Sashe 83
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
diner?" Abincin da bata gama ci ba ta dan dakata, sai ta samu kanta da tauna maganar a ranta, to ama a kan me zata yi missing din wace bata girmamata, ai Auta bata wani dauketa da daraja ba, gayanan ana yi mata kishiya ta je ta dinke da ita wai harda kwana a bangarenta , ita zata nunawa dangi? Ai dadin abin itama ba daga sama akaa cilota ba, tana da nata dangin , babu wanda zai wulakantata saboda haka A bayane kuwa sai ta yi murmushi ta ce" Ni raboka da Auta ai yau kwana uku, tana bangarensu" Dan tsai ya yi, sai kuma ya kawar da maganar daga ransa, domin da farko sai ya ji kamar ba dadi a ransa, Auta ce fa, mai sunnan Maman Aba fa, ko me yasa sam HUZNAH bata damu da kowa nasa ba in ba shi kadai ba, ba ruwanta da kowa nasa sai shi kadai tak, ko mtan Sheik bata zumunci da kowa, ko me yasa? Ita danginta kadai take mu'amala da su, summa basa wani ziyartar junna in ba ta yi dalili ba, ko dan sunna aure da sarakunna ne? To ma shi zumunci ai ba'a ce banda matan manya ko manya ba, du wanda bayaa zumunci ai baima ji dadin rayuwarsa ba sam Yana kai dubansa kan kujerar Nadirah ya samu kansa da sakin murmushi, rabonsa dai da ita tun jiya daa safe, ko a wulge ba'a leko shi ba, da ace wani abinta ya tsumkota, ko yan nemna rigimarta sun tsumkota da yanzu ka ganta ta yiwu zani daban, riga daban ta zo ta gabatar da neman rigimarta ta karra gaba, wai idan zata gaishe da jama'a sai tace sasanunku, uhum bai taba gannin gidan rikici irin yarinyar ba sam, abinda tun randa ta fara ganninsa bata jin tsoronsa bale yanzu da mata suka ga maza? Ai sai dai a kokarta a ji tsoron Allah kar a raina mazan kawai Sun dan jima a falon kasa sannan suka haye sama, A daren ya so fara yi mata sharan shanye, sai dai gaba daya ya ji raunin hakan a zuciyarsa, a dole ya yi shiru da bakinsa ya shiga gabatar da sallah har sai da ya tabatar ta yi barci sannan ya haye sman gadon gefenta ya kwonta yana binta da kallo Kai in kuwa hakane, gaskiya an cuceta, ga dai mace fa, sai dai an shiga tsakani, an hanna mata jun dadi bale shi Dole ya ji tausayin HUZNAH, dole kuma ya taimaketa, dole ya tayata neman hanyar da zata bila *___________* Ranar biyun kwananta Kasancewar yanzu itama takan hantse ne a bangaren mijinta, yauma tana zaune saman kujera mai zaman mutun daya, mai laushi tana binsa da kallo, a lokacin da yake dan kawonsa a cikin dakin barcinsu hannunsa daya a bayansa a jimke, dayan kuwa a mike a kusan kunnensa yana amsa kira, da yannayin da ta fahimci kamar an dan sosa ransa, sai dai a nutse yake bayanin da ta kasa gane wani yare yake yi, domin ba larabci bane, ba kuma turanci bane, ba buzanci bane, ba kuma hausa bane, har ya gamaa ya kashe kiran ya dan jefa wayar saman bed dinsa dake gyare da shinfidar da suka kwana sama wace shine ya jaja da hannunsa ya gyara dan HUZNAH kam bata san wannan yaren ba, sanna ya juyo inda ya saka ta zauna dan zai tatauna da ita A nutse ya janyo kujerar dake gefe ya ajiye face da ita sannan ya hau ya zauna yana mai hade hannayensa ya zubawa fuskarta ido, wace hakan ya sakata sada nata idannuwan dan sun mata kaifi a cikin natan Dan gyara zamansa ya yi yana kallon agogo, a hankali ya ce" HUZNAH, wata tambaya ce da ni kuwa, ban sani ba ko zaki iya tuna a lokacin da kike amarya, me da me ya faru?" Kanta ta dago da alamar tambayar bata gane ba Dan murmushi ya yi ya ce" Oh sorry, ina son sannin a lokacin da aka kawo ki gidan nan, da wa da wa kika mu'amalanta? Wa da ya maki kyauta? Me da me aka baki? Waye mai maki dahuwa?, Wa yake kula da harkar tsaftar bngarenki, komai da komai dai" Da alamu na ta fara damuwa ta ce" SULTAN, wani abu ke faruwa ne?" Gefe ya kalla kadan, sai kuam ya sake dubanta, bai ce mata komai ba yana kallonta, watau dai amsa yake so kawai Zama ta gyara a hankali ta shiga tunani, maganar shekara goma ce fa yake yi mata kai tsayen nan? To ita wasun a lokacin da ko kallonsu bata iya yi dan kunya da bakunta da kuma mutunta su? Abu daya zata iya tunawa tunda aka kawota gidan a matsayin bakuwa A nutse ta fuskance shi ta ce" Aban AUTA, a lokacin da na zo gidan nan bakunta mun zo da jama'ar fada ne, a kala sun min sati biyu har sai da Abah yace ya isa hakanan maza su dawo gida, abinda nake tune da shi dai a lokacin da nake da bakunta komai nawa a wajen UMMA ne, kama daga abincina, suturuna wa'inda aka ringa nuna min kafin a kawo ni bakunta bangarenka, har