Sashe 64
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dake hobara dan tauri da cika ta koma ta yagune tamkar ta tsuma Idannuwanta ta rintse, jikinta na daukan rawa a lokacin da ta ga jikin nasa yake kallo, ga nata jikin a bayane a gabansa hannayensa a jikin cinyoyinta , a hankali ta barke da kukan da bata san dalilin fitowarsa ba, wanda ya fito daga cikin zuciyarta sannan bashi da amo mai karfin da zai saka yan waje su jiyo su, hka akuma tana ambaton sunnan ALLAH ne kirjint na dokawa da karfi da karfi Tabas sai a yanzu ya dawo hayacinsa, lokaci daya kuma maganar SHEIK ta dawo masa a lokacin da yake ce masa idan fa abin a jikin HUZNAH yake ne ake ta neman magani ana bashi shi kadai ita kuma ana gannin ai ba a jikinta yake ba?, Sautin muryar kukanta ya saka shi sasauta rikon da ya yiwa cinyoyinta , cike da tausayin iyalinsa ya myar da gaajeran wandonsa da kyar ya iya cira kafar tasa ya haura saman gadon ya janyo abin rufa ya rufa masu a jikinsu sannan ya janyota jikinsa sosai ya rungumeta yana sake lumshe idannuwansa muryarsa a raunane cen kurya ya ce" HUZNAH, ki daina kukan kin ji? Ki yi hakuri plz" HUZNAH cike da tsoro da fara tunanin to wai ko dai itace mai matsalar nan ta ringa rage kukanta har ta dauke kukan gaba daya sannan ta rukunkumeshi a jikinta tana cusa hancinta a kirjinsa tana dan girgiz kanta cike da tunani kala kala, sai dai yau da sauki take ji sanadiyar gannin har gata a jikinsa a haka ya rungumeta har yana bata hakuri, tabas bata da ja mijinta ba zai bari a wulakantata ba komai wuya!, Matarsa kuwa ta zo ta ga karshen zama a gefen mijinsu, uwa uba gata a jikinsa a ranar kwanan nata ta yi abinda take ikirrin zata yi a gani! ( )............................. Tsaf ta fito daga bayin dakinsa bayan ta yi wanka har ta dauro alwallar sallar asubahi sakamakon kiran da aka yi ta fito a hankali ta rufo bayin ta nemi ficewa dan bu ta boyayiyar hanya ta karasa bangarenta dan a tunaninta tuni UMUGHLUK ITIBEL ya jima a masalaci, domin da ta motsa a barcin ta tabata shima ya tashi daga barcin ya shige wani Bayin Saman gadon ta kai kallonta da shaukin farin cikin kwananta a samansa yau a cikin jikin mijinta, Karra kurawa gadon ido ta yi, gannin tabas ba abin rufar bane a sama shi ne ya sakata nufa da dan sauri ta hau a hankali ta saka hannunta ta yaye rufar ta kai hannunta da nufin tashinsa, sai dai zafin da ta ji a jikinsa ya saka gabanta yankewa ya fadi da karfin gaske , a tsorace ta dan shiga ambatonsa da sunnanyen da take kiransa da su irin na girmamawa tana tambayarsa bashi da lafiya ne? Me yake damunsa ne?, Gaba daya hankalinta tashe tana neman fashewa da kuka Idannuwansa da ya kasa dagawa dan zafin ciwo yake ta motsawa , sai kuma ya samu da kyar ya kamo hannunta ya kai wajen da har ya dan kumburar masa dan azaba yana neman kashe shi Dukka kirjinta yake yi, da sauri ta haura ta shige ciki, a matsayinta na mace wace ta san kanta daidai gwargwadon iyawarta ta shiga bashi taimako dan gannin ya samu sasauci cike da kula da tausayi da tarin soyaya ko zai iya fita masalaci, sai dai abin ya ci tura, domin tun tana yi da karfinta har kanta ya kage hannayenta suka yi sanyi ya kasa samun nutsuwar da ake lalube, hasalima yannayin bashi da alamun sadakawa sai dai sake yin kiri kiri Muryarsa a jigace , cen ciki ya ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 4 Muryarsa a jigace ya ce" HUZNAH???" Dagowa ta yi tana talabe kanta da ya kage tana kallon yannayinsa cike da tausayi, muryarta a sanyaye ta ce" Yaya zan maka ka samu nutsuwa ne?" Idannuwansa ya sake rufewa da karfi yana jin kansa kamar zai fashe, muryarsa a tausashe ya ce " Ki je ki yi sallah, kar mu rasa mu dukanmu" Idannuwanta ta lumshe wasu hawayen na sake ziraro mata a hankali ta ce" Yaya zan iya barinka cikin halin nan bayan na san idan ka kara wasu lokutan a haka zaka iya summa?" Jajayen da idannuwansa da har jan ya kafe ya fara yin duhun baki ya zuba mata, muryarsa a jigace ya ce " na ce ki je ki yi sallah, idan kin gama ku huta zan tashi nima na shiga wanka" A hankali ta sake shi ta dan matsa tana kallon yadda ya mike a hankali ya ja bu ya rufe jikinsa sannan ya nufi bayi da kyar yana wata irin tafiyar da take tambayar kanta a haka yaya zai iya tafia masalaci? Rufowar bayin ya sakata sauke ajiyar zuciya ta mike jiki a sabule ta nufi wajen alkyabarta ta mayar ta sake juyowa ta kalli bed din sannan ta fice ba tare da ta