Sashe 50
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rai bace ta ce" Menene haka? Me kike son aikatawa ne?, Ki nutsu walahi kar ki aikata abinda zai zamto maki dana sani ba, domin da wahala hannunki ya kai kasa ban rama wannan ba gaskiya!" Da karfi ta warce hannunta, a harzuke ta ce"Kina nufin ki mareni?, Ki fada da bakinki kina nufin ki mareni? Da kaf danginki sai na karar da su da hannayena walahi!" Abin mamaki, tar ido cikin ido NADIRAH ta ce" Da gawarwaki sun amsa kiran ubangijinsu kennan?, Ina mamakin yadda kika kawo warhaka a gidan nan a zuciyar mutane da yawa, ko dai a kanmu ne bakya iya boye halinki? Karara nake karantarki, sam baki iya takunki ba, ko sunne idannuwansu ya rufe suke ci gaba da maki kallon da suke yi maki? Abinda na sani shine, rashin hakurinki, da zafin zuciyarki zai kai ki ya baro ki!, Na fada maki ba lale bane na ringa zuwa ina fada maki shirina!, Yayama kike so na iya aikata aikin da ake so na yi ba tare da na saba da shi ba? Ke bakya so a zargi uwar gidansa ne? Dan Allah ki saka ido ki sarara min na gabatar da abinda nake son gabatarwa, in da hali in kin san zaki ringa manta cewa tafiyarmu daya in ina aikata wani abin ki daina zuwa inda nake idan muna zaune da su!, Magana ta karshe itace, ki kula da hannunki, in ya sauka a jikina yana iya wanyewa lafiya, ama ba a jikin wannan ba, bana tunanin an yi halitar da zata daketa ina waje na kyale!, Shegema fa ya san iyayensa!" Daga haka ta yarfar da hannun ta nufi ciki rai bace, walahi sai da ta ji kamar zata hankade banzar nan, ita komai na hauka da karambani? Bata yin komai a ilimance? A yadda ta sako burin nan ai sai ta dan ringa nuna tanada kwakwaluwar cin zalin din, gaskiya tama rainawa ASADEEK wayo da wannan matar ta iya rufemasa ido har zuwa yanzu du iliminsa da ganno mai laifinsa? Mtssss! Tana shigewa Hindu ta yi iya yinta dan zaunar da Ummah A nutse ta fuskanceta ta ce" Hajia, ya dace zuwa yanzu mu yi abin fahimta, magana ta fahimta wace zamu fitowa junna a mutun, zan so ki gane, wannan hargagin da rikicin babu inda zai kaimu sai mu falasa kanmu, mu tonawa kanku da kanmu asiri, UMUGHLUK ITIBEL fa ba mahaukaci bane, ba makaho bane, ba kuma yaro karami bane, kuma ke kika raini abinki, kin fimu sannin idan ya fara fuskantar lamari irin na rashin yarda zai iya dora ayar tambaya a kai, yarinyar nan kuwa da kika gani abu daya zuwa biyu zai iya sakata ta tona lo meye kowa ya shiga uku, Hajia ita ba baiwa bace, iyayenta suke bauta, kin ga a dole yannayi na sada kansu a taka su ya sha bamban, sannan tanada ra'ayi nata na kanta, wanda ya saka take iya dubanka tace ba zata yi abu ba, ko bata son abu, to irin wannan abin yanna sakawa a sha wahalar zama da mutun, mutun mai ra'ayin kansa inaga ko a bariki yanada wuyar sha'ani, ba'a juya shi yadda aka ga dama, HAJIA tunda ta yarda aka yi wannan abu da ita inaga mu bata damar da zata aikata aikinta ta hanyar da ta ga zai fi gyarata, ba mu hannata sakat ba ta hanyar saka mata ido a dukkanin motsinta da neman hannata rawar gaban hantsi, ki sani, bata shigo gidan nan dan ta gaje ba ko dan ta kwace maki wajenki, idan kika yi hakuri gyaranku ne ku duka , watau in kika bata dama kika dauke kanki shiga jikinsu ba dan ta lalata mana aiki bane, Hajia na san baki taba ce mana da bakinki kina cikin tsarin gannin an kawar da shi ba, ama mu ba makafi bane, ba kuma mahaukata bane, bokon ce kawai bamu je ba, ama mun rayu da sannin me yake faruwa a tare da mu, ba gardawan yan kauye kara zube muke ba Hajia, haka kuma muna kishin kanmu, wannan gigi naki na daga hannu ki kawo kusa da mu matsala ne baba, idan ya zamto mun fara cin kanmu da kanmu ba zamu ji dadin tafiyar ba, shawarmu kanta na iya zuwa ba daidai ba, kin ga a haka ba dadi ko?" Umma ta ja numfashi, idannuwanta da suka cenza kala da jikinta dake rawa na bacin rai da fargaba ta dubi HINDU ta ce" Ta yaya zan yarda fakat daya cewa ba ni take son zurmawa ba?, Kin ha abinda ta yi kai tsaye, abin mamaki komai bai ce mata ba?, ASADEEK yanada zafi sosai fa, ama take shige masa hanci da dukunkunne?, Ina fata ba kokari take yi idan ta aikata aikin ta sakayani a ciki ba, domin a yau ta saka na yi abinda ban taba yi ba a gabansa, watau hasala da daga murya!" HINDU ta yi boyayen murmushi, a bayane kuwa ta sake kausasa yannayinta ta karra tabatarwa Umma cewa ta fa yi da aniya, in ba haka ba zata iya saka su a halaka baki dayansu! Da wannan ta