Sashe 33
Zakin Sarakai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zuciyarka za'a fito da ita yanzu in sha Allah" Kai ya karra cirawa ya ce" Ta isa ta kiya, kuma ina mai tabbatar maki babu abinfa za'a yi, yarki ce fa Fadimata, yanzu sanar min, shin ta san abinda zata je yi kuwa? Kuma tabbatar min ta yarda da hakan kuwa? Jaddada min ai ba zata kiya ba ko?" Karra sada kanta ta yi gabanta na karra faduwa da irin girman zaluncin mutanen A sanyaye ta ce"Ba zata kiya ba, in sha Allah zata gabatar da komai bisa tsari" Murmushi ya yi yana gyada kansa ya sake duban hanyat, sannan ya karra kallonta ya ce" kin sani, abu ne da zai zamto farin ciki ma kowa, ciki harda ke da ita, domin yana kasancewa nine zan zamto mau mulkar AGADAZ, Fadimata hakan na nufin kema kin zama gimbiyar Agadaz, kuma ba zan taba bari wani abu ya sameta ba ai kin fahimta ko?, Ci gaban kowa ne da izinin Allah" Fadime ta lumshe idannuwanta, tana mayar da hawayen da ya taru a gurbinsu, bata ce komai ba, hakan ya daga hankalinsa, harma ya dan fitar da kafarsa ya ce" Ko akoy wata damuwa ne?" A hankali ta girgiza kanta ta ce" Dama, akoy kanwata, wace ta raini NADIRAr, Ita NADIRAH din ce ke kukan zata je da ita, ba cen bavan garin ba, iya Fada Allah ya taimakeka, da zarar an daura an tafi da ita, ita kuma sai ta dawo, shine tsaikon da aka samu, ama zasu fito yanzu in sha Allah " "Ita kanwar taki, bata da magana? Kuma ta san me ake nufi da maganar?" Ya fada yana sake kallon Innar birni Fadime ta gyada kanta ta ce" Ta san komai, sannan ta iya bakinta, hasalima tana tare da komai" Lebensa ya cije yana tuna irin rikicin da ya barro Umma tana ta masifar sun cika sake da abu da suka bari wasu suka san maganar bayan su biyu kadai, to idan ta ji ga wata ta karru yaya kennan? Baki ya tabe yana dage kafadu, domin a sanninsa shi ba sa'an yinta bane, sai dai ta nemi wasu daban Dan murmushi ya yi ya ce" To ai da kin fadi tun dazu da an jima da yi Fadimata, su zo mu je, kin ga dare na karra yi ,karfe tara za'a daura auren bana so hanya ta san da wucewarmu" Wata ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi sannan ta mike ta juya da sauri, shi kuma har leke yake yi yana binta da kallo, sannan ya koma ya sake zaunawa a ransa yana ayana' To ko ke kika ce zaki je ai babu ubanda zai hanna Fadimata, ke dai rai da lafiya Gimbiyar Agadaz" Bata jima da shiga ba sai gasu sun fito A hankali ta tsaya daga dokin kofa tana hangensu har mahaifin NADIRAH ya gyara mata alkyabarta bayan ya sakata a motar, sannan Hindu ta shige gaba ta hakimce tana sake raya abinda ta yi niya, ai bataga ubanda zai hanna ba Walahi!, Fadime na tsaye har motar ta bacewa ganninta, a hankali ta dago idannuwanta ta sauke a fuskar mijinta, a hankali ta dora kanta a saman kirjinsa tana jan numfashi a hankali ta ce" Na hakura Abanta, Allah ya bata nasara" Kai ya gyada a hankali yana shafa bayanta shima a sanyaye ya ce" Allah zai rakata a dukkan motsinta, in sha Allah ba zasu sakata a uku ba" Da wannan suka shige ciki, a daren nan ma banda niyar kai goshinsu kasa babu abinda suka yi, haka kuma Fadima tana cike da zulumin lamarin Hindu, ita dai bata so ta aikata wani abin ________ ___________________________ Shigowarsu, bai saka daya daga cikin Umma ko Gimbiya motsawa ba, hasalima HINDU dake rike da ita suka fi tsarewa da ido su dukansu biyun Da waya a kunnensa ya shigo yana amsawa ya dube su da hannunsa ya masu alamun gatanan fa Gimbiya ta cire kanta gefe, Umma kuwa ta ciciba ta mike ta nufi inda suke tsaye sai yatsina take yi irin na raina bayin nan Tana zuwa HINDU ta koma gefe kanta a kasa, ita kuwa ta saka hannayenta cikin isa ta dauke Alkyabar da aka luluba a saman kan NADIRAH A hankali NADIRAH ta dago lumsasun kwartayen idannuwanta masu katon karfi a kan mai kallonsu sannan sun dauki kwali ga santsi da fuskarta ke nunawa koda babu maganar hoda ko makamanciyarta, lebenta kuwa banda walwal babu abinda yake yi na abin gyaran lebe da ake dan shafa mata,tamkar leben jarirai Gaban Umma sai da ya kwonci kwonci ya fadi, lokaci daya zuciyarta ta wani irin mahaukacin bugawa sannan ta saki alkyabar da sauri tana ja baya Jikinta har rawa rawa yake yi, da sauri ta juya ta damki hannun Sarki a gaban matarsa da kuma Hindu da ta zarro ido ta bisu da kallo ta ja shi cen ciki ta rufo kofa Hindu ta hadiye yawu a ranta ta ayana' Toh fa' Sunna shiga Umma ta dube shi kamar yadda yake kallonta ta ce" Cenza wace kuka ce zaku hada kuka yi? Wannan din wacece?" Murmushi ya yi ya kai zaune yana kallonta da kashe ido ya