gyara ba, domin ba su ke gyaran komai ba akoy masu yi ( harda gadon da kika gama baza sirrin nan?) Da kyar ya iya yin wankan sama sama ya dauro alwallah ya fito Sallar kanta da kyar ya iya gabatar da ita, bale idan zai kai sujada sai ya ji kamar mararsa zata fashe biyu, kunnayensa na jiyo masa adu'ar masalaci watau har an gama sallah an yi karatu ana shafa fatiha ana ta yi masa adu'o'in alkhairi Idannuwansa ya lumshe ya kama abu ya mike da kyar ya nufo hanyar fitowa Sauka yake yi ko rawani bashi da shi a kansa, daga shi sai doguwar rigarsa da wandonta sai carbin dake rataye a jikin yan yatsunsa ya ringa sauka a hankali har ya saukowa hankali kwonce ya nufi biyauiyar hanyar falonsa ya bude ya shiga ratsawa yana dubawa har ya karasa kofar nata falon sannan ya dora yatsarsa wajen budewar ya cire lock din ya murda abin budewar ya dan bude shi kafin ya dakata ya shiga dan bubugawa yana sake jinginar da bayansa da garun Daga cikin falon kuwa, zaune suke Auta na kallon yadda Inna ke yiwa NADIRAH gyaran kai, bayan sun gama sallar asubahin Innar ce da kanta ta je ta dora masu abin kari sai kuma tace su zauna a falo su sha hirarsu, sai daria take sha idan Innar ta yi magana, tana matukar son sannin wacece innar? Ama ta kasa tambaya, hasalima tun jiya da suka karaso bangaren nan suka dan taba hira da ta so tafia fakat NADIRAH tace ba inda zata je ta yi zamanta a bangarenta yaya zata iya yin barci ita kadai a nata bangaren bata jin kadaita ne?, Ta daina kadaice kanta ita kadai ba kyau, sai gashi ta kwonta daki daya da wannan mata Inna sun sha hira da kayan dariya kafin su yi barci, asubahi na tashi kuma ta tasheta suka yi sallah suka taba karatu sannan suka fito dan dora abin kari, domin yanzu haske har ya fan fara fitowa kadan kadan, gaba daya jinta take wani iri, wani banbarakwai, ta gaza sakewa ta sha hira da dariya ne dan wannan lamarin kam bako yake a rayuwarta Sake bugawar da aka yi a hankali ya saka su juyawa su biyun Juyo da kan nata Inna ta yi ta hanyar jan gashin hakan ya saka Nadirah furta" Wayo kaina innata" Inna ta ce" Ke dilla juyo, ana maka kitso kana kauce kaucen kai da iya iskanci, ke ba za'a taba maku kanki ba ko?, To sai na caje maki" "Innata kamar ana buga wancen hanyar fa, dama a bude take?" NADIRAH ta fada tana dago kanta ta kalli innarta Auta kuwa da sauri ta mike tsaye tana kallon hanyar ta ce" Dama wani na iya bude kofar cen banda Abahna?, Idan a rufe take da ky ta ciki Abahna kadai ke iya budewa da yatsarsa kar aje wani abu ke faruwa a masarautar?" Inna da sauri ta mike tana daura zanninta a saman cikinta ta kalli hanyar sai kuma ta kalli Auta ta ce" Yar nan ban gane wani abu na faruwa ba? Abu irin na a tardomu a kashemu?" Auta ta yi tsuru tsuru, hakama Innar NADIRAH Nadirah ta kalli Auta ta kalli innarta itama tana jin hankalinta na neman tashi Zata yi magana ya dan miko hannunsa kadan ya rike abin kamawar ta ciki kadan sannan ya janye, hakan ya saka Auta zarro idannuwanta ta ce" Abahna ne" Gaban NADIRAH sai da ya kwonci kwonci ya rufto kasa, innarta kuwa ta dake kallon Auta ta ce" Makashin? Waye Abanki wai? Ki bude baki mana kina magana a kuryar makogwaro" "Inna wai ASADEEK take nufi" NADIRAH ta fada muryarya a sanyaye sosai Innarta ta zarro ido, sai kuma ta kame baki ta karasa kusan NADIRAH ta rankwasa mata dankwashi kasa kasa ta ce" Dan ubanki ban hannaki kama sunnan nan ba?, Kina nufin shine a cen?" NADIRAH ta dora hannunta saman kanta ta kwashashabe fuska ta gyada kanta Innarta ta tafa hannu ta duke kasa da hannunta ta tura NADIRAH kasa kasa ta ce" Jeki jeki yi maza jeki" NADIRAH ta turo baki tana kallon innarta ta ce" Ni kuma Innata?" Innarta ta sake dora hannunta a gefen fuskarta tana salalami kasa kasa sosai ta dubi Auta da abu biyu suka tsaye mata a rai, muguwar dariya da kuma tunanin me yake damun yayanta? Dama yana zuwa nan da kansa ne?, Ta ce" Ke kin ga wani bakon islanci ko? Tambaya take yi wa zai je, ce nai mata ni, nace ni Indi, in baki je wajen cen kika ji me Babanmu ke so ba sai na ci abinda habu baya so ina fada a gidan nan !" Da sauri ta nufi hanyar tana matsar kwallah, ta karasa ta bude tana leka shi suka yi ido hudu da junna, fuskarsa ta zama jajajir, yannayinsa ya zama abin tsoro, lebensa kuwa ya karra yin ja yana walwali , idannuwansa kuwa sam badu da dadin kallo A hankali ta kalli hannunsa da ya miko mata yana karra shanye dubansa , hannun ya karra girma