karra rufe Umma har ta mike ta tafi Bayan ta tafi ta je dakin NADIRAH Saman salaya ta sameta tana jan carbi dan haka ta zauna tana jiranta har ta gama ta shafa fatiha sannan ta mike ta karasa tana shagwabe fuska ta ce" Innata na kwari cikina da yawa, dubi tumbina ya cika makil walahi" Murmushi innarta ta yi tana cewa" To ai na ga kin yi sallah zai ragu, tunda itama motsa jiki ce" Jikin imnarta ta lafe tana sauke ajiyar zuciya Innarta ta dubeta a sanyaye ta ce" Indina, me ya faru yau?" NADIRAH ta dago a hankali ta zuba mata ido, sai kuma ta sakar mata murmushi ta mayar da kanta ta dora a hankali saman cinyarta Muryarta a tausashe ta ce" Abinda na fahimta shine, muguwar yarda, kauna irin ta haihuwa, kusanci mai girma, yarda gaba da baya da ya dauka ya dora mata, bashi da darr ko dari dari a kanta, ransa nan take yake bacewa idan aka tabata, a kanta yana iya yi maka komai, domin yana kiranta da Mamah, mamansa, innata a uwa yake daukanta" HINDU ta lumshe idannuwanta cike da tunani Muryarta a raunane ta ce" In kuwa haka ne, juye mata aniyarta zai zamo aiki mafi wahala a gabanmu" NADIRAH ta ja numfashi itama ta dago ta ce" Innata, jan aiki ne mai wahala, sai dai na fara hango matakin takawa dan karasawa cen, kanwarsa, watau Auta itace matakina, dan kuwa a soyayar tasa da Umma na hangi ta Auta ta maketa, da Auta zan jingina dan ya fara gane yarena, da ita zan jingina dan ya fahimci kumurcin dake tare da shi, domin Innata , Auta da kike ganni, hankalinta rasss, tana dauke da miki ne a tare da ita, da sharin matar cen, ta san yadda ta ci karfinsa har ya yarda cewa kanwarsa mahaukaciya ce, take rayuwa a haka, a zaman da muka yi, na fuskanci shi kadai ke makance da lamarin Umma, domin matarsama bata wani yarda da ita ba, ama kuma bata san girman sharinta ba, a tunaninta kiyaya ce irin ta wasu iyayen mijin, sai dai kashhh, wanda yakeda mahinmancin ne ya yarda da ita, sosai akoy aiki Innata, akoy gagarumin aiki" Ajiyar zuciya Inna ta sauke, a hankali ta ce" in sha Allah, sannu sannu bata hanna zuwa, ita kuma wancen da izinin Allah sai mun kaita kass, sai halinta ya fito karara a gabansa, wanda take dannewa idan tana gabansa na tsayin shekaru, ba an fara yau ba?, Yanzu muka fara!" Da wannan suka yi ta tataunawa da wasu shirye shiryensu hankali kwonce dan su cinma manufarsu! ___________________________________ Dawakai ne kwara biyar, tafka tafka irin ginanun nan masu ji da karfi da isa, sunna tafe sunna sakin huci da abubuwan adon dake jikinsu yana bada sautin cas cas cas Su biyar din dake saman dawakan dukkaninsu manyan mutane ne masu daraja da fada a ji, a cikinsu UMUGHLUK ITIBEL ne a tsakiya, SHEIK a gefensa, sai rikakun yan siyasa, yan kasuwa, sannan jinnin sarautar a gefe da gefe sunna tafe a nutse tafia irin ta ziyara a asibitoci da sanyin safiyar yau, haka kuma sunna tataunawa kan babar Sallar BIANU da bugaje ke yi du shekara shekara SHEIK ya dubi ASADEEK yana murmushi ya ce" ina fata wannan shekarar , iyayen talakawa zasu yi nasu taron da zaman gaisuwa?" Linzamin dokinsa ya rike ya dan ja, hakan ya saka dokin tsayawa, sannan ya juyo barin Sheikh ya dan zuba masa ido Kai ya kada sannan ya kalli gefensa ya ga sauran sunna dan zantawa ne, sannan dogaransu sun barbazu ne sunna tare mutanen dake son yi masu cincirodo Kasa kasa ya ce" Madarata fa , madarar da kake yi min tofi kulun a jiya ban shata ba" Da mamaki Sheikh ya dube shi ya ce" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 3 Da mamaki da kula SHEIK ya ce" Subahanalah, kar dai ka ce min zubewa ta yi?, Ya salam, aya, ka san jiyan nan irin adu'o'in tsarin da muka yi kuwa?, Dan abinda ya dan tunkaro mun nan ko wajen zamanka bi'izinillah daga jiya kulun sai mun masa zama na kansa, dan in mutun ya fi karfinmu bai isa ya ja da ayar Allah ba" Talaicin da ya tuko shi ya saka shi gyada kai ya sake dan taba gefe da gefen cikin Dokinsa, hakan ya saka dokin sake dagawa suka ci gaba da ziyara, ziyara ce ta ba zata, ba a motoci ba, ba sanarwa, sai sun zo kofar wajen a bude masu, a ziyarar su babu inda basa lekawa, a haka suna kara bada talafi sannan sunna gannin sake na wasu likitocin ana rubutawa domin zai yi zama da su ne na musaman Sai da suka gama suka fito dogarai tari guda sunna karra sakin hanyar dan a basu waje su wuce har suka karaso makabarta Sauka suka yi a kafafuwansu suka shige, ADU'A sukaiwa mamata sosai sannan suka ga irin gyare gyare da sharar