ce" Ke fa mayar mata ce,wannan dai ai kin san kamar guba take a wajenki ko?, Koda yake............lamarinki sai ke, ita dai ce yar bayin, yar Fadimata" Zaunawar ta yi itama tana mayar da numfashi ta ce " Lalle mace ce ita!, Ama ina fata ta yarda?" Kai ya gyada yana sake lumewarsa dan barcima zai wuce shi daga nan , dan da wuri zai farka saboda nadi da hawan da za'a yi kafin su wuce da amaryr Mikewa Umma ta yi tana sake daidaita numfashinta ta ce" bara na je na sauke su, ba za'a barta ta kwana a kasa ba, zata hau saman bed din ne" Kafadunsa ya dage, ita kuma ta fice Irin yadda ta ringa haba haba da su sai da abin ya basu mamaki gaba dayansu Shinfida mai kyau harda abinci mai kyau, sannan ta ringa jadadawa NADIRAH ta saki jikinta ita din ummansu ce, ita dai HINDU kiri kiri tana zaune dar tan kallonta , har sai da ta tsargu ta fice dan jin wacece wadda suke tare wai?, Tana fita Hindu ta zauna tana sake bin dakin da kallo NADIRAH ta kalleta ta ce"Innata matar nan warin munafukai take yi" Da sauri HINDU ta rufemata baku tana mata alamun ta yi shiru a kusa da su suke sannan ta sakar mata murmushi ta mata alamun ta zurra ido ________________________________ *Ranar dorawa budurwa daraja* Karfe tara aka yi za'a daura aure, sai dai abin bai kasantu ba sai kusan karfe goma na safe, a cikin masalacin da aka yiwa Sheik iso cewar a ciki za'a daira, bayan ga dumbin mutanne a waje da suka zo dan a daura da su Dayan abin da ya dan bashi mamaki gannin an ware mutanen da zasu kasance sheda basu fi a irga ba an ce sauran su zauna a waje dan AC baya yi, idan waje ya cinkushe hakan zai zamto takura ga mai martaba Shi dai ya gabatar da sadakinsu, sadaki mai daraja, sannan ya amshi auren da aka basu Sun daura aure cikin daraja da mutunci,sannan Sheik ya ja Adu'ar da har sai da Mai martaba ya fara tsitsine masa a ransa, gani yake wannan din ai iskanci ne, ina dalili wannan uban shishigi da janyi ayoyi haka? Daga nan SHEIK ya bude Alku'ani ya nemi da mutanen da suka zo tare su shigo, suka shiga gabatar da saukar alku'ani mai girma wanda hakan ya dake kular da sarki ya koma gefe yana sauraro ama hankalinsa ba a wajen ba, ya fi daukar hakan da wata fuska daban, su kuwa cikin nutsuwa suka yi, kuma kasancewar sunnada yawa nan da nan suka gama aka sake yin watga fatihar sannan aka shiga bayar da sadaka wa mabukata, wace wannanma kokarin Sheik din ne Bayan abubuwa sun lafa SHEIK na murmushi ya dake mikawa Mai martaba hannu a tausashe ya ce" Ashe sunnanta ba bahija bane?, Domin sai na ji kamar UMUGHLUK ITIFAL ya furta cewa sunnan yarinyar BAHIJA?" Wani irin murdawa da cikin Sarki ya yi sai da ya dan karkace zama,haka kuma idannuwansa sai da suka zarro lokaci daya ya shiga tunanin a ina UMUGHLUK ya san sunnan y'arsa? Lokaci daya kwakwaluwarsa ta tuno masa ai maganar ta farko su da kansu suka fada masa yarsu BAHIJA Wata boyayiyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Ai Bahijar kiranye ne, asalin sunnan NADIRAH ne, Bahijar mahaifiyar ke so sai ta saka mata har kowa ke kiranta da hakan" Murmushi Sheikh ya yi yana daj sake kallon abin zufar da yake kokarin jike turkudin Sarki, sai kuma Sarkin ya mike yana fadin" Bara na je da kaina na ga shirin fitowarsu, sai na fito SHEIK" Fatan fitowa lafiya ya yi masa, sannan ya shiga buga numbar ASADEEK yana ayyana ' bawan Allah ko ka kira ka ji an daura lafiya? Gashi har karfe daya zata yi' A birkice ya shige bangarensa yana sake buga numbar UMMA, domin kwata kwata hankalinsa ya kasa kwonciya, so yake yi ya sake jin gaskiyar lamari cewa ASADEEK bai san y'arsa ba! Tana baza kanshi da sabuwar suturar da ta saka dan ta yagawa matan da suke takamar sunne darauta ta karaso ta rufe kofar tana sakin murmushin gannin ai kamar har hakarsu ta cinma ruwa tana fadin" *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, al alaminmu ancinmu.``` *https://www.facebook.com/106494781436168/* *OUMOUGHLOUK ITIBEL* _(ZAKIN SARAKAI)_ _FREE BOOK_ *Na* *SAJIDA NIGER* 2 Ba editing Tana murmushi ta ce" Barka da idasa aiki mafi hatsari Sarki, burinmu, farin cikinmu ya kusa tabata, baka ji yadda raina yake fari ba idan na tuna mun fara kaskantar da darajarsa kennan, duda mun dauko yarinya mai kyau zamu bashi, ama sai dai ya kalleta, domin na tashi daga shawarar cewa ba za'a bata abinda aka ba matarsa ta farko ba, dan kar aje ya yi ido hudu da ita ya nemi shafarta har ya kwatanta shigarta abu ya tabata mu bani!" "Asadeek ya san BAHIJA. Waje ne?" Ya fada yana tare numfashinta Ido ta zuba masa kafin ta ce" Wani abu aka yi ne?" A