← Book details Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 87

Sashe 26

Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kuma ta koma yaren buzanci ta dube su ta ce" Barkarku da aiki, gaskiya kun iya aiki , Allah dai ya karra girma" Amsa a wani yangance ta samu, ita dai ba shine a gabanta ba, abinda ta dawo da shi ta karasa ta yi zaman kaka gida ta basu baya ta saka y'arta a gaba ta ciro leda biyu ne , dayan a cikin galan dan karami, dayan kuwa a kule a leda guda ta girgiza ta bude ta ce" Maza maude ki bani galan din da shi zan koma gobe in sha Allahu" Abin take kallo, sai ta kalli Innarta ta ce" Inna, shima maganin zahin ne?" Innarta ta harareta ta ce " Ni wai Indi a me kika daukeni ne ni? Ya du idan na miko maki abu sai kin tsatsareni da tambayoyi kamar wace zan saka maki susau a ciki? Kin maude ko sai na moda maki mari?" Da sauri ta kafa ta rintse ido a tunaninta wani dabri dabri zata ji, ko kaifin wani abin, sai ta ji rubutu ne babu dabri babu kaifi sai kanshin tawada da irin kanshin rubutun nan, dan haka ta shanye shi tassss, ta miko hannu ta amshi na ledar shima ta tila ta kafa a bakinta ta shanye shi tassss tana murmushi ta ce " Innata wannan ai rubutu ne dama kin saba bani walahaula a gida ai, na zata wancen abin ne maganin zafi ko me? Ki ga fa wanda kike sakani tsakiyar dare, innata sai na yi barci ba gaba ba baya barci ya yi masifar dadin nan kike sungumata ki tsomani wai dan kanoma da bakin duniya, Innata ki duba ki gani kika wuni kina rubuta yusufa kika wanken na sha wai meye ake yi dan Allah?" Hindu ta yi tsuru tsuru zata bata amsa mai murzartar nan ta taso da hadi na kwai , da sauro Hindu ta boye abubuwan da ta shigo da su tana watsa mata hakora Matar ta sakata mikewa ta dubi Hindu ta ce" Ki koma ciki, zan mata wankan madara" Hindu ta yi wata yar dukawa ta ce" Yanzu kuwa hajia, Yar gidan Inna sai na kawo maki mag anin zafin zan fada maki, ai zafi ke rarakarki yar albarka sai na dawo" Kamar ta bi innarta haka take ji, wai wankan madara, wannan abuma na kona mata rai, ruwan madara da ake sha a yi kat ita dumamashi ake yi a masa hadin su zuma da duminsa a sakata ciki a dora mata kokomba a gurmin idannuwanta a lafta mata hadin kwai da nescafe da madara a fuska a mata gargadin banda magana ko dariya kar ta bata fasalin fuskarta? Ai ita take kan gannin rayuwa , tsakninta da su bata san ba sai ta hada su da Allah ko ba sai ta yi ba? Ta dai zubawa sarautar Allah ido HINDU na komawa ciki ta tarar da Fadime ta gama girki tuni tana gyara komai , falon kansa yana fitar da dadadan kanshi ta zauna saman kujera tana fadin " Ya arahamani ya rahimi Allah mai gabas da yama, kudu da arewa, mai tudu d gangare na gode maka da ka dawo da ni lafiya ka saukoni daga saman jaki a cikin kasar sahara" Fadime ta sake juyowa da mamaki tana kallonta, ruwan da ta yi niyar daukowa ta dauko ta zo kusa da ita ta zauna tana kallonta ta ce" Yanzu tsakaninki da Allaj daga Timiya kike HINDU? Me yasa bakya jin magana ne ? Yanzu da ake tarewar nan da aka tareku fa? Kariya ba tana Adu'a ba muma kuma muna yi? Haba HINDU" HINDU ta dauki ruwan sanyin nan ta sha ya isheta ta ajiye tana yin mika ta gajiya ta ce" Aunty tunda na dawo ai shikenan, ama aunty na ga ikon Allah,malamai irin namu masu tsoron Allah, ba malaman tsubu ba, Aunty tsaf aka rubuce wakadimna kafa dubu arba'in da daya aka bani na wanke da dan ruwa kadan , sannan aka rubucen wasu na tsarin aka wanken na kamo hanya, kin ga harda tsuminsu na kauye na matan sarakansu aka bani, ai ni tafiya ta yi kyau sai hamdallah kawai, nema kuwa du abinda akace in ba Indi zan bata ne, Allah ya kama mana ya tsareta" Haba ta rike tana kallonta ta ce" To ina rubutun yake?" Hindu ta dubeta tana murmushi ta ce" Haba ke kuwa, a saman jaki fa ana tafe rike nake da galan din ba da igiyarsa ba, yaya zan yi wasa ai fatana na shigo gidan nan, ina shigowa na bata ta shanye tasss, Aunty yaya maganar ruwan zigalan kin saka min a frij din?" Fadime ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina kai ta ce" Na saka, na zuba peak dinma a ciki, sannan na markada maki kankanar itama, kuma na markada cocumbar da peak din, tunda kin riga kin saka kanki a tunanin da bashida wani tsari ai sai ki yi, ni dai ido ne nawa, kuma in sha Allah yau zan mata bayanin nan, tambaye tambayenta sun isheni gaskiya" A firgice Hindu ta mike zaune daga ringesawar da ta yi ta yi wiki wiki da ido ta ce" Yau yau