Sashe 17
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
rayuwar gidan nan so take ta dauke dukkan wani abu mai daraja da kike da shi a rayuwa, kama daga fahimta, fara'a, nutsuwarki baki sani ba" "Ikon Allah daga yiwa yarki fada shine za'a dora min wani abin daban?" Fadime ta fada tana zama daf da ita, domin ta ga ta yi kalar serius, ko menene ba da wasa ta zo mata da shi ba Matsowa ta yi ta kama hannunta ta rike tana kallonta , a sanyaye ta ce" kin san na san ba lamarin Indirah bane ya saka ki kuka, shin me yake damunki da kika kasa fadawa Yaya bayan kunnada kyakyawar alaka tsakaninku, bakya boye masa komai?" Ido ta fara zuba mata, kafin ta waiga wajen dakin da NADIRAH take, ta karra tabatarwa ta yi barci, sannan ta sake dubanta A hankali ta sada kanta, sai ga hawaye ya shiga bin gurbin idannuwanta Muryarta na rawa rawa ta ce" Ina tsoron wata rana na gaza kanwata, abubuwan da nake gani nake ji sun fara neman fin karfin kunnuwana da kuma hankalina da tunanina.........., Bayan neman shiga mutuncina da ake yi wanda na jima da fuskantar haka, shi yasa nake sake lulube jikina da tufafi dan na kare mutuncin kaina da na aurena, a yanzu maganar da nake maki abinda kunnayena suka jiyo dangane da UMUGHLUK ITIFAL nake tsoron kasa rikewa!, Shin me y masu da zafi haka?, Me ya kashe masu ne? UMUGHLUK ai uban kowa ne, yanada kannanun shekaru ama kuma ya dauki girman, ni ba zan taba manta shi ba domin shi ya wanke zargin da ake yiwa Ummu kafin ta rasu, a dazu na ji abinda ke neman tarwatsa min tunanina, na san banida wata hanya da zan iya kare shi sai dai Adu'a, ama ina jin tsoron kar karambani ya sakani tarban aradu da kai, bayan na san banida nasara a kokowar....., Hindu ina ji a cen kasan zuciyata wata rana zan iya shiga uku idan na ci gaba da aikin nan" Hankali tashe Hindu ta ce" Aunty dole ne? Ki bar aikin mana, dan Allah ki samawa kanki sauki , innalilahi wa inna ilaihi rajune wa yake son shiga mutuncinki? Me suke so su yiwa UMUGHLUK ITIFAL? Na zata dan uwansu ne?, " Ajiyar zuciya ta sauke mai zafi ta ce" Idan na bar aiki ba zan iya zama a gidan nan ba, kennan na tafi na bar mijina? Sia yaushe zamu ringa gannin junna? Karshen wata ko shekara?, Idan na bar aikin nan aurena na cikin hatsari!, Kuma da kike fadin dan uwansu, ai na rabaki da giyar mulki, du wanda ya kurbeta ba zai taba sakuwa daga maye ba!" Hindu kam ta rasa me kuma ya dace ta ce, gaba daya auntynta ta sakata a hali na tunani da cikin duhu, ta rasa me ya dace ta yi tunani a kai a yanzu A sanyaye ta ce" Ko me suke takama, zakin sarakai ubansu ne!" Itama a sanyaye ta ce" Haka ne, idan yana gannin fada gaba da gaba ba, idan kuwa ta karkashin kasa ake binsa da sharin fa? Sai dai A'lah ya kare shi kamar yadda yake kare shi a kulun!" "Allah ya tsare shi, aunty, wa yake bibiyarki?" Hindu ta fada Gabanta ya sake faduwa, a hankali ta janye hannunta tana mikewa ta ce" Ki tashi mu kwonta kar mu rasa sallar asubahi a kan lokaci" A dole Hindu ta yi hakuri da abubuwan dake zuciyarta ta je itama ta samu waje gefen y'arta ta kwonta barcin Tunda suka rashi sukai sallar asubahi su biyun suka dinke a daki sunna zantawa tsakaninsu, ita kuwa wannan lokacin ta riika ta matsa kusa da pampo ta darji wankin nan gabaa dayansa A lokacin da mahaifiyarta ta fito dan yin wanka ta shirya ta ganta tana shanyar karshe Da mamaki ta bita da kallo, sai kuma ta nufi pampo dan dibar ruwa a bokici Da sauri NADIRAH ta ajiye ta zo ta tararwa mahaifiyarta ruwan ta mika mata bayin sannan ta koma ta ci gaba da wankinta Wata biyayiyar ajiyar zuciya mamanta ta sauke ta karasa ciki ta yi wankan ta fito Tana kimtsawa tana jin muryar Hindu na fadin ta bar sharar nan ta je ta yi wanka bara ita ta karasa sharar, watau dai sunna ja in ja sunna kus kus ga dukkan alamu gardamar kar ta ji ake yi Murmushi ta yi ta kintsa da kyau sannan ta dauki lafcecen hijabinta ta fito ta ajiye kujerar tayani tsegumi ta zauna tanaa fadin" Kin ga je ki yi wankan ki zo ki je ki amso abin karinmu yi maza".. Murmushi ta yi ta nufi bayin, domin ta mika ruwan tuni , ita kuma HINDU ta gama kamaala sharar ta kwashe taba murmushi ta kalli abin shanyar ta ce" Ka ga yar arziki irin albarka, yarinya mai albarka gaba da baya, ina fata a sallarku ta yauma kin mata Adu'a mai kyau Aunty?" Murmushi Fadime ta yi, kasa kasa sosai ta ce" A kullun inai maku Adu'a ku dukanku, ina fata Allah ya sshiryar min