban sare kansa ba?, Na karashe maki magana , a amincewar tamu mu din ba masoya zamu kasance a gaban idannuwansa ba, ta yiwu idan mun yi nauyin baki har muna iya samun mugun hukuncin da kawunnanmu ba zasu iya dauka ba....., Haka kuma cikin hatsarin da zaki je ana iya cin galaba a kanki, a haka duka muka amince NADIRAH muka salwantar da farin cikinmu, ba dan komai ba sai dan mu kamanta kyautatawa wanda yake kyautatawa bayin Allah " Irin kallon da NADIRAH ke binsa da shi, kamar tana son gane a fuskarsa me da me aka hada aka haliceta ne!, Muryarta na rawa ta ce" Aba , da me kuka amince?" "NADIRAH ke fa ba karamar yarinya bace, shekaru ashirin ba kwana ashirin bane, a birni ko a kauye kin isa ajiye ya'ya uku rass naki, abinda ake nufi shine an saka aurenki ke da UMUGHLUK ITIFAL nan da kwana goma sha biyu bi'izinillah, zaki je a matsayin yar sarkin garin nan, zaki je ki rayu a cen a matsayin matarsa, bisa umarninsu, sannan zasu biki da wani aiki wanda idan kika aikata ke da ubangijinki, watau kawar da shi a doron kasa!, Abinda mu muke maki nuni a nan kuwa shine, biyaya ta zame mana dole, itace abu ta farko da zamu yi a matsayinmu na wa'inda ke karkashinsu, muna iya bijirewa duda irin
Chapter 27 · 0% Book details