Aunty?" Fadime ta gyada kanta Hindu ta ce" Ama me yasa yau?" FADIME ta dubeta da kyau ta ce" Kamar yaya me yasa yau? A irgenki yau saura kwana nawa igiyar aure ta hau kanta?" HINDU ta sake yin wani iri ta ce" To ama, me zai hanna ki bari in je gida sai ki sanar mata?" Fadime ta girgiza kanta ta ce" kin ga ki daina irin wannan sarewar, kar ki saki ko nuna gazawarki a gabanta walahi, kuma da kike cewa ki je gida ya dawo daga tafiyar ne?" HINDU ta ce " Aunty dan Allah kar ki yi maganar nan yau, walahi rikitamu zaki yi, karma ki mata maganar nan" Fadime ta mike tana tabe baki ta ce" Ai sai ki yi,ke da kin san da mi za'a shiryata ama kike haka? Ya dace tunda wuri ta san abinda ke jiranta ba sai lokaci ya kure mana ba, domin bamu san lokacin da zasu dauketa ba, su kuma kwaliyar kawai zasu koya mata sai mugun nufin" A haka HINDU ta idasa wuni a ranar, sukuku da ita tamkar bata da lakkah, sai idan lokacin cin abincin ya yi ta je ta kai mata madarar da dan abinci kadan sai kuma wani hadin cikin dubunnan hade haden da take bata na gyara, tun daga na sanhi har na gyaran mata, ita babu ruwanta da wani wai ga yadda mijinta yake, wannan su ta shafa, ko wace wace kawai Aban NADIRAH na dawowa shima da Innar birni ta sheda masa a yau fa zata fuslanci NADIRAH da amsar tambayarta domin kwata kwata ta hannata sakat, in me take sai ta tsareta da tambayoyi, tana tambayarta gidan nan fa? Wa ke basu abincin nan? Yaushe zadu tafi? Me yasa ake mata wannan abin? Na menene? Ita bata so dai da sauransu Shima jikinsa sukukun ya yi har yama ya yi sosai aka dawo da ita aka kuma shige da ita aka yi mata wanka da turaren ruwa a cikin ruwan wankan sannan aka bata sutura mai dumama jiki da su safa aka umarceta sakawa bayan an shafa mata mayukan gyaram kafa da su tafin hannu Zaunawa ta yi saman babar kujera a falonsu tana girgiza kai, gajiya na tare da ita tilis ama magariba ta shigo ba danar yin barci yanzu, Innar birni na kusa ba zata bari ba, innarta kuwa tana daki wai nafila zata yi, ko sallar magariba ba'a yi ba a gaba ama innarta ta shige nafila, ko ta mecece? Yannayin zamanta matar nan ta yi tsaye a kanta tana mata fadansa, ta fuskanceta da kyau ta ce" N hannaki zama irin wannan, wannan din ba zamanki bane, ya dace ki ringa zama irin na masu matsayinki, daga yannayin zamanki ne jikinki zai dauki yannayin tafiyarki, kin ga fa kanki, da idannuwanki komai zaki yi da su ne, idn ba ke da makusantanki ba babu wanda zai samu yawan maganarki, ki gyara zamanki ko mu yi gyaran dare yau!" Da sauri NADIRAH dake hararen gefe ta zarro ido ta juyo tana gyara doguwar rigar dake jikinta ta gyara dan kwalinta da kyau sannan ta gyaran zamanta, ba zama irin na kafa daya kan daya ba, no, zama irin na hade kafafuwa wahe daya sannan a basu karfi gefen hagu ko na dama, haka kuma bayanka kan bada yannayin halitarsa da kyau, kuma dukkan wani fasali naka kan fitowa da kyau da irin girman isar da sakon yannayi a irin zaman Ido ta zubawa NADIRAH, har yanzu takan ji a rants yarinyar kamar ba Yar bayi ba, koda yake ko menene ta tabata mai girma le tunkarar rayuwarta Idannuwanta na matukar bata mamaki, kamar ba yar africa ba?, Yannayinta na bata mamaki, mutun ce mai son sakewa, Dan murmushi ta yi a boye, kasa kasa ta ce" Ki dan saki fuskar taki, ki kasance mai aika murmushi koda ranki ya bace ba fushi ba kin ji?" NADIRAH ta gyada kai, tana kallon matar ta juya ta fice cike da takama hakan ya sa ta rakata da harara har kamar idannuwanta zasu fado kasa dan rigima Innar birni ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce" Hararanta kike yi?" A zabure ta juyo tana daidaita yannayinta, kasa kasa ta yadda ita da kanta bata san cewa abinda take gujewa ya fara tasiri a kanta ba ta ce" Aa innar birni, bara na je na yi sallah" Kai Fadime ta gyada a hankali ta ce" Idan kin gama, ki same mu a dakin Abanki" Dan juyowa ta yi, sai kuma ta amsa ta shige nata dakin da har yanzu take mamakinsa, waje aljanar duniya ace nata ne? Birni birni basa jin tsoron Allah sam! _________________________________ Bayan sallar Magariba da isha'i Zaune suke su ukun , kowane ba yalwataciyar fara'a a saman fuskarsa, dama dama Innar Birni tana dan shan shayi ne a kofi irin na bugaje tana dan kallon su a ranta kuwa tana adu'ar Allah ya kawo masu koma menene da sauki Tun kafin ta shigo, samsanyan, rikitacen kanshi ne ya fara shigowa, sai da ta tsaya bayan ta yi salama har
Chapter 26 · 0% Book details