ku, gashi kuwa ashe dai da dan sauki a halayar naku" Murmushi kawai hindu ta yi ta zuba ruwa a roba mai dumi ta zauna ta saka kafarta ta shiga darza, wanda Hakan ya saka Innar birni zuba mata ido tana kallonta da tunanin ita rabonta da ta darji kafarta ba har ta manta ba? Sai dai ta darji ta wasu, watau ta gimbiya ko ta bahija Da dan sauri ta dauki lafayarta mai ruwan dalbejiya ta nada a saman yar doguwar rigarta sannan ta suri kwanon da innar birni ta nuna mata ta nufi fita a ranta tana ayanna' Ban san yaya aka yi hankalinsu ke kwonce a cikin gidan sarauta ba, rayuwa irin ta prison ? Baka isa ka yi kwakwaran motsi idan wani dan Adam din na kusa?, Ai wannan din sam ba rayuwa bace, ukuba ce walahi!, Ina dalili rayuwa ba yanci ba sauki ko kadan?, Ba zan taba irin rayuwar nan ba, ya zamto abinci sai ka zo baban dakin madafa ka amso naku ka juya? Iyayen gidan gidan na hangenku sunna maka maku harara tamkar dabobin da suka siya a kan dole?, Shi yasa ta fi ganewa rayuwar kauye, ta fita ta sakata ta bararake ta wala da ranta ta saki karinta ta hau sama ta fado hankali kwonce, idan ta yi ra'ayi ta yi wanka a teku, ko ta je rafi ta yi, kauyen da ake sako budurwa a gaba dan bata yi aure da wuri ba, kauyen yanzu da sauki, bale Innarta a gefe?ai sai dai ku kashe junna kai da ita!, A hankali ta kai dubanta wajen baban falo, watau falon uwar gidan Sarki Kai ta cire ta karasa tana gaishe da masu kula da madafar sannan ta musamman ka nasu kwanon Mai zubawar ta kama haba tana fadin" Iyeah, wannan dai kamar Nadirar sarkin dogarai?" Nadirah ta yi murmushi tana dan kawar da kanta tuni ta shiga jan wala haula, domin ya zame mata jiki ko dan azalzalar da innarta ke mata a kan haka cewa ko ido hudu suka yi da mutun ta ja masa wala haula dan ba'a san irin mutun ba sam Amsa ta yi tana ji sunna ta maganarta harda mai tambayarta kuma an saka ranar aurenta ko kuwa? Ita fai murmushin dai ta karra basu sannan ta wuce abinta cikin takunta a hankali tana kuma sake kallon bayin dake ta kai kawo ta tabe baki a ranta tana ayana' ku kunna aiki, su kuwa sunna sama?' "Wacece wannan?" Gimbiya ta tambaya daga tsayen da take a jikin babar tagar dakinta tana dan shan Lipton mai dumi dan tuni ta shirya fitowar mijinta wanda baki suka dakatar kawai take jira domin har alkyabarta ta rufa Da sauri wace ke kula da ita da sasafe kafin Innar birni ta karaso ta duba wace ake tambaya Da dan murmushi tana sada kai ta fadi ko wacece, domin a jiya ai sun jima sunna hirar yarinyar, dan kuwa du ta leleka su, yarinya mai dadin hali da kyau kamar ba yar bafade ba Kara zuba mata ido Gimbiya ta yi har ta bacewa ganninta A hankali ta koma cikin dakinta ta zauna saman kujera ta dora kafa daya a kan daya tana kallon waje daya Wani irin murmushi ne ya kubuce mata ta kai dubanta wajen wayarta dake haskawa alamar kira na shigowa Dagawa ta yi ta amsa , sai kuma ta mike da sauri ta idasa hada abubuwan da ya dace ta zuba a jakarta sannan ta ba baiwar nan dama ta dauko suka fito NADIRAH na komawa ta tarar da mahaifanta sunna ta kimtsawa, watau shiri na fita Da mamaki take kallonsu ta ce " Innar birni ga abin karrin fa? Aban birni ina kwana?" Hannunta abanta ya kamo yana murmushi ya ce" Lafia kalau indin innarta, kin ga zamu je Agadaz ni da mamanki, in sha Allah da yama zamu dawo, ki zauna dam kin ji ko? Banda tabin magana" Da dan sauri ta daga kafa tana binsu ta ce" Ama ai baku karya ba fa?" Mahaifiyarta ta dakata daga tafiyar da ta fara domin sun yi bankwana da kanwarta tuni ta juyo ta kamo hannun Nadirah, Gefen fuskarta ta shafa a hankali, ta sakar mata murmushi kadan a sanyaye ta ce" Ai zamu karya, abanki ba zai barni da yinwa ba tunda tare muke, ki kula kin ji yar albarka?" Murmushi ta yi tana gyada kanta tana hangensu har suka fice kwata kwata a balbalin Kwanon abincin ta kalla innarta ta zuba mata Zama ta yi ta turo baki ta ce" Innata, ni bana son cik abincin nan nasu, wainar fulawa nake so da yaji mai dadi, sai kuma , yauwa sai kuma in hau doki" Ido innarta ta zarro tana kallonta ta ce" zo nan yar albarkana mu ci mu gama, sai mu ga yaya za'ayi da maganar dokin, ama wainar fulawa ina muka ganta mu a nan? Bari da rana zan fita na damo maki nono da kaina , na tabata rigimar ba ta wainar fulawa bace ta nono ce" Ai kam, innarta ta gama sanninta ciki da bai, ta saba idan ba karyawa ta yi da sabuwar tatsa ba har wata kasala ke lulubeta, da murmushinta