zuwa shirye shirye irin na amare da ake kara yi a lokacin, wanda a wannan lokacin ban ga an yiwa BAHIJA ba" Idannuwansa yake dan kiftawa bayan ta ajiye maganar A nutse ya sake fuskantarta , da hannunsa na dama yana dan misaltawa ya ce" Ohk, a cikin launikan abincin da ake baki, ko sutura, ba'a baki abinda ya saka kika tsantsamta ba?, Koma menene ba'a baki wani abin da ya saka kika dan yi mamakin abin ba? Ko sutura baki yi anfani da wata wace sam baki yarda da ita ba?" Fuskarta na nuna alamun damuwa ta ce" Allah ya taimakeka, hankalina ya fara tashi da maganar nan, shin akoy wani abin da yake faruwa ne dan Allah?" "Kima tune ko bakya tune da komai?" Ya sake fada kai tsaye yana kallonta Ksa ta sada dubanta, gaba daya kanta ya fara sarawa dan neman abinda ya saka shi yi mata tambaya irin wannan, gaba daya ta nemi amsar da ya dace ta bashi ta rasa tunda ita bata ga dalilin tambayar tasa bamaa kwata kwata A tunaninta bata hango wani abu da aka bata ta ci, ko ta saka a jikinta ba, wanda zai sakata a wani irin yannayi? Ta rasa gane gabanta bale bayanta, gashi sai magana yake bata a dunkule A sanyaye ta dago tana kallon kamilaliyar fuskarsa, ba zata ce tana karantar bacin rai a fuskarsa ba, duda ta yi mamakin yadda sam yau bai tashi da muguwar damuwar ya kasa shigarta ba, hasalima bai gwada shigar tata ba, ita dai ya taimakawa ya rikitata har ta samu nutsuwa, ama shi sai ya yi kwonciyarsa yana rungumeta a jikinsa, ta yi tunanin zasu farka daa ciwonsa ne , sai ta ga ya tashi y shige bayi ya samu sallat asubahi, har gashi da ya shigo sun dora hira Ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye ta ce" Ni dai a tunanina, bana tune da wani abin da aka bani wanda ya sakani a wani yannayi, duda ban fahimci wani irin yannayi kake nufi ba,ama sam ni ban ga wani abin da aka bani wanda ya sakani a shaku ko hali na rashin lafiya" Idannuwansa ya lumshe, a hankali ya kai hannunsa saman llalausan sajensa yana shafawa Kasa kasaa ya ce" thn, kina iya tafiya " *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 6 Kallonsa take yi kamar zata dauke shi da idannuwanta, Jiki babu karfi ta mike tsaye tana gyara alkyabarta, sai kuma ta sake juyowa tana kallonsa fuskarta na raunana A sanyaye ta ce" In tafi?, Shikenan ba zaka sanar min wani irin yannayi kake nufi ba?" Idannuwansa da sam kwanakin nan basa rabo da dan jaja jaja ya sauke a kan fuskarta Mikewa ya yi tsayen shima, hakan ya sa tsayinsa kere nata sosai Yana kallonta ta kasan idannuwansa, muryarsa na fita a azance ya ce" Ban san me zan ce ba HUZNAH, ban san wani irin yannayi zan kirayi abin ba, abinda na sani shine damuwar dake damunmu tsayin shekaru goma a jikinki ne take ba a jikina ba" A rarabe ya ajiye maganar, sannan a lokacin da ya ajiye din kwayar idannuwansa mararsa tsoro sai da suka kauce daga cikin nata dan jin nauyin furucin, hakan ya sakata tsure jayen lebunansa da ido tana son gane me yake nufi bata ko kiftawa A hankali ta ringa jin faduwar gabanta na dan son ta fi karfinta Da sauri ta ture tunanin dake cikin zuciiyarta ta hanyar dan yin dan murmushi tana kallonsa a hankali ta ce" Cutar dake damunmu? Wace cuta ce wannan............................" Sai kuma ta dakatar da furucinta, a hankali ta dago idannuwanta ta saka a cikin nasa domin ya dake juyowa ne yana kallonta Irin kallon da yake yi mata ya sakata saurin bude bakinta dake dan barbarbar yana rawa kamar mazari , sai kuma ta mayar da shi ta damke shi, ama kuma hannayenta ne suka amshi rawa a hankali a hankali har ta dago su tana kallo, Shima hannayen nata yake kallo zuciyarsa na neman babalewa dan bai san ta yaya zai iya dogon magana da ita a haka ba Yanzu fuskarta ba alamun murmushin dazu , ta sake dubansa ido cikin ido , muryarta na crakng ta ce" Husband......., Kan nufin cutar dake damunmu, wace ta hanna mana kasancewa daya, wace muke zaune cikin kunci sanadiyarta......a jikina take? Like a jikina kadai ne kake haduwa da hakan?" Dara daran idannuwansa ya sake saukewa a kanta, tarin rauni da duba irin na nagarta yake yi mata, hakan ya sakata jin zuciyarta ta yi bugawar da tana da hawan jini ta tabata da a yau sai ta tashi da shanyewar barin jiki A hankali ta damki damtsen hannunsa sakamakon tareta da ya yi a lokacin da ta ji kamar za'a makata da kas sanadiyyar Juwa Tun daga kafarsa ta ringa dago dubanta a hankali har ta kawo kan fafadan kirjinsa, zuwa zaratan hannayensa ta sauke a kan